| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
3 minti karatu
Iran ta bayyana cikakkun bayanai na shawarwari 14 ga Amurka da nufin kawo ƙarshen yaƙi
Haka kuma shawarwarin sun tabbatar da “dage dukkan takunkumai da kuma kudurorin Majalisar Tsaro ta Majalisar Ɗinkin Duniya, da janye sojojin Amurka daga yankunan da ke kusa da Jamhuriyar Musulunci ta Iran,” in ji shi.
Iran ta bayyana cikakkun bayanai na shawarwari 14 ga Amurka da nufin kawo ƙarshen yaƙi
Iran ta bayyana cikakkun bayanai na shawarwari 14 ga Amurka da nufin kawo ƙarshen yaƙi / AP

A ranar Talata ne Iran ta bayyana cikakkun bayanai na sabuwar shawararta da ta miƙa wa Amurka domin kawo ƙarshen yaƙin da Washington da Isra’ila suka ƙaddamar kan Tehran a watan Fabrairu.

An bayyana cikakkun bayanan ne daga mataimakin ministan harkokin wajen Iran, Kazem Gharibabadi, yayin wata ganawa da mambobin kwamitin tsaro na ƙasa da manufofin waje na majalisar dokoki, inda ya gabatar da cikakken rahoto kan sabbin ci gaba a harkokin diflomasiyya tsakanin Iran da Amurka.

Gharibabadi ya ce shawarwarin Tehran sun jaddada “haƙƙin ƙasar na tace sinadarin uranium da gudanar da ayyukan nukiliya na zaman lafiya,” kamar yadda kamfanin dillancin labarai na hukuma IRNA ya ruwaito.

Shawarwarin kuma sun haɗa da “kawo ƙarshen rikice-rikice a dukkan fannoni, ciki har da Lebanon; ɗage takunkumi kan sojojin ruwan Amurka; sakin kadarorin Iran da aka ƙwace; da kuma biyan diyya daga Amurka kan barnar da aka yi yayin yaƙin na baya-bayan nan domin taimakawa ayyukan sake gina ƙasar.”

Haka kuma shawarwarin sun tabbatar da “dage dukkan takunkumai da kuma kudurorin Majalisar Tsaro ta Majalisar Ɗinkin Duniya, da janye sojojin Amurka daga yankunan da ke kusa da Jamhuriyar Musulunci ta Iran,” in ji shi.

A ranar 10 ga Mayu, Iran ta mika martaninta ga shawarar Amurka da nufin kawo ƙarshen yaƙin ta hanyar Pakistan, amma Shugaba Donald Trump ya bayyana shawarar Iran a matsayin “wacce ba za a amince da ita ba kwata-kwata.”

Kafofin yada labarai na Iran sun ruwaito a ranar Litinin cewa Iran ta sake gabatar da sabuwar shawarwari mai matakai 14 ga bangaren Amurka ta hannun masu shiga tsakani daga Pakistan.

A ranar Asabar, Trump ya sake yin barazanar ƙarin farmakin soja kan Iran, inda ya wallafa hoto a dandalinsa na Truth Social wanda ke nuna jiragen ruwa na yaƙi masu tutar Amurka, ciki har da wani jirgi da ke ɗauke da tutar Iran, tare da rubutun “IT WAS CALM BEFORE THE STORM.”

A yammacin Litinin kuma, Trump ya sanar cewa ya dakatar da wani harin soja da aka shirya kai wa Iran a ranar Talata, bisa buƙatar Saudiyya, Qatar da Hadaddiyar Daular Larabawa.

Ya kuma ƙara da cewa ya umarci Ma’aikatar Tsaro “ta kasance cikin shiri don kai cikakken babban hari kan Iran cikin gaggawa, idan har ba a cim ma yarjejeniyar da ta dace ba.”

Bayan tattaunawar da ta tsaya cak da Pakistan ke shiga tsakani, Amurka ta kakaba toshewar tashoshin jiragen ruwan Iran tun daga ranar 13 ga Afrilu, ciki har da waɗanda ke kan mashigar ruwa mai muhimmanci ta Hormuz.

Iran ta mayar da martani ta hanyar rufe mashigar, tare da tilasta jiragen ruwa su rika neman izini daga Tehran kafin wucewa, a yayin da ake fargabar cewa tsagaita wuta mai rauni da ake da ita tun 8 ga Afrilu na iya rushewa idan ba a cim ma yarjejeniya ba ta kawo ƙarshen yaƙin.

Rumbun Labarai
Amurka ba ta bayar da wani rangwame mai gamsarwa ba a martaninta ga Iran: Kafofin watsa labaran Iran
Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya ta bayar da umarnin sirri don kama jami'an Isra'ila biyar
Ben-Gvir ya sanar da shirin Isra'ila na gina sabbin haramtattun matsugunai a Lebanon
Har yanzu Amurka ba ta ba da bizar Gasar Kofin Duniya ga tawagar ƙwallon ƙafar ƙasarmu ba: Iran
Netanyahu na Isra'ila ya yi tattaunawar sirri a UAE da Al Nahyan yayin yaƙin Iran
Saudiyya ta kai hare-haren sirri kan Iran bayan an kai mata hari — Rahoto
Bayanan sirri na Amurka sun nuna cewa Iran na da iko da makamai masu linazami masu ƙarfi - Rahoto
Fidan ya yi gargadi kan amfani da Mashigar Teku ta Hormuz a matsayin makami a rikicin yankin
An jikkata sojojin Isra’ila takwas yayin kutse a Lebanon duk da yarjejeniyar tsagaita wuta
Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta riƙa kai hare-hare Iran a asirce a yaƙin Amurka da Isra'ila: rahoto
Rusassun cocina, alamomin Kiristanci da salon hare-haren Isra’ila da ke ci gaba a Lebanon
Trump ya kira martanin Iran ga shawarar zaman lafiya abin da 'ba za a lamunta ba kwata-kwata'
Iran ta mayar da martani ga masu shiga tsakani na Pakistan kan shawarar Amurka ta kawo ƙarshen yaƙi
Saudiyya ta musanta zargin bayar da izinin amfani da sararin samaniyarta don ayyukan soja
Iran ta harba makamai masu linzami ga sojin Amurka bayan hari kan tankar dakon manta
Darussa daga sabon tsarin tafiyar da duniya: Ba za a iya sayen tsaro ba, amma dole a gina shi
Trump ya dakatar da shirinsa na taimaka wa jiragen ruwa wucewa ta Mashigar Hormuz
Shugabannin duniya na matsa wa Iran lamba yayin da ake fargabar batun tsagaita wuta zai iya rushewa
Harin da Amurka ta kai Mashigar Hormuz ya kashe fararen-hula 5, a cewar Iran
Iran ta ce duk wani shirin Amurka kan mashigar Hormuz zai zama keta yarjejeniyar tsagaita wuta