| Hausa
DUNIYA
4 minti karatu
Trump ya yi wa Iran barazana, ya kira ICC ‘marar gaskiya‘, ya sauya sunan AI zuwa ‘SI’
Shugaban Kasar Amurka Trump ya ce a nan kusa za a iya cim ma yarjejeniyar kawo karshen yaki tsakanin Rasha da Ukraine.
Trump ya yi wa Iran barazana, ya kira ICC ‘marar gaskiya‘, ya sauya sunan AI zuwa ‘SI’
Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya yi jawabi ga Babban taron MDD a birnin New York /Photo: Reuters

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya yi imani za a cim ma yarjejeniya da Iran jim kadan bayan zaben da ke tafe a Amurka, yayin da ya yi gargadin cewa zai jefa Tehran "cikin babban bala’i" idan ba a cim ma yarjejeniya ba.

Ya bayyana hakan ne a yayin Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 81 a birnin New York na Amurka.

"Shin zan tura su cikin babban bala’i ne inda babu damar tsira ko fatan samun daukaka ko ci gaban al'umma a nan gaba?" in ji Trump a ranar Talata.

"Na yi imani za mu cim ma yarjejeniya nan take bayan zaben, domin babu ma'ana su ƙi amincewa. Suna jiran su ga yadda zan yi a zaben tsakiyar wa'adi," in ji Trump, inda ya kara da cewa shi ba dan takara ba ne kuma ba zai bari zaben ya shafi manufofinsa game da kasar Iran ba.

Trump ya ce ya fara tattaunawa da Iran tun lokacin da ya hau karagar mulki, inda ya ba da shawarar "hadin gwiwar tattalin arziki" domin musayar dakatar da shirin nukiliya na Tehran, amma Iran ta "ki amincewa kwata-kwata" da tayin a wancan lokacin.

Ya sake nanata cewa ba za a taba barin Iran ta mallaki makamin nukiliya ba, tare da yin kira ga dukkan kasashe da su nisanci Iran ta fuskar tattalin arziki.

Trump ya kwatanta gwamnatin Iran a matsayin mai "rauni da kuma da ke cikin mawuyacin hali."

Yakin Rasha da Ukraine

Trump ya bayyana cewa ana iya cim ma yarjejeniya tsakanin Rasha da Ukraine domin kawo karshen yakin nan ba da jimawa ba.

"Muna aiki kafada-da-kafada da shugabannin Rasha da Ukraine, kuma za mu cim ma hakan. Ina ganin matakin zai faru ne cikin sauri fiye da yadda mutane ke zato. Sun gaji da halin da ake ciki," in ji Trump.

A baya, ya shaida wa manema labarai a yayin babban taron Majalisar Dinkin Duniya cewa sakonsa ga Shugaban Rasha Vladimir Putin shi ne ya "kawo karshen yakin".

Ana sa ran daga bisani Trump zai gana da Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy, sannan zai halarci bikin sanya hannu na bangarori uku domin tabbatar da sabuwar yarjejeniyar tsaro ta Greenland, kamar yadda Fadar White House ta bayyana.

Latin Amurka

Shugaban Amurka ya bayyana cewa wata yarjejeniya game da man fetur din Venezuela "ta fara samun ci gaba a yanzu haka," inda ya kara da cewa wasu daga cikin manyan kamfanonin mai na duniya na shiga kasar.

Trump ya kuma bayyana cewa Mexico ce cibiyar tashe-tashen hankula da kungiyoyin masu safarar miyagun kwayoyi ke haifarwa, yana mai cewa dole ne kasar ta sake kwato iko kan yankunanta.

Da ya juya ga batun Cuba, Trump ya shaida wa Majalisar Dinkin Duniya cewa kasar "za ta ruguje."

"Gwamnatina na kuma neman a samu gagarumin sauyi a halin da ake ciki a Cuba, inda gwamnatin gurguzu ke fuskantar matsin lamba mai tsanani—wato matsin lamba mafi girma da ta taba fuskanta. Kasa ce da ta gaza gaba daya; tana kara rushewa fiye da kowane lokaci a baya, kuma za ta ruguje," in ji Trump.

Greenland

Ya ce Amurka za ta kafa "babbar rundunar soji" a Greenland, wadda ta hada da manyan sansanonin soji guda biyu, kuma za a rattaba hannu kan yarjejeniya a ranar Talata.

Kotun ICC

Trump ya yi kira ga dukkan kasashen da ke cikin Kotun Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) da su fice daga kotun, yana mai cewa ta fita daga ikon sarrafuwa.

"Amurka ma tana adawa da wannan kotu da ta fita daga ikon sarrafuwa, wato Kotun Manyan Laifuka ta Duniya," in ji shi a zauren Majalisar Dinkin Duniya.

"Ina kira ga dukkan kasashen da ke mambobi a ICC da su janye daga wannan kotu mai daukar matakan da ba su dace ba nan take," in ji shi.

AI ko SI

Trump ya ce takardun gwamnatin Amurka za su yi amfani da "super intelligence (SI)" a nan gaba maimakon fasahar wucin gadi kuma ya maimaita kiran da ya yi a baya game da gargadin Kirkirarriyar Basira (AI) a matsayin ƙarya.

"Daga wannan lokacin zuwa gaba, za a sauya duk takardun Amurka, da kuma ma na duniya, don amfani da kalmar "super" mafi daidaito……" in ji Trump.

"Ba zan hana ci gaban wani abu da zai fi juyin juya halin masana'antu girma ba," in ji shi.