| Hausa
Ra'ayi
GABAS TA TSAKIYA
9 minti karatu
Daina taimaka wa sojojin Isra’ila ba ɗaya yake da kawo karshen haɗin baki da ita ba
Matakin da Washington ta ɗauka na kawo ƙarshen tallafin soja na biliyoyin daloli ga Isra'ila duk shekara, ya nuna sauyin matsayin siyasa. Amma ci gaba da sayar da makamai ga ƙasar da ƙara haɗin gwiwar tsaro tsakaninsu na ɗorar da wannan goyon baya.
Daina taimaka wa sojojin Isra’ila ba ɗaya yake da kawo karshen haɗin baki da ita ba
amurka da Isra'ila sun yarda da kawo karshen tallafin a karshen shekarar nan. / َAA / TRT World

Sanarwar da gwamnatin Amurka ta fitar cewa Amurka za ta dakatar da bayar da kusan dala biliyan 4 na tallafin soja da take bai wa Isra'ila duk shekara, a karon farko, wanda hakan ke kama da wani gagarumin sauyi na tarihi.

Babu shakka, wannan mataki yana da matuƙar muhimmanci. Sai dai ya kamata Falasɗinawa su bambanta tsakanin dakatar da bayar da kuɗin tallafin na shekara-shekara da kuma rusa tsarin da ya ba Isra'ila damar aikata tashe-tashen hankula, mamaye yankunan Falasɗinawa da kuma kaucewa hukunta ta kan laifukan da take aikatawa.

A wata hira da gidan talabijin na Fox News, Trump ya yi ikirarin cewa Washington da Netanyahu sun amince da kawo ƙarshen tallafin kafin ƙarshen wannan shekara, saboda Isra'ila ta zama ƙasa mai nasara wadda ba ta buƙatar kuɗin Amurka a yanzu.

Ya ƙara da cewa Isra'ila za ta ci gaba da samun damar sayen makamai daga Amurka, kuma Amurka za ta ci gaba da taimaka mata idan ta buƙaci taimako.

Wannan ba wani mataki ba ne na amincewa da kuskure ko nuna nadama kan abin da ya faru a Gaza bisa dalilai na ɗabi'a. Gwamnatin Trump ba ta ambaci dubban Falasɗinawa da aka kashe, lalata garuruwa baki ɗaya, ko kuma rawar da makaman Amurka suka taka wajen taimakawa wajen aikata waɗannan abubuwan ba.

Gwamnatin Amurka ba ta sanar da sanya takunkumin hana sayar da makamai ga Isra'ila ba, ba ta nemi a hukunta ta kan ayyukanta ba, kuma ba ta sanya sharadin cewa duk wani haɗin gwiwar da za a ci gaba da yi da ita a nan gaba sai ta mutunta dokokin ƙasa da ƙasa ba.

A maimakon haka, ta bayar da wani bayani mai matuƙar nasaba da siyasa. A cewarta, tallafin soja da ake bai wa Isra'ila ya zama wani batu da ke jawo wa 'yan jam'iyyar Republican matsala a fagen siyasa.

Gwamnatin ta yi korafi musamman kan sukar da Abdul El-Sayed, ɗan takarar jam'iyyar Democrat a zaɓen Majalisar Dattawan Amurka na jihar Michigan, yake yi. El-Sayed ya nuna adawa da bayar da goyon baya ga Isra'ila ba tare da sanya wani sharadi ba.

Wannan amincewa da gaskiyar lamarin tana da matuƙar muhimmanci.

Tsawon shekaru da dama, 'yan siyasar Amurka sun ɗauki goyon bayan Isra'ila a matsayin wani abu da ba ya jawo musu wata matsala ta siyasa. Bayar da biliyoyin daloli ga Isra'ila ba ya buƙatar wani cikakken bayani ga jama'a, duk da cewa gwamnatocin Isra'ila daban-daban sun ci gaba da ƙarfafa mamayar yankunan Falasɗinawa, faɗaɗa matsugunan Yahudawa da ba su halatta ba, tare da kai hare-hare akai-akai kan Gaza.

Ana sa ran Falasɗinawa za su amince da cewa tallafin soji na Amurka ga Isra'ila abu ne na dindindin, wanda manyan jam'iyyun siyasar Amurka biyu ke goyon bayansa, kuma ba abin da jama'a za su iya ƙalubalanta ta hanyar dimokuraɗiyya ba ne.

Sai dai wannan kariyar siyasa da Isra'ila ke samu ta fara rugujewa.

