| Hausa
Ra'ayi
GABAS TA TSAKIYA
11 minti karatu
Darussa daga sabon tsarin tafiyar da duniya: Ba za a iya sayen tsaro ba, amma dole a gina shi
Iyakacin abin da kudi zai iya saya kenan, kuma kasashen Gulf sun gano katankatanar dogaro kan Amurka ita kadai don kare su daga abokan hamayya na yankin. Iran ta canja ka’idojin wasan.
Darussa daga sabon tsarin tafiyar da duniya: Ba za a iya sayen tsaro ba, amma dole a gina shi
FILE PHOTO: Jirgin yakin Sojin Amurka samfurin B-52 bombers yake sauka a sansanin Sojin Sama na Al Udeid da ke Qatar. / Reuters

Rikice-rikicen da ke ci gaba da wakana tsawon lokaci sun bayyana abu ɗaya a sarari: tsohon tsarin kariya da aka saya yana rugujewa. Abin da zai maye gurbinsa ne zai bayyana tsarin duniya na gaba.

Shekaru da dama, ana ɗaukar tsaro a matsayin wani abu - wani abu da za a iya samu, a biya kuɗi, kuma a bayar da shi a kan lokaci.

Tsarin da yankin Gulf ya bi ya bayyana wannan dabarar karara: a biya Washington isassun kudade, a kafa isassun sansanonin soja, kuma barazanar za ta ci gaba da kasancewa daga nesa. Farashin ya ci gaba da hauhawa, amma dabarar ta ci gaba. Har sai da ta zama ba ta yi aiki ba.

Abin da rikicin Iran-Isra'ila/Amurka, yakin Rasha-Ukraine, da kisan kare dangi na Gaza suka bayyana wa duniya ba wai kawai gazawar wannan ko wancan kawancen ba ne.

Sun fito da rugujewar tsarin tsaro a matsayin haja. A cikin kowanne daga cikin waɗannan rikice-rikicen da ke ci gaba, ma'aunin da ke bayyana ba shi ne adadin kuɗin da wata ƙasa ta kashe kan kwangilolin tsaro ba - ko kowace kasa ta gina wani abu da zai iya jurewa ko kuwa a’a.

Dorewa, ba wai kashe kuɗi ba ne babban kuɗin ayyukan soji a zamaninmu na yau.

Sabon nahawun da ake yaki da shi

Yaƙin Rasha a Ukraine, wanda aka fara a watan Fabrairun 2022, an yi tsammanin zai ci gaba na wani dan lokaci. Yanzu ya wuce shekaru huɗu. Ukraine ta ci gaba da dagewa ba kawai saboda ƙudurinta ba, amma saboda ta gina - kuma ta sami goyon baya daga - wani yunƙurin yaƙi mai ɗorewa.

Rasha ta shiga yaƙin da kasafin kuɗi na tsaro na biyu mafi girma a duniya - amma duk da haka ta kasa mamaye ƙasar da ta raina.

Dalilin abu ne mai sauƙi: a ɗaya ɓangaren ba Ukraine kaɗai ta tsaya ba, har ma da gungun abokan hulɗar Yamma da ke ba da makamai, leƙen asiri, kuɗi, da matsin lamba na takunkumi ta hanyar da aka tsara, mai dorewa.

Ukraine ba ta fita daga wannan yaƙin ba tare da wata matsala ba - nesa da hakan. Amma ta ja da baya ga mamayar da aka tsara da kawo ƙarshenta cikin makonni, ta sake kwace wani yanki mai muhimmanci, kuma ta canza matsayin dabarun da Rasha ke aiki da su.

Mafi muhimmanci, hakan ya nuna wani abu da masu shirya ayyukan soji da za su zo nan gaba ba za su manta ba: cewa ƙasa mai ƙawaye manya, al'umma mai juriya, da kuma sansanin abun duniya za ta iya wuce abokiyar gaba mai arziki wanda ke yaƙi ita kaɗai.

Idan Ukraine ta nuna abin da tsaro mai ɗorewa zai iya cim mawa, Gaza ta nuna abin da rashin dabaru da kayan aiki jnyo wa - ba ga ɓangaren da ya fi rauni ba, amma ga wanda ya fi ƙarfi.

