Hukumar ƙwallon ƙafa ta Portugal ta ce ba ta amince da shawarar gwarzon ɗanwasanta Cristiano Ronaldo, ta yin ritaya ba tare da karrama shi ba.
Gwarzon ɗanwasan ya sanar da yin ritayarsa daga buga wa ƙasarsa wasa, amma labarin ya zo da bazata, kasancewar ba a daɗe ba ya ayyana cewa zai ci gaba da bugawa tawagar ƙasarsa.
Hukumar ta fitar da sanarwa mai martani ga ɗanwasan, wanda ya sanar da yin ritaya daga bugawa ƙasarsa ranar Alhamis, inda take cewa "Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Portugal ba za ta amince da wannan bankwana ta faru ba tare da karramawar da ta dace ba”.
“Muna da cikakken nufin shiryawa, tsarawa, da shiga hidima da haɗa hannu cike da karsashi a koyaushe don yin karramawar da ta dace ga gagarumin aikin Cristiano Ronaldo, a inda masoya da ƙasar za su jinjina da karrama, ɗanwasan da ya ba mu tarin gudummawa."
Sanarwar ta fara ne da cewa, "Hukumar ƙwallon ƙafa ta Portugal tana bayyana matuƙar godiya ga kyaftin ɗinta na har-abada, Cristiano Ronaldo, wanda a yau ya sanar da yin tabbatacciyar ritayarsa daga tawagar ƙasa."
Fatan cin ƙwallo 1000
"Cikin gagarumar yabawa da bege, Hukumar ƙwallon Ƙafar take bayyana jinjinawa da godiya ga Cristiano Ronaldo saboda fitaccen aikinsa na yi wa ƙasarmu hidima.
“Kyaftin ɗinmu ba wai kawai ɗanwasa na musamman ba ne, shugaba ne mai tasiri, kuma abin misali kan jajircewa, kuma babbar alamar kishi ga tawagar ƙasarmu.”
Tsawon zamaninsa na buga ƙwallon ƙasa-da-ƙasa, Ronaldo ya buga wasanni 234 kuma ya ci ƙwallo 146, tare da kafa tarihin cin adadi mafi girma da wani ɗanwasa ya taɓa ciyowa ƙasarsa a tarihin ƙwallon ƙafa a duniya.
Haka nan sanarwar ta ƙara da cewa, "Duk gumin da ya ɗigar, duka muhimmiyar ƙwallon da ya ci, da duka kambun kyaftin ɗin da ya saka, ya yi ne da alfahari a filin wasa, kuma manuniya ce ta cikakkiyar soyayyarsa ga rigar ƙasarmu."
"Jajircewarsa da tarihin da ya bari ya haura fagen wasa. Cristiano Ronaldo ya ɗaukaka sunan Portugal, ya saka karsashi ga rukunin ‘yanwasa matasa da ke burin bin sawunsa. A wajen da yawanmu, shi ne gwarzon ɗanwasa a duka tarihi!"
A ƙarshe sanarwar ta ce, "Muna godiya gare ka kan duka abin da ka yi, ya kyaftin, nan zai ci gaba da zama gidanka, mu je zuwa ga cin ƙwallaye 1000."




















