| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Amurka ta kai sabbin hare-hare a wuraren soji a kudancin Iran — rahoto
An kai harin ne wajen da aka yi amanna cewa yana barazana ga dakarun Amurka da sufurin jiragen ruwa na kasuwanci a Mashigar Hormuz, kamar yadda rahoton ABC News ya bayyana.
Amurka ta kai sabbin hare-hare a wuraren soji a kudancin Iran — rahoto
Yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta fara aiki a ranar 8 ga Afrilu ta hanyar shiga tsakanin Pakistan, amma tattaunawar da aka yi a Islamabad ta gaza samar da yarjejeniya mai dorewa. (HOTO NA TARIHI) / Reuters

Amurka ta gudanar da sabbin hare-hare ta sama kan wani wurin soja a kudancin Iran, in ji rahoton wani gidan talabijin Amurka yana ambato wani jami'in Amurka.

Farmakin ya nufi wurin da ake tsammanin yana barazana ga sojojin Amurka da kuma zirga-zirgar jiragen kasuwanci a Mashigar Hormuz, kamar yadda jami'in ya shaida wa ABC News a ranar Laraba.

Tun da farko, yayin da yake tofa albarkacin bakinsa kan tattaunawar kawo ƙarshen yaƙin da aka yi da Iran, Shugaban Amurka Donald Trump ya ce “ban gamsu da ita ba, amma za mu gamsu. Ko dai hakan, ko kuma mu gama aikin baki ɗaya.'

Tashin hankali a yankin ya sake kunnu kai ne a ranar 28 ga Fabrairu, lokacin da Amurka da Isra'ila suka kai hare-haren da ba a yi tsammani ba a kan Iran, abin da ya sa Tehran ta mayar da martani da harin jiragen sama marasa matuki da makamai masu linzami a fadin yankin, tare da rufe Mashigar Hormuz.

Tsagaita wuta ta fara aiki a ranar 8 ga Afrilu ta hanyar shiga tsakanin da Pakistan ta yi, amma tattaunawar da aka yi a Islamabad ba ta haifar da yarjejeniya mai ɗorewa ba.

Daga bisani Trump ya tsawaita zaman tsagaitawar wutar, yayin da ya ci gaba da hana jigilar jiragen ruwa da ke shiga ko fita daga tashoshin Iran ta wannan mahimmin hanyar ruwa, kana lokaci-lokaci yana cewa an kusa cimma yarjejeniyar ta zaman lafiya.