Jagoran Addini na Iran, Mojtaba Khamenei, ya umarci manyan kwamandojin sojin ƙasar da su mayar da martani nan take tare da kai hare-hare a duk inda ya dace, ba tare da taƙaita harin zuwa wani yanki ba, idan Amurka ko Isra'ila suka sake kai wa Iran hari.
Wannan umarni na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙara hasashen yiwuwar sake barkewar yaƙi a Gabas ta Tsakiya.
A cewar wata sanarwa daga ofishinsa, Khamenei ya gana da manyan jami'an soji a ranar Asabar.
A cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafinsa na intanet, Khamenei ya ce: “Duk wani mataki ko nau'in barazana dole ne a fuskance shi da martani nan take, mai tasiri, kuma ba tare da takaita shi ga wani yanki na ƙasa ba.”
Sanarwar ta ce ya bayar da wasu umarni masu muhimmanci da suka shafi dabarun yaƙi, amma ba ta yi cikakken bayani kan taron ba. Ofishinsa ya ce za a wallafa ƙarin bayanai kan umarnin cikin 'yan sa'o'i masu zuwa.
Gargaɗi ga Amurka
A wata sanarwa ta daban da aka wallafa a shafinsa na Telegram, Khamenei ya gargaɗi Amurka kan yiwuwar sake kai hare-hare kan Iran.
Sanarwar da aka danganta da shi ta ce: “Idan maƙiya suka sake kai hare-haren soji ko na ta'addanci, rundunar sojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da al'ummar ƙasar ne za su yanke lokacin da kuma sharuddan kawo ƙarshen waɗannan hare-hare.”
Sanarwar ba ta ambaci wata takamaimiyar sabuwar barazana ba. Sai dai hakan na zuwa ne yayin da ake ƙara hasashen cewa za a iya sake samun barkewar faɗa tsakanin Iran da maƙiyanta.
Amurka da Isra'ila sun ƙaddamar da hare-hare kan Iran a ranar 28 ga watan Fabrairu. Iran kuma ta mayar da martani ta hanyar kai hare-hare kan Isra'ila da sansanonin sojin Amurka da ke yankin.
Daga bisani, ɓangarorin biyu sun cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta a watan Afrilu, lamarin da ya kawo ƙarshen zangon farko na faɗan.
Sai dai ƙoƙarin rage zaman tankiya tsakanin ɓangarorin ya fuskanci tsaiko.
A ranar 18 ga watan Yuni, Washington da Tehran sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna kan 'yancin zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar ruwan Hormuz, wadda tana ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin jigilar kayayyaki ta ruwa a duniya.




















