| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Yaƙin Gabas ta Tsakiya ya haifar da tsaiko mafi girma a tarihi a wurin samar da man fetur
Ana fargabar samar da mai a duniya zai ragu da kimanin ganga miliyan 8 a kowace rana a watan Maris saboda toshe Mashigin Hormuz.
Yaƙin Gabas ta Tsakiya ya haifar da tsaiko mafi girma a tarihi a wurin samar da man fetur
Ƙasashen Gulf na Gabas ta Tsakiya sun rage samar da mai da aƙalla ganga miliyan 10 a duk rana / Reuters
12 Maris 2026

Yakin Gabas ta Tsakiya yana haifar da tsaiko mafi girma a tarihi wurin samar da man fetur, in ji Hukumar Makamashi ta Duniya (IEA) a ranar Alhamis, kwana guda bayan hukumar ta amince da fitar da adadin mai mafi yawa a tarihi daga ma’ajiyarta.

Ana fargabar samar da mai a duniya zai ragu da kimanin ganga miliyan 8 a kowace rana a watan Maris saboda toshe Mashigin Hormuz, wata tsukakkiyar hanar ruwa a Tekun Iran, tun bayan da Amurka da Isra'ila suka fara kai farmaki ta sama kan Iran a ranar 28 ga Fabrairu.

Masu AlakaTRT Afrika - Farashin gangar ɗanyen mai ya ɗara $100 yayin da yaƙin Gabas ta Tsakiya ke ƙamari

Ƙasashen Gulf na Gabas ta Tsakiya sun rage samar da mai da aƙalla ganga miliyan 10 a duk rana — adadi da ya kai kusan kashi 10 cikin ɗari na abin da ake buƙata a duniya sakamakon rikicin, in ji IEA a sabon rahotonta na wata-wata kan kasuwar mai.

Ta ƙara da cewa idan ba a yi gaggawar ci gaba da jigilar man fetur ba wannan asarar za ta ci gaba da ƙaruwa.

“Dakatar da aikin haƙo man fetur zai ɗauki makonni a wasu wuraren ma watanni kafin a koma yadda ake kafin wannan rikici inda ya danganta ne da ga yanayin dagulewar al’amuran da kuma lokacin da ma’aikata da kayan aiki da sauran albarkatu suka koma yankin,” in ji hukumar.

Rumbun Labarai
Hare-haren Iran sun lalata fiye da gidaje 1,000 tare da mayar da su kufai a Tel Aviv - Magajin Gari
Iran ta kama mutum 127 kan zargin taya abokan gaba shirya kai mata hari ta ƙasa
Trump ya ce za a yi amfani da ‘manyan katafilolin tone kasa’ don kwashe sinadarin Uranium daga Iran
Iran ta sanar da bude Mashigar Ruwa ta Hormuz ga dukkan jiragen ruwan duniya
Jakadan Iran a MDD ya bayyana ƙawanyar Amurka a matsayin 'matakin tsangwama'
Pakistan na neman fara sabuwar tattaunawa tsakanin Amurka da Iran don tsara yarjejeniyar nukiliya
Wasu jiragen ruwa suna sauya hanya daga Mashigar Hormuz zuwa ta Oman
Ministan Isra’ila ya soki Shugaban gwamnatin Jamus kan gargadinsa na mamayar Gabar Yamma
Saudiyya ta bukaci Amurka ta janye matakin rufe Mashigar  Hormuz: Rahoto
Iran ta zargi ƙasashen Larabawa biyar da hannu a hare-haren Amurka-Isra’ila, ta nemi a biya ta diyya
Isra’ila na iya ɗaukar Turkiyya a matsayin babbar maƙiyiya a yankin bayan Iran: Fidan
Trump na duba yiwuwar kai wa Iran sabbin hare-hare — rahoto
Amurka da Iran sun gaza cim ma yarjejeniyar zaman lafiya a tattaunawarsu a Pakistan
Amurka ta ce China na shirin kai wa Iran makaman kare sararin samaniya – Rahoto
Jagoran Addinin Iran ya ce an buɗe ‘sabon babi’ kan kula da Mashigar Hormuz, ya nemi diyyar yaƙi
Trump ya yi gargaɗin mayar da martanin soji idan ba a cika alƙawuran yarjejeniya da Iran ba
Iran ta ce Amurka ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta
Iran na iya janyewa daga yarjejeniyar tsagaita wuta idan Isra'ila ta cigaba da yaƙar Lebanon: Rahoto
Sharuɗɗa 10 na zaman lafiya da Amurka ta amince da su a yarjejeniyar tsagaita wuta da Iran
Mazauna Tehran sun fada halin rashin tabbas bayan barazanar Trump ta baya bayan nan