Isra'ila ta ƙaddamar da yaƙin kisan kare dangi a Gaza da ƙarfin soja, goyon diflomasiyya na Amurka, da kuma shiru a karon farko daga Turai.

Haka kuma ta shiga yakin da rashin girmama ga dokar jinkai ta kasa da kasa, ƙa'idojin kare fararen hula.

A ƙasa, Isra'ila ta cim ma manufofin muhimmai: sake mamaye yankunan Gaza, matsin lamba mai ɗorewa a Gabar Yamma da aka mamaye, da kuma lalata kayayyakin more rayuwa na ƙungiyar Hamas mai fafutukar Kare Falasɗinawa.

Ta hanyar ma'aunin harin soja na yau da kullun, waɗannan riba ce mai ma'ana. Amma yanzu an daina auna yaƙi a murabba'in kilomita.

Rarrabuwar goyon bayan Turai ya zama lamarin da ba za a iya watsi da shi ba. Ireland, Sfaniya, Norway, da Belgium sun yi zama sosai kan batun ɗaukar matakin diflomasiyya da na shari'a.

Amma ko a cikin ƙasashen da suka ci gaba da kusantar Isra'ila - Birtaniya, Jamus, da Italiya - muryoyin hukuma sun ƙara karya matakai, suna kira da a tsagaita wuta, a sanya takunkumi kan makamai, a kuma sami damar shiga ayyukan jinkai.

An shiga tsakani a Kotun Shari'a ta Duniya. Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya ta bayar da sammacin kama shugabannin Isra'ila.

Kamfanoni da ke aiki a ƙarƙashin tsarin ESG suna sake duba yadda suke bayyana kansu a hankali.

Kuma wataƙila mafi muhimmanci na dogon lokaci: a harabar jami'o'i daga London zuwa Los Angeles, ra'ayin goyon bayan Falasɗinawa ya ƙaru a hankali, duk da cewa wasu gwamnatoci sun matsa lamba don takaita ko kuma sanya irin wannan furuci ya zama laifi.

Ƙoƙarin danne muhawara, a lokuta da yawa, ya ƙara zurfafa shi. A duk faɗin Kudancin Duniya, matsayin diflomasiyyar Isra'ila ya yi lalacewa mai tsanani - kuma babu nasarar soja da za ta iya gyara hakan.

Isra'ila na iya mallakar iyakoki fiye da yadda ta yi a watan Oktoban 2023. Amma tana zaune a wata duniya ta daban - wacce keɓancewarta ta dabarun ya ƙara zurfafa a kowane wata.

Wannan shi ne rashin jituwar nasarar gajeren lokaci a zamanin iya tuna abu da daukar nauyi na tsawon lokaci.

Ƙasa za ta iya cin nasara a yaƙin kuma ta rasa yanayin da ke sa tsaro a nan gaba ya yiwu: halascin ƙasashen duniya, haɗin kan tattalin arziki da zurfafa haɗin gwiwa.

A Gaza, duniya ta kalli ainihin lokacin da ƙarfin soja ya nuna cewa ƙarfin kai hare-hare da dauwama ba su da alaƙa.

Tsarin tsaro mai karko da dorewa

Abin da waɗannan shari'o'in suka yada- da kuma abin da babban sauyin yankin Gulf ya bayyana a sarari - wani sauyi ne na tsarin da tsaro ke nufi a zahiri.

Tsohuwar dabarar ta kasance mai sauƙi: kuɗi yana sayen ƙarfin soja, ƙarfin soja yana samar da tsaro. Kasashen Gulf sun shafe shekaru da yawa suna gwada wannan dabarar, kuma sakamakon ya kasance mai koyar da darussa.

Saudiyya ta biya ɗaruruwan miliyoyin daloli don karɓar bakuncin sojojin Amurka a ƙasarta - sojojin da aka yi niyyar hana barazanar waje da su amma suka zama tushen tashin hankali na siyasa, kuma a karshe suka zama wadnad aake kai wa hari ma.

