MDD ta yi gargadi kan yunwa a yankin Kordofan na Sudan a yayin da fararen-hula ke ƙara shiga matsi

Ƙungiyoyin bayar da agaji sun yi gargaɗi dangane da yadda yunwa ke ƙara ƙaruwa a Sudan da kuma matsalolin da suka shafi taƙaita zirga-zirga da kuma ƙaruwar rikice-rikice.

By
Ƙungiyoyin jinƙai sun bayyana damuwarsu kan ci gaba da kai hare-hare kan fararen-hula da kuma ababen more rayuwa na fararen-hula. / Reuters

Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta yi gargadin cewa fararen-hula a fadin yankin Kordofan na Sudan suna fuskantar mawuyacin hali da ke ƙara taɓaɓarewa yayin da hare-hare ke ƙaruwa inda ƙungiyoyin ba da agaji suka ba da rahoton yanayi na tamowa da ƙawanyan da ake yi da kuma ƙarin hare-hare kan fararen-hula da ma’aikatar agaji

"Abokan aikinmu na agaji suna gargaɗi har ila yau cewa fararen-hula a faɗin yankin Kordofan suna fuskantar ƙarin hatsari yayin da hare-hare ke ƙaruwa," kamar yadda mai magana da yawun MDD Stephane Dujarric ya shaida wa manema labarai a New York.

Ya ce majalisar ma’aikatan ƙungiyoyin agaji a ƙasar Sudan sun fitar da wata sanarwa "inda suke Allah-wadai da hare-haren da ke tsananta a fadin Kordofan da kuma ƙawanyar da ake ci gaba yi, lamarin da ya yi sanadin killace birane ."

Mutane sun maƙale a Dilling da Kadugli, inda suke fuskantar "matsi mai tsanani da taƙaita tafiya mai yawa da kuma samun muhimman ayyuka da kariya," in ji shi .

Dujarric ya tabbatar da "yanayi na tamowa da aka gano a Kadugli,"yana mai ƙarawa da cewa an ba da rahoton hare-hare babu ƙaƙƙautawa a Babanusa da ke Kordofan ta Yamma a cikin ‘yan kwanakin nan.

Ƙungiyoyin jinƙai sun bayyana damuwarsu kan ci gaba da kai hare-hare kan fararen-hula da kuma ababen more rayuwa na fararen-hula.

Durƙushewar agaji na tafe

Dujarric ya yi gargaɗin cewa tashin hankali na taƙita damar samun abinci da magani da muhimman ababen amfani tare da hana manoma zuwa gonakinsu da kasuwanni, lamarin da ke ƙara "barazanar yaɗuwar tamowa a faɗin jihar Kordofan ."

Ya yi kira ga dukkan ɓangarorin su kare fararen-hula , "ciki har da ma’aikatan jinya da na agaji , musamman waɗanda ke tserewa daga wuraren da aka yi wa ƙwanya da kuma masu aikin taimakon rayuka a fagen daga."

Ma’aikatan jinya na "fusktantar gagarumin hatsari" yayin da suke ƙoƙarin gabatar da muhimman kayayyakin agaji ga mutum miliyan 1.1 a fadin Kordofan, in ji shi, yana mai jaddada cewa suna buƙatar "damar mai amincewa" domin kaiwa ga wadanda ke buƙata .

Sai dai kuma, a Darfur ta Arewa, ƙungiyar ba da agaji ta Save the Children ta ce fiye da mutum 43,000 da aka raba da gidajensu a Al Fasher tun watan Oktoba sun isa garin Korma da sansanin Silk , inda suka "ƙara matsi mai yawa" kan al’ummar da ke karɓar baƙunci da kuma ke da rauni.

Rikici tsakanin sojin Sudan da rundunar RSF, wanda aka fara a watan Afrilun shekarar 2023, ya kashe dubban mutane da kuma raba miliyoyin mutane da gidajensu, inda hukumomin bayar da agaji ke gargaɗin cewa tamowa da hare-hare na yaɗuwa a yakuna da yawa.