| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Aikin matatar man Dangote zai ci gaba a gaɓar tekun Kenya, a cewar Shugaba Ruto
Shugaba William Ruto ya ce aikin wanda attajirin Nijeriya Aliko Dangote ke mara wa baya zai samar da ayyukan yi 60,000 tare da samar da mai a ƙasashen Afirka 8.
Aikin matatar man Dangote zai ci gaba a gaɓar tekun  Kenya, a cewar Shugaba Ruto
TSOHON HOTO: Shugaban rukunin kamfanonin Dangote , Aliko Dangote

Shugaban Kenya William Ruto ya bayyana ranar Jumma’a cewa shirye-shirye na abin da ake tsammanin za ta kasance matatar mai mafi girma a gabashin Afirka na dab da ci gaba bayan tattaunawa da attaijirin Afirka ɗan Nijeriya, yana mai cewa aikin zai samar da ayyuka kimanin 60,000 ga matasa ‘yan Kenya.

Da yake magana wajen ƙaddamar da mataki na biyu na shirin tallafin gwamnati na Nyota, Ruto ya ce shi ya cim ma wata yarjejeniya da Dangote ta ci gaba da aikin matatar mai, wadda za a gina a jihar Lamu da ke gaɓar teku, kimanin nisan kilomita 470 ( mil 292 ) kudu maso gabas da babban birnin ƙasar Nairobi.

“A yanzu Kenya za ta gina matatar gabashin Afirka a nan Lamu, inda za mu buƙaci matasa 60,000 su yi aiki,” a cewar Ruto.

“Na yi magana da mai zuba jari Aliko Dangote, kuma mun cim ma matsaya cewa matatar man ba kawai Kenya za ta yi wa hidima ba, za ta yi aiki wa Ethiopia da Sudan Ta Kudu da Uganda da Tanzania da Rwanda da Burundi da kuma Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo, yayin da za ta samar da damarmaki na ayyukan yi ga matasa,” a cewarsa.

Cibiyar makamashi ta yanki

Ruto ya ce matatar za ta mayar da Kenya wata cibiyar makamashi ta yanki ta hanyar samar da kayayyaki na man fetur da sinadirai a faɗin gabashi da tsakiyar Afirka yayin da za ta rage dogaron yankin kan tataccen mai da ake shiga da shi.

Aikin ya biyo bayan shawarar da masana’antar Dangote ta yanke ne wajen kafa matatar man a Lamu, lamarin da ya kawo ƙarshen watanni da aka shafe ana jita-jita kan ko za a gina ta a Kenya ko Tanzania.

Matatar, mai girman tace gangar mai 700,000 a kowace rana ana tsammanin za ta kasance matata mafi girma ne a gabashin Afirka da kuma tallafa wa ci-gaban masana’antu a kewayeen hanyar Lamu da Port-South da Sudan zuwa Ethiopia (LAPSSET), wani muhimmin abin more rayuwa na yanki da ke haɗa gaɓar tekun Kenya zuwa ta ƙasashe maƙwabta.

Kamfanin ya ce ana tsammanin aikin gina matatar zai ɗauki kimanin watanni 30 da zarar an fara yinsa.

An zaɓi Lamu ne saboda muhimmancin wurin da yake a bakin tekun Indiya da tashar jiragen ruwa mai zurfi da kuma kusanci da hanyoyin tafiya da wasu ƙasashen gabashi da tsakiyar Afirka mara gaɓar teku ke amfani da su.