| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Kakakin Majalisar Jihar Ribas da wasu ‘yan majalisa 16 sun sauya sheƙa daga PDP zuwa APC
Majalisar ta gudanar da zamanta a yau, inda waɗanda suka sauya sheƙar suke cewa sun bar jam’iyyar ta PDP ne saboda rikicin cikin gida da ya addabi jam’iyyar.
Kakakin Majalisar Jihar Ribas da wasu ‘yan majalisa 16 sun sauya sheƙa daga PDP zuwa APC
Da wannan sauya sheƙar, Jam’iyyar APC tana da mambobi 17. / Others
5 Disamba 2025

Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Rivers, Martin Amaewhule, ya fice daga Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya koma Jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Amaewhule ya sauya sheƙar ne tare da wasu mambobi 16 na Majalisar a ranar Juma’a.

Majalisar ta gudanar da zaman ta a yau, inda waɗanda suka sauya sheƙar suke cewa sun bar jam’iyyar ta PDP ne kan rikicin da ke cikin jam’iyyar.

Sauran waɗanda suka bar PDP sun haɗa da Mataimakin Kakakin Majalisar, Dumle Maol mai wakiltar mazabar Gokana, Major Jack mai wakiltar Akuku-Toru da Linda Stewart mai wakiltar Okrika da Franklin Nwabochi mai wakiltar Ogba/Egbema/Ndoni da Azeru Opara mai wakiltar Port Harcourt 3 da Smart Adoki mai wakiltar Port Harcourt 2 da Enemi George mai wakiltar Asari-Toru da Solomon Wami mai wakiltar Port Harcourt 1.

Har ila yau, sauran sun haɗa da Igwe Aforji mai wakiltar Eleme da Tekena Wellington mai wakiltar Asari-Toru 1 da Looloo Opuende mai wakiltar Akuku-Toru 2 da Peter Abbey mai wakiltar Degema da Arnold Dennis mai wakiltar Ogu/Bolo daChimezie Nwankwo mai wakiltar Etche da Gerald Oforji mai wakiltar Oyigbo da Ofiks Kabang mai wakiltar Andoni.

Da wannan sauya sheƙar, Jam’iyyar APC tana da mambobi 17.

Mambobi 10 da suka rage na PDP a Majalisar sun naɗa Sylvanus Nwankwo na mazabar Omuma a matsayin shugaban marasa rinjaye.

Rumbun Labarai
Matatar Dangote ta samar da litar fetur 32.02 ga Nijeriya a Disamban 2025, in ji NMDPRA
Gwamnatin Kano ta dakatar da likitocin da suka manta almakashi a cikin wata marar lafiya
Gobara a wasu gidajen mai ta ƙone Keke Napep 17 da tankokin dakon mai biyu a Kano
Nijeriya da UAE sun soke harajin kayayyaki 13,000 da suke cinikayya a kansu
Amurka ta aika kayayyakin soji ga Nijeriya bayan ƙaddamar da ayyukan tsaro na haɗin gwiwa
Rundunar 'yansanda a Nijeriya ta dakile harin da aka kai wa wani sansaninta a Obajana na jihar Kogi
Mutum 33 sun mutu, 33 sun jikkata a wata uku sakamakon hatsarin wutar lantarki a Nijeriya
Muhimman abubuwa kan sababbin dokokin harajin Nijeriya
Sojojin Nijeriya sun ceto mutum 18 daga hannun 'yanbindiga a gaɓar tekun Kamaru
Jami'an tsaro a Nijeriya sun kashe 'yanfashin daji da dama a Jihar Kogi
'Yanbindiga sun kashe mutum huɗu a wani sabon hari da suka kai Jihar Neja
An soma bincike kan zargin sakacin wani asibiti a mutuwar ɗan marubuciya Chimamanda a Legas
Hukumar DSS a Nijeriya ta tabbatar da kama ma'aikacinta kan zargin sace ƙaramar yarinya a Jigawa
Trump ya yi barazanar kai ƙarin hare-hare a Nijeriya
Trump ya ƙara Nijeriya da ƙasashen Afirka 12 a jerin waɗanda za su biya $15,000 na bizar Amurka
An gano wani bam da bai fashe ba a Jihar Neja
Dakarun Nijeriya sun kubutar da wani Kanal mai ritaya da aka yi garkuwa da shi a jihar Filato
An kashe sojojin Nijeriya tara a mummunan harin kwanton-ɓauna a Jihar Borno
Sojojin Nijeriya sun ciro gawarwaki 27 a hatsarin kwale-kwale a Jihar Yobe
Fiye da mutum 50 ne suka mutu a harin 'yan bindiga a jihar Neja ta tsakiyar Nijeriya