An sake lissafa wuraren aikin sojojin Amurka a faɗin yankin Gulf a jerin wuraren da Iran ta ayyana z ata kai wa hari. Wuraren da ake tsammanin za su samar da tsaro, a zahiri, sun zama wani ɓangare na yanayin barazanar.

Kunshin tsaro da aka saya bai haɗa da abin da ke cikin rasitin ba.

Tabbataccen tsaro a yau yana buƙatar wani abu daban: zurfafar masana'antu wanda za su iya aiki ƙarƙashin takunkumi da katsewar sayen kayayyaki; tsarin abinci da makamashi waɗanda ba sa yin garkuwa da yanayin siyasa; karfin fasaha a fannin jiragen sama marasa matuƙa, yanar gizo, da sadarwa waɗanda ba za a iya kashe su ta hanyar shawarar gwamnatin ƙasashen waje ba.

Kuma yana buƙatar haɗin kai na zamantakewa wanda ke sa al'umma su jure maimakon su yi rauni a ƙarƙashin matsin lamba.

Babu ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan da za a iya sayen su daga wani ɗan kwangila na ƙasashen waje. Dole ne a gina su - tsawon shekaru da yawa - ta hanyar manufofi na gaske da kuma kyakkyawar aniyar siyasa. Wannan shi ne dalilin da ya sa dabarun gogayya tsakanin manyan kasashe masu ƙarfi suka canza.

Ba wai kawai batu ne na waye ya fi kashe kuɗi ba. Ya zama batu game da wanda ya gina wani abu da zai dawwama.

Duk da haka, akwai darasi na biyu da ke tafiya tare da hujjar dorewa - kuma yana iya zama daidai da muhimmanci kamar ta.

A cikin duniyar da babu tsarin kawance ɗaya da ya isar wa dukkan barazanar da ƙasa ke fuskanta, sassaucin dabaru ya zama ƙwarewar samun tsira.

Kasashen Gulf sun fahimci wannan tun da daɗewa. Saudiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa, da Qatar sun shafe shekaru goma da suka gabata suna zurfafa dangantaka da China da Rasha yayin da suke ci gaba da kulla alakar tsaro da Amurka.

Dangantakar mai karfi tsakanin Saudiyya da Pakistan — wadda aka gina a kan muradun hana rikici da kuma dogaro da juna a fannin kuɗi — ta zama ɗaya daga cikin haɗin gwiwa mafi muhimmanci a yankin, kuma wacce ba ta cikin tsarin haɗin gwiwar ƙasashen yamma da aka saba gani.

Ma'anar ita ce mai sauƙi: tsaron tattalin arziki yana buƙatar rukunin abokan hulɗa guda ɗaya. Ci gaban fasaha yana buƙatar wani. Hana soja na iya buƙatar na uku. Yanayi da tsaron abinci suna buƙatar tsarin haɗin gwiwa da yawa waɗanda suka shafi duk abubuwan da ke sama.

Ƙasar da ta dage kan haɗin gwiwa da bangare ɗaya don magance duk waɗannan fannoni za ta sami kanta ba ta da amfani ga mafi yawancin su.

Turkiyya da karfi mabambanta da ake da su

Pakistan tana ba da kandagarkin makaman nukiliya. Turkiyya tana kawo zurfin fasaha da aiki - musamman a tsarin jiragen sama marasa matuki. Saudiyya tana ba da gudunmawar tanadin kuɗi da samun kayan aiki.

Haɗin gwiwar Saudiyya da Pakistan, wanda aka zurfafa ta hanyar haɗin gwiwa tsakanin sha'awar tsaro da alaƙar tattalin arziki, yana nuna wani yanayi mai faɗi: kasashe ba wai kawai suna zaɓar ɓangarori ba ne cikin sauki.

Suna zaɓar ayyuka - kuma suna gina ƙawance daban-daban don biyan buƙatu daban-daban.

Tambayar ba "wane sansani kuke ciki ba?" Tambayar ita ce "wane haɗin gwiwa kuke yi da ke ba ku abin da kuke buƙata, don wane ƙalubale na musamman, a kan wane takamaiman lokaci?"

Wanda ya kawo mu ba makawa ga Turkiyya - kuma ba a matsayin tunani na baya ba, sai wataƙila misali mafi bayyananuwa na sabbin manufofin ƙasa na hulɗar bangarori da yawa.

