| Hausa
AFIRKA
3 minti karatu
Afirka ta Kudu ta buƙaci ƙasashen Afirka da ta mayar da jama'arsu gida su biya ta ladan jigila
Afirka ta Kudu na buƙatar gwamnatocin sauran ƙasashen Afirka da dama su biya ta kuɗaɗen da ta kashe wajen jigilar dubban 'yan ƙasashensu zuwa gida.
Afirka ta Kudu ta buƙaci ƙasashen Afirka da ta mayar da jama'arsu gida su biya ta ladan jigila
Dubunnan 'yan ci rani mafi yawa daga kasashen Afirka sun bar Afirka ta kudu a kwanan nan saboda znaga-zangar kyamar baki.

Afirka ta Kudu na neman wasu gwamnatocin Afirka da dama su mayar mata da kuɗin da ta kashe wajen mayar da dubban 'yan ƙasashensu gida.

Buƙatar ta zo ne bayan da Afirka ta Kudu ta kori ko ta taimaka wajen mayar da baƙin haure sama da 80,000 gida, bayan zanga-zangar adawa da shige da fice ba bisa ka'ida ba.

A cewar ma'aikatar harkokin cikin gida ta ƙasar, wacce ta yi wa 'yan majalisar dokoki bayani a ranar Talata, ƙasar ta kashe kusan dala miliyan 18 wajen ɗaukar nauyin baƙin da suka nemi komawa ƙasashensu.

Ma'aikatar Harkokin Wajen ƙasar ta aika da buƙatar neman biyanta kuɗi ga Malawi, Habasha da Najeriya a rubuce, in ji jami'an.

Kuɗaɗen sun haɗa da na hawa motocin bas da wuraren kwana

Kuɗin ya ƙunshi na motocin bas don jigilar baƙi, da cibiyoyin mayar da su na wucin-gadi da biyan ma'aikata saboda wuce lokutan aiki, da sauran kuɗaɗen da aka kashe.

Tommy Makhode, Babban Darakta na sashen Harkokin Cikin Gida, ya bayyana kuɗaɗen a matsayin "na ba-za-ta kuma ba makawa sai an kashe su."

Wasu ƙananan hukumomi da ma'aikatun gwamnati da ke da hannu a dawo da su suna neman diyya daga ma'aikatar Harkokin Cikin Gida, tunda ba a tsara kasafin kuɗin aikin ba.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Leon Schreiber, ya bayyana yawan komawar mutane gida da korar da aka yi a wajen gida daidai da wani abu da ba a taɓa ganin irin ta ba.

Ruruwar rikici

Barin kasar ya faru ne a lokacin da ake ta samun tashin hankali kan shige da fice a Afirka ta Kudu. Kungiyoyin hana kwararar baƙin haure sun gudanar da zanga-zanga, kuma wasu hare-haren da ake kai wa 'yan kasashen waje sun kawo cikas ga dangantaka da sauran gwamnatocin Afirka.

Kungiyoyin sun zargi baƙin haure da janyo rashin aikin yi, da aikata laifuka da kuma matsin lamba kan ayyukan gwamnati.

Kwanan nan, Ghana ta yi kira da a saka halin da ake ciki a Afirka ta Kudu a cikin ajandar taron Tarayyar Afirka da za a yi nan gaba, shawarar da hukumar nahiyar ta yi watsi da ita.

A cewar sabbin alkaluman gwamnati, mutane 82,875 ko dai an mayar da su gida da son rai ko kuma an kora su tun lokacin da rikicin ya fara. Duk da haka, alƙaluman da gwamnatocin ƙasashen da bakin haure suka fito sun nuna cewa jimillarsu ya kai kimanin 178,000.

An mayar da dubbai zuwa ƙasashe na kusa

Ficewar 'yan gudun hijirar daga Afirka ta Kudu wani ɓangare ne na wani gagarumin matakin da gwamnati ke ɗauka. Tsakanin watan Afrilu da Yuli, an kori mutane 16,078 waɗanda galibinsu suka fito daga ƙasashen Lesotho, Malawi, Tanzania, Zimbabwe da Mozambique ta hanyar Cibiyar Korar 'yan gudun hijira ta Lindela da ke ƙasar.

Jami'an tsaro na Afirka ta Kudu sun faɗa a makon da ya gabata cewa za su ƙara kaimi wajen kai samame kan baƙin haure da ke zaune ba bisa ka'ida ba, da kuma masu aikata laifuka masu alaka da hakan.

Sun ce sun kama kusan mutum 60,000 da ke zaune a ƙasar ba bisa ƙa'ida ba, ciki har da mutane 16,208 da aka kama a watan Yuli kaɗai.