Yaƙin Gabas ta Tsakiya ya haifar da tsaiko mafi girma a tarihi a wurin samar da man fetur

Ana fargabar samar da mai a duniya zai ragu da kimanin ganga miliyan 8 a kowace rana a watan Maris saboda toshe Mashigin Hormuz.

By
Ƙasashen Gulf na Gabas ta Tsakiya sun rage samar da mai da aƙalla ganga miliyan 10 a duk rana / Reuters

Yakin Gabas ta Tsakiya yana haifar da tsaiko mafi girma a tarihi wurin samar da man fetur, in ji Hukumar Makamashi ta Duniya (IEA) a ranar Alhamis, kwana guda bayan hukumar ta amince da fitar da adadin mai mafi yawa a tarihi daga ma’ajiyarta.

Ana fargabar samar da mai a duniya zai ragu da kimanin ganga miliyan 8 a kowace rana a watan Maris saboda toshe Mashigin Hormuz, wata tsukakkiyar hanar ruwa a Tekun Iran, tun bayan da Amurka da Isra'ila suka fara kai farmaki ta sama kan Iran a ranar 28 ga Fabrairu.

Ƙasashen Gulf na Gabas ta Tsakiya sun rage samar da mai da aƙalla ganga miliyan 10 a duk rana — adadi da ya kai kusan kashi 10 cikin ɗari na abin da ake buƙata a duniya sakamakon rikicin, in ji IEA a sabon rahotonta na wata-wata kan kasuwar mai.

Ta ƙara da cewa idan ba a yi gaggawar ci gaba da jigilar man fetur ba wannan asarar za ta ci gaba da ƙaruwa.

“Dakatar da aikin haƙo man fetur zai ɗauki makonni a wasu wuraren ma watanni kafin a koma yadda ake kafin wannan rikici inda ya danganta ne da ga yanayin dagulewar al’amuran da kuma lokacin da ma’aikata da kayan aiki da sauran albarkatu suka koma yankin,” in ji hukumar.