Gwmnatin Tarrayar Nijeriya ta ce tufka da warwarar da jagoran ‘yan adawa kuma ɗantakaran jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ke yi kan batun mayar da tallafin mai na nuna cewa siyasa kawai ne yake son yi da batun mayar da tallafin.
A wata sanarwar da ya fitar ranar Laraba babban mai bai wa Shugaban Tinubu Shawara kan Watsa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya ce sauya maganar da Atiku ya yi sau uku cikin mako ɗaya ya nuna cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasar siyasa kawai yake yi da batun dawo da tallafin mai.
“Cikin mako ɗaya, ‘yan Nijeriya sun ji bayanai daban daban iri uku game da abin da gwamnatin Atiku za ta yi game da batun tallafin mai. Ruɗanin yanzu ya zama abin da ba za a iya watsi da shi ba,” in ji Onanuga.
Sanarwar ta ce daga farko mai magana da yawun Atiku, Paul Ibe, ya ce Atiku zai mayar da tallafi idan aka zaɓe shi kuma zai janye tallafin a hankali. Ibe ya bayyana matakin a matsayin wani matakin wucen gadi mai zummar bai wa ‘yan Nijeriya da kamfanonin damar farfaɗowa, in ji shi.
Ya ƙara da cewa daga baya wani bayani ya sake zuwa daga wani babban hadiminsa, Phrank Shaibu, wanda ya ce sanarwar Ibe wata sanarwa ce da ba a ba da izinin yinsa ba kuma wanda ke rudar da mutane game da matsayar Atiku.
“Shaibu ya ce Atiku ba zai fitar da ranar da za a kawo ƙarshen tallafin mai ba. Maimakon hakan, zai cigaba har zuwa lokacin da ƙarfin tace man cikin gida ya faɗaɗa, kuma samar da mai ya ɗore kuma gogayya ya yi zurfi kuma kasuwa za ta iya ba da farashi mai rahusa ba tare da tallafin gwamnati ba,” in ji sanarwar.
“Amma cikin sa’o’i, Atiku da kansa ya saka baki kuma ya soke wannan ƙarin hasken. Ya nanata cewa matsayarsa “ba ta canza ba” kuma shi zai mayar da abin da ya kira wani ‘tallafi da zai mayar da hankali wani wuri’ idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa. Ya kuma ce, “Za ni mayar da tallafi da ya mayar da hankali kan wani wuri na kuma mayar da ikon iya sayayya hannayen ‘yan Nijeriya ‘“, in ji sanarwar.
Fadar gwmanatin ƙasar ta ce wannan ba kawai sauya ma’anonin kalamai ba ne, amma karo da kai na manufofi mai hatsarin gaske.
“Idan matsayar Atiku ba ta sauya ba, me ya sa ɗaya daga cikin manyan hadimansa ya ce tallafin zai kasance na wucen gadi ne kuma za a janye shi a hankali? Me ya sa ya zama wajibi ga wani babban hadiminsa ya yi wasti da wannan bayanin a bainar jama’a ya kuma fito da wani tsari na daban bisa yanayin kasuwa? Kuma me ya sa sannan Atiku ya shigo domin sake tabbatar da matsayarsa ta asali?,” in ji sanarwa.
Ta ƙara da cewa ‘yan Nijeriya suna buƙatar bayani da ke a fili, ba manufa ta gwaji da kuskure ba.
Kazalika Onunaga ya bayyana cewa da alama bayanin Atiku bai gane yanayin kasuwar man fetur ba.
“Fetur ba ya araha kawai saboda gwamnati ta ba da umarnin tallafi ko kuma domin ana tsamanin gogayya ta bayyana. Wasu dalilai, ciki har da farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya da kasuwar musayar kuɗi da farashin tace mai da na dakon mai da rarabawa da sauran kuɗaɗe na kasuwa suna tasiri kan farashin man fetur a gidajen mai,” a cewar Onanuga.
Ya ce gogayya ka iya inganta yanayin aiki da riba, amma ba zai iya kare Nijeriya daga farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya ko kuma kuma daga farashin kayayyakin aiki ba.
Kazalika sanarwar ta zargi Atiku da zaƙewa wajen mayar da lamarin wani abu mai sauƙi fiye da kima.
“Da gaske, farashin makamashi da na sufuri na tasiri kan farashin abinci. Amma farashin man fetur kaɗai bai taɓa haddasa hauhawar farashin abinci ba. ‘Yan Nijeriya suna fama da tashin farashin har cikin shekarun da aka yi da tallafin man fetur,” in ji sanarwar.
Ya ce ingancin harkar noma da rashin tsaro da yanayin kasuwar musayar kuɗaɗe da jigilar abinci da ajiya da ambaliya da tsadar kayayyakin abinci da samuwar kuɗaɗe da matsalolin samar da abinci na da muhimmaci wajen farashin abinci.
Onanuga ya ƙara da cewa dole wani tsarin tattalin arziki mai ma’ana ya magance waɗannan dalilan kamar yadda Shugaba Tinubu yake yi tun shekaru uku da suka gabata, maimakon mayar da matsalar tsadar rayuwa matsalar farashin man fetur kawai.
“Saboda haka muna kira ga Atiku ya daina sauya matayarsa ya kuma bayyana abin da yake nufi da “tallafi da ya mayar da hankali kan wani wuri”: nawa za a kashe kansa, wa zai ci moriyarsa, ta yaya za a gane waɗanda za su ci moriyarsa, ta yaya za a samu kuɗin tafiyar da shi, kuma wani yanayi na tattalin arziki ne zai yanke hukunci kan kawo ƙarshensa daga baya?,” in ji shi.
Ya ce ‘yan Nijeriya ba za su iya ɗaukar nauyin wani tsarin tallafi mai tsada da aka ƙawata da sabbin kalamai ba
Ya ƙara da cewa tattalin arziki abu ne da muhimmacinsa ya yi ƙarfin tufka da warwara da rashin daidaito da tunzura jama’a da dabarun yaudara da jan hankali na zaɓe.
Sanarwa ta tambayi Atikun da ya ce ce tallafinsa zai bi gangar ɗanyen mai cewa shin ya san kashi 45 cikin 100 na gangar ɗanyen mai ne kawai ke ɗauke da man fetur, tana mai cewa ko wane gangar ɗanyen mai na samar da wasu ire-iren mai waɗanda aka riga a cire musu tallafi tun shekaru da yawa da suka gabata.
“Man gas, wadda gwamnatin Obasanjo da Atiku ta cire wa tallafi a shekarar 2004, shi ne kimanin kashi 25 cikin 100 na gangar mai ɗaya. man jirgin sama da kananzir su ne kimanin kashi 9 cikin 100 na gangar ɗanyen mai. A shekarar 2009 ne gwamnati ta tsame hannayenta daga kananzir da man jiragen sama kuma ta cire musu tallafi a shekarar 2016,” in ji sanarwar.
Kazalika sanarwar ta ce kimanin kashi 10 zuwa kashi 15 cikin 100 na gangar ɗanyen mai na samar da ababen haɗa roba da sauransu da ake amfani da wasu wajen haɗa buroshi da kofi da kuma ƙulle kayayyaki.
“Ƙwalta ne kashi 2 zuwa kashi 4 ciiin 100 na gangar ɗanyen mai,” in ji Onanuga. wanda ya ƙarƙare sanarwarsa da cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasar kansa bai gane sabuwar manufarsa.





















