Gaskiya mai ɗaci: Yadda rashin haraji mai yawa kan lemuka da giya ke illata lafiyar mutanen Afirka

Rashin haraji mai yawa da sauƙin samuwar lemukan sha da giya ya zama wani sassauƙan mataki, wanda yake haifar da jidalin taɓarɓarewar lafiyar al'umma a nahiyar Afirka.

By
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta alakanta raunuka da tashin hankali masu nasaba da barasa kai tsaye da samun barasa mai arha. Hoto: Christopher Black / WHO

Samuel Omondi, direban tasi mai shekaru 34 a Nairobi, a da yana shanye kwalabe biyu ko uku na lemo mai sukari, a awanni 12 na aikinsa, wanda ya ƙunshi zirga-zirga a cikin birnin mai cunkoso.

"Shi ne abin da yake ƙara min kuzari," in ji shi, a lokacin da yake ɗan hutawa a tasharsu ta ‘yan tasi a babban birnin Kenya. "Ga araha, ga zaƙin ɗanɗano, kuma koyaushe yana ba ni ƙarin kuzari don ci gaba da aiki."

A bara, an gano Samuel yana da ciwon suga na Nau'i na 2. Mahaifi ne ga yara uku kuma yanzu yana kashe babban ɓangare na abin da yake samu kan magunguna da gwaje-gwaje na mako-mako.

Yana riƙe da kwalbar ruwa ya shaida wa TRT Afrika cewa, "Na zata ina kawar da ƙishirwa ne kawai. Ban san ina shan abin da zai jefa ni cikin rashin lafiya ba. Da a ce lemun nan ya kasance mai tsada fiye da haka, wataƙila da daɗewa da na zaɓi ruwa."

Dubunnan milamilai daga can, a Lusaka na Zambia, ɗalibar jami'a mai shekaru 19, Chileshe Banda, ta rasa ɗan-uwanta a bara cikin haɗarin mota sakamakon tuƙin mota cikin maye.

"Giiya tana nan ko'ina a wannan yanki, kuma tana da araha sosai tamkar kana sayen iska," in ji Chileshe da yake zantawa da TRT Afrika. "Ta sace min ɗan-uwana."

Direban ya kasance yana shan giya mai ƙarfi, kuma mai araha, wadda ake samun ta cikin sauƙin farashi ƙasa da farashin ruwan roba a wasu wurare.

Dabaibayin haraji

Ga iyalin Chileshe, giɓin tattalin arziƙi da kuma na tunani ba zai kau ba. Wannan haɗari kuma ya nuna dalilin da ya sa Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ke danganta rauni da tarzoma wadda samuwar barasa mai araha ke haifarwa.

Labaran Samuel da Chileshe shidu ne na matsalar lafiya a faɗin nahiyar Afirka wadda ke faruwa saboda ƙanƙantar haraji mai kan abinsha mai sukari da barasa. Bincike da dama na WHO sun nuna cewa yayin da waɗannan kayayyaki suke raguwa a farashi, jidalin cututtuka da suke haifarwa yana nauyi kan tsarin lafiya yana ƙaruwa.

"Harajin lafiya na ɗaya daga cikin ƙarfafan kayan aikin da muke da su don inganta lafiya da hana cutuka," in ji daraktan WHO, Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus.

WHO na ƙarfafar gwamnatoci su "ƙarfafa sosai" waɗannan haraji, tana gargaɗin cewa, rauni harajin lafiya yana barin kayayyaki masu cutarwa su ci gaba da kasancewa masu araha, yayin da al'umma ke ɗaukar nauyin matsalar da suke haifarwa mai dogon zango.

Duk da cewa ƙasashen Afirka da dama sun gabatar da irin waɗannan haraji, sau da yawa suna kan matsayi mara tasiri kuma ba za su canja halayyar mutane ba sosai. WHO ta ruwaito cewa matsakaicin haraji kan lemu mai sukari gamagari ba ya kai kashi 2% na farashinsa, kuma yawanci ba ya shafar jerin kayan da ke da sukari mai yawa, kamar ruwan 'ya'yan itace da madaran da aka ƙara wa sukari.

Tsarin manufofi mara jituwa

Kan barasa, matsakaicin harajin a duniya yana da ƙanƙanta har ba shi da mahimmanci idan aka kwatanta da na wasu kayayyaki. A ƙasashe da dama, waɗannan harajin ba a daidaita su da hauhawar farashi, wanda ke sa giya, barasa da giya mai ƙarfi su zama masu araha, ga kuma yawaitar masu amfani da ke ƙaruwa.

"Barasa mai araha na haifar da tashin hankali, raunuka har da cututtuka," in ji Dr Etienne Krug, daraktan sashen fayyace lafiyar na WHO. "Yayin da masana'antu ke samun riba, lafiyar jama'a tana ɗaukar mummunan sakamakon amfani da waɗannan kayayyaki a matakin yawa."

A yayin yawaitar waɗannan kayayyaki da kuma taimakon gudanarwa da suke samu, ƙasashen Afirka da dama sun aiwatar da haraji kan abinsha mai sukari. Afirka ta Kudu ta jagoranci ƙaddamar da harajin inganta lafiya, "Health Promotion Levy" wadda ta fara a 2018. Maroko, Tunisia, Seychelles, Mauritius, Namibia, Botswana da Eswatini sun bi sahu.

Kenya na saka haraji kan abinsha mai sukari, yayin da Uganda, Zambia da Nijeriya su ma suka aiwatar da harajin. Manufofin haraji na Nijeriya na ci gaba da zama abin muhawara game da aiwatarwa da ƙarin harajin da ake caji.

Matsin lamba a wasu wurare

Dangane da ƙiyasin WHO, matakan haraji a cikin waɗannan ƙasashe da dama har yanzu ba su kai ba, domin rage sha ko samar da kayan zaƙi, da kuma inganta samun manyan kuɗaɗen shiga ga harkar kiwon lafiya.

Masana manufofi sun yarda cewa dole ne harajin 'zunubi' ya kasance mai tsoka, da faɗi da zai shafi duk kayan da ke ɗauke da sukari, kuma a daidaita shi akai-akai da hauhawar farashi, da karuwar ƙaruwar albashi domin hana waɗannan abubuwa su kasance masu araha a tsawon lokaci.

Sabon shirin WHO mai taken "3 by 35" yana da niyyar ƙara farashin ainihi na taba, barasa da abinsha mai sukari zuwa shekarar 2035. Ga gwamnatocin Afirka, saƙon ya fito fili: jan hankali na ɗan lokaci na abubuwan shan da suka yi araha ana biyan sa ne a asibitoci da ɗakunan jana'iza ta hannun mutane kamar Samuel da iyalai kamar na Chileshe.

A Nairobi, Samuel yanzu yana aiki a matsayin mai sa-kai a asibitin unguwarsa, a matsayin mai wayar da kan jama'a game da illolin abinsha mai sukari. "Dole ne mu sanya zaɓin lafiya ya kasance mafi sauƙi a wajen zaɓi," in ji shi.

A Lusaka, Chileshe na kiran a yi adalci ta hanyar rigakafi. "A ƙara haraji kan barasa. A sanya ta zama mai wuyar samu a yi sha da gaggawa. Idan zai ceci rai ɗaya, ya yi daraja," in ji shi ga TRT Afrika.