Kakakin Majalisar Jihar Ribas da wasu ‘yan majalisa 16 sun sauya sheƙa daga PDP zuwa APC

Majalisar ta gudanar da zamanta a yau, inda waɗanda suka sauya sheƙar suke cewa sun bar jam’iyyar ta PDP ne saboda rikicin cikin gida da ya addabi jam’iyyar.

By
Da wannan sauya sheƙar, Jam’iyyar APC tana da mambobi 17. / Others

Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Rivers, Martin Amaewhule, ya fice daga Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya koma Jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Amaewhule ya sauya sheƙar ne tare da wasu mambobi 16 na Majalisar a ranar Juma’a.

Majalisar ta gudanar da zaman ta a yau, inda waɗanda suka sauya sheƙar suke cewa sun bar jam’iyyar ta PDP ne kan rikicin da ke cikin jam’iyyar.

Sauran waɗanda suka bar PDP sun haɗa da Mataimakin Kakakin Majalisar, Dumle Maol mai wakiltar mazabar Gokana, Major Jack mai wakiltar Akuku-Toru da Linda Stewart mai wakiltar Okrika da Franklin Nwabochi mai wakiltar Ogba/Egbema/Ndoni da Azeru Opara mai wakiltar Port Harcourt 3 da Smart Adoki mai wakiltar Port Harcourt 2 da Enemi George mai wakiltar Asari-Toru da Solomon Wami mai wakiltar Port Harcourt 1.

Har ila yau, sauran sun haɗa da Igwe Aforji mai wakiltar Eleme da Tekena Wellington mai wakiltar Asari-Toru 1 da Looloo Opuende mai wakiltar Akuku-Toru 2 da Peter Abbey mai wakiltar Degema da Arnold Dennis mai wakiltar Ogu/Bolo daChimezie Nwankwo mai wakiltar Etche da Gerald Oforji mai wakiltar Oyigbo da Ofiks Kabang mai wakiltar Andoni.

Da wannan sauya sheƙar, Jam’iyyar APC tana da mambobi 17.

Mambobi 10 da suka rage na PDP a Majalisar sun naɗa Sylvanus Nwankwo na mazabar Omuma a matsayin shugaban marasa rinjaye.