Sanarwar gwamnatin Trump ta nuna cewa shekaru da dama na bayyana wa duniya halin da Falasɗinawa ke ciki, shirya fafutuka da kamfen sun sauya yadda 'yan siyasar Washington, DC ke kallon wannan batu.

Hakan ya nuna tasirin ƙoƙarin ɗalibai, masu fafutuka, 'yan jarida, al'ummomin Falasɗinawa, Larabawa da Musulmi, ƙungiyoyin masu adawa da yaƙi, da kuma ƙarin yawan Amurkawa da suka ƙi yarda a mayar da abin da ke faruwa a Gaza wani rikici na ɗan lokaci kawai.

Taimako da ya wuce batun tallafi

Tabbas Amurka ta daina ganin Isra'ila a matsayin ƙasa mai amfani gare ta. Abin da ya faru shi ne, ya ƙara zamar mata da wahala ta kare goyon bayan Isra'ila a gaban al'ummar Amurka.

Kasancewar gwamnatin Amurka ta ga ya zama dole ta sanar da kawo ƙarshen tallafin a daidai lokacin da Amurkawa ke kada ƙuri'a a zaɓe, tare da ambaton sunan El-Sayed kai tsaye, yana nuna irin babban sauyin da aka samu a muhawarar siyasar ƙasar.

Wata manufar da a da ake gabatarwa a matsayin wani abu da ba za a iya tambayar ingancinsa ba, domin wai tana nuna ƙimar Amurka, yanzu ta zama wani batu da ka iya jawo wa 'yan siyasa asarar ƙuri'u a zaɓe.

Hatta Trump, wanda ya bai wa Isra'ila gagarumin goyon baya ta fuskar siyasa da soja, da alama ya yi imanin cewa alaƙa da tallafin da ake bai wa Isra'ila ba tare da wani sharadi ba na iya jawo wa jam'iyyarsa asarar ƙuri'u.

Ya kamata a amince da wannan a matsayin gagarumar nasara ta ƙungiyar fafutukar kare haƙƙin Falasɗinawa. Sai dai bai kamata a ɗauke ta a matsayin ƙarshen rawar da Amurka ke takawa wajen taimakawa Isra'ila a ayyukanta ba.

Shi kansa Netanyahu ya daɗe yana goyon bayan sauya tsarin taimakon Amurka na gargajiya ga Isra'ila.

Kalmar da ya fi so a yi amfani da ita ita ce sauyawa daga tsarin “taimako zuwa haɗin gwiwa”. Wato, Isra'ila za ta daina karɓar tallafin kuɗi na shekara-shekara wanda kowa ke iya gani, amma a lokaci guda za ta faɗaɗa haɗin gwiwa da Amurka wajen ƙirƙira da haɓaka makamai, fasahar soja, musayar bayanan sirri da kuma samar da kayan aikin tsaro.

Wannan ba rabuwa ba ce. A maimakon haka, yana iya zama wata hanya ta zurfafa haɗin kai tsakanin ƙasashen biyu.

Tsarin yarjejeniyar da ake amfani da shi a halin yanzu yana bai wa Isra'ila tallafin dala biliyan 3.8 a duk shekara, wanda galibinsa ake amfani da shi wajen sayen makamai daga Amurka. Wannan yarjejeniya tana ƙarƙashin wata yarjejeniya ta fahimtar juna wadda za ta ci gaba da aiki har zuwa shekarar 2028.

Gwamnatin Trump ba ta bayyana yadda za ta kawo ƙarshen wannan yarjejeniya kafin wa'adinta ba, ko irin kuɗaɗen da za a dakatar da su a zahiri, ko kuma yadda Majalisar Dokokin Amurka za ta mayar da martani. Haka kuma, Netanyahu bai tabbatar a bainar jama'a da yarjejeniyar da Amurka ke ikirarin an cim ma ba.

Abin da ya fi muhimmanci shi ne, kawo ƙarshen wannan yarjejeniya ba zai hana Isra'ila sayen jiragen yaƙi, bama-bamai da makamai masu linzami daga Amurka da kuɗaɗenta ba.

Trump ya bayyana hakan karara, inda ya ce Isra'ila za ta iya ci gaba da sayen duk makaman da take so.

Haka kuma, tallafin Amurka na iya ci gaba ta wasu hanyoyi, ciki har da tallafin kuɗi na kare kai daga makamai masu linzami, tallafin soja na gaggawa, musayar bayanan sirri, lamunin kuɗi, da haɗin gwiwar bincike kan fasahar basirar na'ura (AI), yaƙin yanar gizo, fasahar kimiyyar halittu, tsarin yaƙi da jiragen sama marasa matuƙa (drones), da sauran fasahohin soja.

