| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Sojin ruwan Turkiyya da dakarun Somaliya sun ceto jirgin dakon kaya daga 'yanfashin teku
Ma’aikatar ta ce an aiwatar da aikin ne a ƙarƙashin yarjejeniyar haɗin kai ta tsaro tsakanin Somaliya da Turkiyya, wadda ta ƙarfafa dangataka ta haɗin kai wajen kare bakin tekun Somaliya, inda take tabbatar da tsaron teku da kuma yaƙar fashin teku.
Sojin ruwan Turkiyya da dakarun Somaliya sun ceto jirgin dakon kaya daga 'yanfashin teku
A ƙarƙashin yarjejeniyar ana tsammanin Turkiyya za ta tallafa wa Somaliya wajen kare wuraren tekunta da tsare kadarorin tekunta

Rundunar Sojin Ruwan Turkiyya da Rundunar Sojin Somaliya (SNAF) sun ceto wani jirgin ruwa na dakon kaya MV LATUF, wanda ‘yanfashin teku suka ƙwace a kusa da bakin tekun Somalia, a wani aikin haɗin gwiwa, kamar yadda Ma’aikatar Tsaron Somaliya ta bayyana ranar Asabar.

A wata sanarwar da ta wallafa a shafinta na X, ma’aikatar ta ce an shafe kwanaki 10 ana aikin bayan ‘yanfashin teku sun yi garkuwa jirgin ruwan ranar 17 ga watan Agusta kusa da ifle a gundumar Eyl a arewa maso gabashin lardin Nugaal.

An lalata kwale-kwale huɗun da ‘yanfashin tekun suka yi amfani da su kuma an kashe ‘yanfashin teku 14 a samamen, in ji ma’aikatar.
Ta ƙara da cewa matsi babu ƙaƙƙautawa daga dakarun tsaro ya tilasta wa sauran ‘yanfashin tekun yin watsi da jirgin ruwan.

Daga baya dakarun tsaro sun karɓi cikakkiyar ragamar jirgin mai suna MV LATUF, wanda ya sake soma tafiyarsa cikin aminci, in ji sanarwar.

Ma’aikatar ta ce an aiwatar da aikin ne a ƙarƙashin yarjejeniyar haɗin kai ta tsaro tsakanin Somaliya da Turkiyya, wadda ta ƙarfafa dangataka ta haɗin kai wajen kare bakin tekun Somaliya, inda take tabbatar da tsaron teku da kuma yaƙar fashin teku.

Yayin da take tabbatar da cewa fashin teku babban laifi ne da ke da uƙuba mai tsanani, ma’aikatar ta yi gargaɗin cewa waɗanda ke da hannu a irin waɗannan aika-aikar, tare da masu mara musu baya da kuma duk wanda ke yi kamar ba ya ganinsu, duk za a hukunta su.

Ma’aikatar ta yaba wa dakarun tsaron Somaliya da rundunar sojin ruwan Turkiyya game da haɗin kansu tare da ƙara tabbatar da jajircewarta wajen kare bakin tekun ƙasar da kuma ruwan ƙasar da yaƙar fashin teku da tabbatar da tsaron tafiya a teku.

Wata yarjejeniyar tsaro da tattalin arziki da aka ƙulla tsakanin Turkiyya da Somaliya a watan Fabrairun shekarar 2024 ta ƙunshi dangataka ta tsaro tare da ƙoƙarin ƙarfafa ikon tsaron tekun Somaliya.

A ƙarƙashin yarjejeniyar ana tsammanin Turkiyya za ta tallafa wa Somaliya wajen kare wuraren tekunta da tsare kadarorin tekunta da kuma yaƙar harkokin da suka saɓa wa doka.

Turkiyya ta daɗe tana ba da horaswa na soji da tallafi na inganta ƙwarewa ga Somaliya.