Hukumar Falasɗinawa ta yi maraba da shirin Kwamitin Tsaro na MDD kan Gaza

Ma'aikatar Harkokin Waje ta yi kira da a gaggauta aiwatar da shirin, ta jadda shirinta na yin aiki tare da ɓangarorin da suke da ruwa da tsaki.

By
Majalisar Tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya ta amince da kudurin da Amurka ta shirya ranar Litinin.

Hukumar Falasɗinwa ta yi maraba da amincewar da Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi da wani ƙuduri da Amurka ta tsara, wanda ya ba da izinin kafa Kwamitin Zaman Lafiya da kuma Rundunar Duniya ta Daidaita lamura a Gaza.

A wata sanarwar Ma'aikatar Harkokin Waje a shafin X ranar Talata, Hukumar Falasɗinu ta kalli ƙudurin a matsayin tabbaci na "tsagaita wuta na dindindin kuma cikakke a Gaza, da isar da agajin jinkai ba tare da tsaiko ba, da kuma hakkin mutanen Falasɗinu na yanke hukuncin kansu da kafa ƙasarsu mai 'yanci."

Ta kuma nuna godiya ga "duk ƙasashen da suka nuna shirin yin aiki tare da Ƙasar Falasɗinu da sauran ɓangarorin da abin ya shafa don tallafa wa ƙoƙarin Falasɗinu na kawo ƙarshen mamaya da kuma cim ma ‘yancin kai."

Jamhuriyar Falasɗinu ta tabbatar da shirinta na yin aiki tare da duk ɓangarorin da abin ya shafa, ciki har da Amurka, mambobin Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya, da ƙasashen Larabawa da na Musulunci, don tallafa wa aiwatar da ƙudurin.

Sannan ta yi kira da a ɗauki matakai nan da nan domin ganin ƙudurin ya fara aiki don kawo ƙarshen wahalar mutanen Falasɗinu a Gaza, da Yammacin Tekun da aka mamaye, da Yammacin Birnin Kudus da aka mamaye.

'Kwamitin Zaman Lafiya'

Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ya amince da wani ƙudurin da Amurka ta tsara a ranar Litinin, wanda ya tanadi kafa Kwamitin Zaman Lafiya da kuma ba da izinin Rundunar Daidaita Duniya don sa ido kan shugabanci, da sake gina, da ƙoƙarin samar tsaro a Gaza.

Ƙudurin da Amurka ta gabatar ya zo a matsayin wani ɓangare na yarjejeniyar tsagaita wuta da musayar fursuna tsakanin Isra'ila da Hamas wacce ta fara aiki a Gaza a ranar 10 ga Oktoba bisa wani shirin maki 20 da Shugaba Donald Trump ya gabatar.

Mataki na farko na yarjejeniyar tsagaita wutar ya haɗa da sakin fursunoni 'yan Isra'ila a musayar fursunonin Falasɗinu.

Shirin ya kuma tanadi sake gina Gaza da kafa sabon sabuwar ba tare da ƙungiyar Hamas ba.

Tun daga Oktoban 2023, fiye da Falestinawa 69,000 ne suka rasa rayukansu, mafi yawansu mata da yara, kuma sama da 170,700 sun samu raunuka a abin da aka kira yaƙin kisan kare-dangi na Isra'ila a Gaza, wanda ya mayar da yankin zuwa tarkace.