Tuni dai ake tattauna wasu shawarwari da za su faɗaɗa haɗin gwiwa tsakanin masana'antun tsaro na Amurka da Isra'ila, tare da shigar da wasu sassan wannan alaƙa cikin shirye-shiryen Ma'aikatar Tsaron Amurka sosai.

A wasu kalmomi, tallafin na iya zama wanda ba a cika gani a fili ba, ba tare da rage muhimmancinsa ko tasirinsa ba.

Wannan mataki na iya yi wa Trump da Netanyahu amfani. Gwamnatin Trump za ta iya gaya wa masu zaɓen Amurka cewa kuɗaɗen harajin da suke biya ba za su ƙara zama hanyar biyan kuɗaɗen Isra'ila ba. Shi kuma Netanyahu zai iya ikirarin cewa Isra'ila ta cim ma 'yancin kanta ta fuskar dabarun tsaro.

A halin da ake ciki kuwa, makamai za su ci gaba da kwarara zuwa Isra'ila, masana'antun soja na ƙasashen biyu za su ƙara haɗewa da juna, yayin da Washington za ta ci gaba da riƙe ikon shiga tsakani a duk lokacin da Isra'ila ta buƙaci tallafi.

Kuɗin tallafin zai ɓace, amma hanyar samar da makamai za ta ci gaba da kasancewa.

Duk da irin kariyar siyasa da tallafin gargajiya ke samu, aƙalla ana iya ganin sa a fili. Yana samar da adadi na kuɗi wanda 'yan jarida, masu zaɓe da 'yan majalisa za su iya bincikawa tare da yin tambayoyi a kansa.

Mayar da tallafin zuwa tsarin haɗin gwiwar kasuwanci, kwangilolin tsaro da sayen kayayyakin soja ta hannun Ma'aikatar Tsaron Amurka, na iya sa wannan alaƙa ta zama mafi rikitarwa da wahalar ganewa, wanda hakan zai ƙara wahalar ƙalubalantar ta.

Haka kuma, wannan mataki na iya bai wa Isra'ila damar kauce wa ɗaya daga cikin manyan tambayoyin da yakin Gaza ya haifar: Me ya sa masu biyan haraji a Amurka suke ɗaukar nauyin kuɗaɗen lalata rayukan Falasɗinawa?

Sai dai ƙasa ba za ta kuɓuta daga alhaki kawai saboda ta sauya yadda ake rubuta kuɗin da take biya ba.

Kawo karshen tallafi da hadin gwiwa 

Gwamnatin da take sayar da bama-bamai, yaɗa bayanan sirri, kare waɗanda suka aikata laifuka ta hanyar diflomasiyya, tare da ci gaba da cike ma'ajiyar makamai ta Isra'ila a lokacin yaƙi, tana da hannu a cikin ayyukan da ake amfani da waɗannan makaman.

Saboda haka, a wajen Falasɗinawa, ba za a auna sauyin da aka samu da ko ana bayyana Isra'ila a matsayin ƙasar da ke karɓar tallafi ko kuma ƙawar Amurka ta fuskar dabarun tsaro ba.

Abin da ya kamata a yi la'akari da shi shi ne ko manufofin Amurka sun daina taimakawa wajen ci gaba da mamayar ƙasashen Falasɗinawa, tsarin wariyar launin fata, tilasta wa mutane barin muhallansu da kuma kashe mutane da yawa.

Kawo ƙarshen tallafin soja na shekara-shekara har yanzu zai kasance wani muhimmin mataki. Isra'ila ta more wata dama ta musamman wadda ba a bai wa wata ƙasa mai arziki makamanciyarta ba: samun biliyoyin daloli na tallafin kuɗin sayen makamai daga Amurka wanda aka tabbatar da shi, duk da yawan keta dokokin ƙasa da ƙasa da ta aikata.

Soke wannan dama ta musamman zai karya wani muhimmin jigon siyasa da a da ba a cika ƙalubalantar sa ba, tare da tabbatar da cewa bayar da goyon baya ga Isra'ila ba tare da wani sharadi ba ba wani abu ne da dole ne ya kasance haka har abada ba, kuma ana iya sauya shi.

Sai dai yanzu dole ne ƙungiyar fafutukar neman 'yancin Falasɗinawa ta matsa kaimi fiye da sanarwar da aka yi a kafafen watsa labarai. Buƙatarsu ba za ta tsaya kawai ga cewa: A daina bai wa Isra'ila makamai kyauta ba.