| Hausa
NIJERIYA
1 minti karatu
Ɓarayin daji sun ƙaƙaba harajin naira miliyan 40 kan mazauna wani gari a Sokoto
Mai magana da yawun rundunar ‘yansandan Jihar Sokoto, DSP Ahmed Rufai, ya ce rundunar tana sane da rahoton barazanar.
Ɓarayin daji sun ƙaƙaba harajin naira miliyan 40 kan mazauna wani gari a Sokoto
Gwamnan Jihar Sokoto, Ahmad Aliyu Sokoto

Rahotanni daga Nijeirya na cewa mazauna garin Kebbe a ƙaramar hukumar Kebbe ta jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin ƙasar na fuskantar barazanar tsaro bayan waɗanda ake zargin ɓarayin daji ne sun buƙaci mutanen su biya naira miliyan 40, sanna suka yi barazanar kai hari idan ba su biya kuɗin ba.

Majiyoyi daga garin sun bayyana cewa ‘yanta’addan sun fara ba da wa’adin kwanaki biyar ne ga mazauna garin su samo kuɗin kafin su tsawaita wa’adin bayan mutanen sun roƙe su.

Mai magana da yawun rundunar ‘yansandan Jihar Sokoto, DSP Ahmed Rufai, ya ce rundunar tana sane da rahoton barazanar.

“Rundunar tana sane da bayanin kuma ɓangaren da ke yaƙi da garkuwa da mutane na rundunar (AKU) ya riga ya fara aiki a kan bayanin,” in ji shi.

Sai dai kuma ya ƙara da cewa waɗanda ake zargin cewa ɓarayin dajin ne sun riga sun bai wa mutanen garin wa’adin har zuwa ranar Lahadi domin su nemo kuɗin.

 Lamarin ya haddasa damuwa ga mazauna garin, waɗanda ke fuskantar barazanar yiwuwar a kai musu hari idan ba su iya biyan kuɗin ba.