A lokaci guda, Turkiyya mamba ce ta NATO wadda take da tasiri a matakan kawance kan batutuwa tun daga shigar Sweden zuwa fitar da jiragen sama marasa matuki; ƙasa da ke tattaunawa don shiga Tarayyar Turai amma a kullun tana zurfafa dangantakarta ta tattalin arziki da diflomasiyya da Moscow; tattalin arzikin G20 da ke tattaunawa kan batutuwan da suka shafi BRICS; ƙasa da ke shiga taron ƙungiyar haɗin gwiwa ta Shanghai a matsayin abokiyar aiki; kuma ƙasa da ta sanya kanta a matsayin muhimmiyar ƙasa ga lissafin kusan kowace babbar ƙasa a cikin rikice-rikice daga Libya zuwa Syria zuwa tekun Bahar Maliya.

Wannan ba sabani ba ne. Dabaru ne - na gaske da ake gina abinda za a iya kira mai matuƙar muhimmanci.

Turkiyya ta fahimci hakan kafin yawancin takwarorinta a cikin tsarin duniya mai rarrabuwar kawuna su gane hakan, ƙasar da za ta iya hulɗa da kowa tana da tasiri mai ɗorewa fiye da ƙasar da ta fi kusantar bangare ɗaya.

Ankara ba ta sanya kanta a matsayin ƙasa mai kama da kuli-kuli da za a yi kulla alaka da ita ba, sai a matsayin wata hanya da dole manyan kasashen da ke fafatawa da juna za su bi ta cikin ta don yin tattaunawa masu muhimmanci.

Yarjejeniyar hatsi da aka kulla a Istanbul a shekarar 2022 ba wai arashin yanki ba ce.

Wannan ya samo asali ne daga shekaru da dama na gina dangantaka da Moscow da Kiev - dangantakar da Washington ba za ta iya kwaikwayon ta ba, kuma Brussels ta yi tsauri sosai ta ma iya yin yunkurin yin hakan.

Turkiyya ta yi aiki a matsayin mai shiga tsakani mai muhimmanci saboda ta ƙi amincewa ta zama saniyar ware da ke can gefe.

Hakanan ma'anar ta shafi rawar da Turkiyya ta taka a tattaunawar Hamas da Isra'ila, a diflomasiyyar Caucasus, da kuma cikin tsarinta mai sarkakiya na sarrafa iyakokin Syria.

A kowane hali, amfanin Ankara ga tsarin ƙasa da ƙasa ya samo asali ne daga ƙin sadaukar da sassauci don jin daɗin daidaiton akida.

Duniya da aka bayyana a nan - inda ake gina tsaro maimakon sayen sa, inda nasarori gajeru ke ɗaukar dogon lokaci, kuma inda haɗin gwiwa sassauƙa ya fi aminci ga ƙawance na musamman.

Amma ita ce duniyar da ke wanzuwa.

Ƙasashen Gulf suna sake tsara tsarin tsaronsu don yin aiki da shi. Ukraine tana fafutukar neman 'yancin zama a cikin kasar. Isra'ila tana bankade-bankade, tare da babbar asarar ɗan adam, abind aya ci a ce ta yi watsi da shi.

Kuma Turkiyya wataƙila misali ce mafi bayyanuwa wajen zama a tsakiya, wadda ke kan hanyarta ta zama mai karfin iko, ba wai kawai za ta iya tsira daga wannan sauyi ba, har ma ta tsara yadda zai kasance.

Darasin da ya fito daga Kiev zuwa Gaza, daga Riyadh zuwa Ankara, a ƙarshe yana haɗuwa a kan wannan batu: mafi ƙarfin abinda ƙasa za ta iya ginawa ba shi ne dandamalin makamai ba, ajiyar kuɗi, ko makwantar soja ba.

Mataki ne a duniya wanda babu abokin gaba ɗaya da zai iya kawar da shi - kuma babu abokin tarayya ɗaya da zai iya barin sa.

Wannan shivne yadda tsaro mai ɗorewa yake. Kuma wannan shivne kawai nau'in da ya cancanci a samu.