'Yan fashin daji sun kashe mutum 30 a hare-haren da suka kai a Katsina da Kwara
Mazauna wurin sun ce maharan sun kutsa wurin ba tare da wata matsala ba, suna kashe mazauna ƙauyen da kuma ƙona gidaje kafin su tsere.
Aƙalla mutum 30 aka kashe ranar Talata a hare-haren da ‘yan fashin daji suka kai wasu ƙauyuka a jihohin Katsina da Kwara, yayin da mahara ke sabunta hare-hare kan ƙauyuka da ƙona gidaje da motoci da kuma tilasta wa mazauna tserewa.
A jihar Katsina, an kashe aƙalla mutum 20 a lokacin da ‘yan fashin daji suka far ma ƙauyen Doma a mazaɓar Tafoki a ƙaramar Hukumar Faskari.
Mazauna yankin sun ce maharan sun kutsa wurin ba tare da wata matsala ba inda suka kashe mazauna ƙauyen tare da ƙona gidaje da motoci inda daga bisani suka tsere.
Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, shugaban ƙaramar hukumar Faskari, Surajo Aliyu, ya bayyana harin a matsayin na ramuwar gayya kuma mafi muni a cikin ‘yan watannin nan.
“Wannan harin na ramuwar gayya ne, kuma mai muni ne sosai domin ba mu taɓa samun irinsa ba cikin watanni biyar da suka gabata a wannan wuri,” in ji Aliyu.
Ya ƙara da cewa an sanar da jami’an tsaro, amma ba su iya isowa a kan lokaci domin hana kashe-kashen ba.
“A yau sun kashe aƙalla mutum 20. Sun ƙona motoci da gidaje yayin harin mai munin gaske. Mun ba da rahoton lamarin ga jam’ian tsaro, amma ba su iya isowa ba kafin ‘yan fashin su yi aika-aikar,” a cewarsa.
Aliyu ya bayyana cewa an kai gawarwakin waɗanda lamarin ya rutsa da su wurin jana’izar da za a yi da safiyar Laraba a Tafoki.
“Muna taya mutanen Doma da mazaɓar Tafoki da kuma Faskari da ma ɗaukacin mutanen jihar Katsina State jimami, musamman iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su. Allah Ya kawo mana ƙarshen waɗannan kashe-kashe mara dalili,” a cewarsa.
Ƙaramar hukumar Faskari na cikin ƙananan hukumomin da suka ƙulla yarjejeniyar sulhu da ‘yan fashin daji kimanin watanni biyar da suka gabata, wani matakin da ya ɗan kawo zaman lafiya har zuwa lokacin da aka kai hari na baya bayan nan.
Sai dai kuma a jihar Kwara, an kashe aƙalla mazauna wani ƙauye 10 ranar Talata da yamma a lokacin da ‘yan fashi suka far ma ƙauyukan Woro da Nuku a ƙaramar hukumar Kaiama.
Maharan, wadanda ake sa ran sun fito ne daga gandun dajin ƙasa na Borgu daga jihar Neja mai maƙwabtaka , sun far ma ƙuyukan ne da misalin ƙarfe 6 na yamma, in ji rahotanni, inda suka yi ta harbi tare da tayar da hankula mutane . Sun ƙona wasu gidaje yayin harin.
Wani shugaban a wurin, wanda ya yi bayani bisa sharaɗin sakaye sunansa domin dalilai na tsaro, ya tabbatar da adadin waɗanda aka kashe.
Da take mayar da martani, gwamnatin jihar Kwara ta bayyana ɓacin ranta game kashe-kashen, tana mai cewa Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq yana bibiyar lamarin da kansa.
A wata sanarwar da ya fitar da daren Talata, sakataren watsa labaran gwamnan, Rafiu Ajakaye, ya bayyana harin a matsayin wani “nuna takaici na ragwaye” da ‘yanta’addan suka yi a matsayin wani martani ga ayyukan sojin da ake yi a jihar.
“Gwamnan ya yi Allah wadai da harin, wanda ya bayyana a matsayin wani ƙoƙari da ragwaye da ‘yanta’dda ke yi bayan hare-haren daƙile ta’ddanci da aka kai wasu sassan jihar da kuma nasarorin da aka samu kawo yanzu,” in ji sanarwar.
Gwamnatin ta yi iƙirarin cewa an kai harin a daidai wannan lokacin ne domin a kawar halin jami’an tsaro da kuma yin zagon ƙasa ga nasarorin da aka samu kan masu garkuwa da mutane kwanan nan.