Venezuela ta rantsar sabbin sojoji 5,600 yayin da rikici tsakaninta da Amurka ke ƙara tsami
Gwamnatin Venezuela ta bayyana ‘‘barazanar mulkin mallaka’’ da kuma ayyukan sojojin Amurka na baya-bayan nan a yankin Caribbean a matsayin dalilanta na fadada rundunonin sojin ƙasar.
Hukumomi a Venezuela sun sanar a ranar Lahadi cewa, an rantsar da sabbin sojoji har 5,600 a cikin rundunar sojin ƙasa ta Bolivarian a daidai lokacin da rikici tsakanin gwamnatin ƙasar da Amurka ke ƙara tsami.
An ɗauki sabbin sojojin aiki ne saboda “barazanar mulkin mallaka,” a cewar kafofin watsa labarai na cikin gida, suna masu nuni kan wata sanarwa ta gwamnatin ƙasar, wadda ta yi nuni kan barazanar Amurka da kuma tura jiragen sojin ruwanta zuwa yankin Caribbean.
Amurka ta fadada ayyukan sojinta a faɗin yankin Latin Amurka kwanan nan, inda ta tura jiragen sojin ruwa da jiragen yaki da na bama-bamai da kuma jiragen sama masu saukar ungulu da jirage marasa matuka.
Sanarwar ta jaddada cewa sabbin sojojin sun yi rantsuwar biyayya ga Shugaba Nicolas Maduro kana ta bayyana sojojin a matsayin ƙashin bayan “kwanciyar hankali da zaman lafiya da tsaro da kuma makomar Venezuela.”
Manjo Janar Javier Jose Marcano Tabata ya shaida wa gidan talabijin na VTV cewa aikace-aikacen soji sun karu sosai.
“A halin da ake ciki, yayin da sojojin mulkin mallaka ke kai hari ƙasar ba bisa ƙa’ida ba, da ƙarfi tsiya da kuma yaudara da ƙarya a fili, dubban ‘yan ƙasa musamman matasa suna shiga rundunonin sojojin ƙasa ta Bolivarian,” a cewar Marcano.
Bayanai daga hukumar ƙasar suna bayyana cewa Venezuela tana da sojoji kusan 200,000, da jami'an 'yan sanda 200,000 da miliyoyin ‘yansa’kai.
Amurka ta kai hare-hare akalla sau 22 a yankin tun daga watan Satumba kan jiragen ruwa da ake zargin suna safarar miyagun ƙwayoyi, inda ta kashe aƙalla mutane 87.
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi gargaɗin cewa nan ba da jimawa ba ƙasarsa za ta soma kai hari kan hanyoyin kasa da ake bi wajen safarar miyagun ƙwayoyi a Venezuela.