Matashin tauraron ƙwallon ƙafa na Spain ɗan asalin Afirka, Lamine Yamal, ya zama abin sha'awa da ƙauna a duniya.
A matsayin ɗaya daga cikin 'yan wasa mafi ƙarancin shekaru a Gasar Cin Kofin Duniya ta FIFA 2026, Yamal ya taimaka wa Spain cin kofin bayan sun doke ƙungiyar Argentina ta Lionel Messi 1-0 a wasan ƙarshe.
Bayan murnar nasarar da kuma yadda lamarin ya zama hanyar shaharar ɗan ƙaramin ƙaninsa Keyne har aka san shi sosai, akwai wani abin game da Yamal: wato alaƙarsa da ƙasashe uku, Moroko, da Equatorial Guinea, da kuma Spain.
An haife shi a ranar 13 ga Yunin 2007 a Esplugues de Llobregat, kusa da Barcelona, daga wani iyali mai al'adu daban-daban.
Mahaifinsa, Mounir Nasraoui, ɗan Moroko ne, yayin da mahaifiyarsa, Sheila Ebana, ta fito daga Equatorial Guinea.
Wannan asali nasa na gauraye tsakanin Arewcaci da Tsakiyar Afirka da kuma al’adun ƙasar Sifaniya, sun sa ya zama na musamman.
Iyalan suna son ƙwallon kafa sosai kuma suna goyon bayansa. Mahaifinsa, wanda tsohon ma'aikacin gidan abinci ne, shi ne malaminsa na ƙwallo na farko, wanda ya fara koya masa tun a kwararo.
Ko bayan rabuwar iyayensa, sun ci gaba da alaƙa cikin mutunci inda suke ƙarfafa masa gwiwar kasancewa mai tawali'u.
Ya fara ƙwallon ƙafa da wuri a ƙananan shekaru. Yamal ya shiga La Masia yana da shekara bakwai bayan gano shi a La Torreta. Babbban abin da ya sa ya zama na daban kuma fitacce ne shi ne natsuwarsa, da kasancewarsa bahago, wato mai amfani da ƙafar hagu wajen yin wasa, da kuma rashin tsoro.
A watan Afrilun 2023, a lokacin da yake ɗan shekaru 15 da wata 9 da kwana 16 kacal, Yamal ya fara buga wa Barcelona wasa, inda ya zama ɗanwasa mafi ƙarancin shekaru da kulob din ya taɓa samu.
A 2024 ya taimaka da ƙwallaye kuma ya ci wasu ƙwallayen a Gasar Euro 2024, inda ya taimaka wa Spain lashe gasar.
Yamal, mai shekara 19 wanda ya kasance yaro mai fikira da nutsuwa da azama a lokacin buga wasa, ya taso ne a unguwar Rocafonda da ke yankin Mataró, kilomita 30 arewa da birnin Barcelona.
Lamine Yamal yana kallon ƙwallon kafa a matsayin misali na "haɗewar al'umma", koda yake yana adawa da wariyar launin fata da ake yi masa wanda yawanci ya danganci asalinsa na Afirka da kuma addininsa na Musulunci.
Ya taɓa cewa ƙa'idarsa ita ce "yin farin ciki da jin daɗin riƙe ƙwallo a ƙafarsa", kuma yana alfahari da asalinsa.
A Gasar Duniya ta 2026 ya sa ƙyalle mai rubutun 'Rocafonda' a kansa ya kuma saka tutocin Maroko da Equatorial Guinea a takalmansa.
Bayan ya ci ƙwallo, ya yi sujjada ta Musulunci don yin godiya ga Allah.
Wasan ƙarshe ya kasance mai cike da tarihi. Yamal ya fafata da Messi mai shekaru 39, wanda a iya cewa sawunsa yake bi a yanzu a Barcelona.
Shekaru da dama da suka gabata, an ɗauki hoton Messi yana yi wa jariri Yamal wanka a wani taron UNICEF. Wannan hoton ya sake bayyana a lokacin Gasar Duniya.
Yamal ya kasance mai tawali'u. Ba ya kwatanta kansa da Messi, yana cewa irin wannan kwatance ba shi da "ma'ana".
Tarihi zai ci gaba da rubuta labarin wannan matashin ɗanwasa, amma tuni ya riga ya zama ɗaya daga cikin zaratan matasan ‘yanwasa da tauraronsu ke haskawa a zamanin nan.


















