| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
An gano gawarwaki 61 bayan harin ta'addanci a jihar Neja ta Nijeriya
Harin ya janyo ɗaruruwan mazauna yankin sun rasa matsuguni, inda suka nemi mafaka a makarantar Zumba Central Primary School da wasu wurare a Karamar Hukumar Shiroro.
An gano gawarwaki 61 bayan harin ta'addanci a jihar Neja ta Nijeriya
Mazauna yankin sun soki gwamnati kan gaza ɗaukar mataki bayan samun bayanan sirri da zai iya hana faruwar harin.

An gano aƙalla gawarwakin mutane 61 ciki har da na jami’an tsaro da na farar-hula da aka kashe a wani harin ‘yan fashin daji da ya faru ranar Talata a garin Bagna da Erena a ƙaramar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja a Nijeriya.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa mazauna yankin ne suka kwaso gawarwakin daga dazukan da ke zagaye da su, kwanaki bayan afkuwar mummunan lamarin da ya haɗa da satar mutane.

Sai dai zuwa yanzu gawarwakin farar-hula kawai aka binne a Erena, yayin da aka ajiye na jami’an tsaro a mutuwaren Babban Asibin Gwamnati da ke Minna.

Masu AlakaTRT Afrika - An gano wani bam da bai fashe ba a Jihar Neja

A cewar jaridar, wani mazaunin yankin na Erena ya shaida cewa waɗanda abin ya rutsa da su sun haɗa da ‘yan bijilante, da jami’an tsaro na ƙasa, da kuma farar-hula.

Sai dai hukumomin ‘yansanda sun tabbatar da kisan ‘yansintiri guda uku ne kacal, kamar yadda jaridar ta ambato.

Duk da cewa mazauna garin sun yaba wa yunƙurin jami’an tsaro da suka kawo ɗauki bayan zuwan maharan har suka kore su, sun kuma soki gwamnati kan gaza ɗaukar mataki bayan samun bayanan sirri da zai iya hana faruwar harin.

Harin dai ya janyo rasa matsuguni inda ɗaruruwan mazauna yankin suka nemi mafaka a makarantar Zumba Central Primary School da wasu wurare a Shiroro LGA.

Rumbun Labarai
'Yanta'addan Lakurawa sun kashe jami'an hukumar kwastam biyu a Jihar Kebbi ta Nijeriya
Rundunar sojin Nijeriya ta ce babu shaida ta kashe fararen-hula a harin sama a kasuwa a Zamfara
Nijeriya na tattaunawa da Bankin Duniya kan sabon bashin $1.25bn: rahoto
Shugaba Tinubu na Nijeriya na halartar taron Afirka da Faransa a Kenya
Rundunar Sojin Nijeriya ta musanta kashe fararen-hula a harin sama a jihar Neja
Nijeriya da Amurka sun ƙarfafa haɗin gwiwa kan tsaro da yaƙi da ta’addanci bayan ganawa a Washington
Sojin Nijeriya sun halaka ‘yanta’adda 50, sun yi asarar dakaru biyu yayin daƙile harin ISWAP a Yobe
'Yanbindiga a Nijeriya sun kashe mata masu juna biyu uku da wasu mutum 11 a Filato
Dakarun sojin Nijeriya sun kashe 'yanta'addan ISWAP da masu garkuwa da mutane
Sojojin Nijeriya sun ceto yaran da aka sace daga gidan marayu
Sanƙarau ta kashe mutum 33 a Sokoto yayin da hukumomi ke ƙoƙarin daƙile yaɗuwarta
Dangote ya sanar da shirinsa na samar da megawat 20,000  na wutar lantarki a Nijeriya
Nijeriya da Amurka sun ƙaddamar da cibiyoyin aikin tsaro don magance matsalar rashin tsaro
Dakarun Nijeriya sun kashe 'yanta'adda a Jihar Zamfara
Nijeriya na nuna kayan tsaro da ta ƙera a taron baje-kolin SAHA 2026 da ke gudana a Istanbul
Kwamitin wucin-gadi na Majalisar Dokokin Nijeriya zai je Afirka ta Kudu kan batun ƙyamar baƙi
Jam'iyyar NDC ta miƙa takarar shugaban ƙasa ga kudancin Nijeriya, in ji Buba Galadima
Nijeriya za ta fara kwaso 'yan ƙasar daga Afirka ta Kudu saboda rikicin ƙyamar baƙi
Peter Obi ya bayyana shirin ficewa daga jam'iyyar ADC
Ba mu yanke shawara kan makomarmu ta siyasa ba – Kwankwaso