Kotun Hukunta Manyan laifuka (ICC) ta nuna damuwa ranar Jumma’a game da matakin da Chadi ta ɗauka na ficewa daga kotun tana mai kira gare ta sake tunani game da matakin.
Venezuela ta yi shelar ficewarta daga kotun da ke zama a birnin Hague ranar 25 ga watan Yuli kuma Chadi ta bi bayanta bayan kwanaki biyu. Ƙasashen biyu sun zargi kotun da nuna bambanci a bincikenta.
"Shugabanci [na kotun] na nadamar waɗannan matakan," in ji wata sanarwar shugabancin kotun, wanda a halin yanzu ya ƙunshi Finland da Saliyo da Poland.
Ta ce janyewa daga yarjejeniyar Roma da ta kafa Kotun Hukunta Manyan laifuka na "barazanar zagon ƙasa ga ƙoƙarin bai-ɗaya na neman hukunta laifuka tare da raunata ƙoƙarin duniya na kawo ƙarshen rashin hukunta laifuka."
Matsin Amurka
Ta ƙara da cewa: "Kotun ICC tana tsakiyar tsarin duniya na tabbatar da bin gaskiya kuma kyawun aikinta ya dogara ne ga tallafi babu ƙaƙƙautawa da ya fito ƙarara daga ƙasashen duniya."
"Shugabanci [na kotun] ya yi kira ga Chadi da Venezuela su ci gaba da kasancewa ƙasashen da suka yarda da Yarjejeniyar Roma."
Daga farko dai Amurka ta ƙaddamar da farmaki na diflomasiyya kan kotun- wadda ta zarga da barazana ga Amurkawa- tana mai ɗaukar alƙawarin ƙaƙaba mata sabbin takunkumai da kuma kira ga sauran ƙasashe su janye daga kotun.
Dangantaka tsakanin gwamnatin Shugaba Donald Trump da kotun na da rauni inda wasu alƙalai suke fuskantar takunkuman Amurka.
Mayar da hankali kan ƙasashen Afirka
Chadi ta zargi ICC da mayar da hankali kan ƙasashen Afirka. Gwamnatocin Burkina Faso da ta Mali da ta Nijar sun nuna cewa suna son barin ICC.
Venezuela, wadda kotun ta ICC ke bincike a kanta, ta yi irin waɗannan ƙorafe-ƙorafen.
"Venezuela na ganin matakan kotun na nuna bambancin bisa yankuna inda ta fi mayar da hankali kan ƙasashen Afirka da na yankin Latin Amurka," in ji miniatan harkokin waje Felix Plasencia.
AFIRKA
2 minti karatu
Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta yi kira ga Chadi ta janye matakinta na ficewa daga kotun
Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta yi gargaɗin cewa ficewar na barazanar zagon ƙasa ga ƙoƙarin kawo ƙarshen rashin hukunta laifuka.

Rumbun Labarai

















