Rundunar RSF ta amsa aikata 'take haƙƙi' a Al Fasher na Sudan
Shugaban rundunar RSF, Dagalo, ya ce an kafa kwamitoci domin bincike kan aika-aikar da dakarunsu suka yi ta aikata a Al Fasher.
Rundunar RSF ta Sudan ta amsa cewa dakarunta sun aikata ;aifukan “take haƙƙoƙin” bil’adama a Al Fasher, babban birnin Jihar North Darfur, tana mai iƙirarin cewa an kafa tare da ƙaddamar da kwamitocin bincike game da batun.
"Na ga abubuwan wuce-gona-da-iri a Al Fasher, kuma a yanzu ina sanar da kafa kwamitocin bincike. Waɗannan kwamitocin sun riga sun isa Al Fasher," in ji kwamandan RSF, Mohamed Hamdan Dagalo a cikin wani bidiyon da aka naɗa kuma aka wallafa a manhajar Telegram ranar Laraba.
Hukumomin Sudan da kuma ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa sun zargi RSF da aikata "kisan kiyashi da kuma cin zarafin ‘yan’adam " a Al Fasher, ciki har da "kisan gilla," da kama mutane babu dalili da kuma raba fararen-hula da muhallansu a lokacin da ta kai hari a birnin ranar Lahadi, bayan ta yi wa birnin ƙawanya fiye da shekara ɗaya.
Shugaban Majalisar Gwamnatin Riƙon ƙwarya ta Sudan Abdel Fattah al Burhan ya tabbatar da cewa rundunar sojin ƙasar ta janye daga birnin domin kare ta daga ƙarin "ta’adi da kisa" na RSF.
Hukumar jinƙai ta Sudan ta bayyana ranar Laraba cewa rundunar RSF ta kashe fiye da mutum 2,000 a lokacin da ta kai hari birnin. Ƙungiyar likitocin Sudan ita ma ta zargi RSF da kashe dukkan majinyata da ke asibitocin Al Fasher.
Iƙirarin bincike
A cikin bidiyon nasa, Dagalo ya yi iƙirarin cewa "kwamitocin bincike na shari’a za su bincika tare da hukunta duk wani soja ko hafsa da ya tauye haƙƙin ɗan’adam nan-take kuma za a bayyana sakamakon binciken nan-take."
Ya kuma yi iƙirarin cewa za a bai wa fararen-hula damar kaiwa da komowa cikin birnin kuma za a saki fararen-hular da aka kama nan-take.
Dagalo ya yi kira ga mazauna wurin su koma Al Fasher duk da "ƙalubale na yanzu daga mahaƙar ma’adinai da kuma na take haƙƙoƙi na yaƙi."
"’Yan ƙasa za su iya komawa gidajensu, musamman waɗanda suke da gidaje a cikin Al Fasher," in ji shi.
"Mun yi nadamar bala’in da ya same ku, amma ba mu da zaɓi; an ƙaƙaba mana yaƙin ne. Shawarar da aka yake ita ce dukkan sojoji su kasance a bayan garin Al Fasher bayan an tsare birnin kuma an kawar da ƙalubalen," a cewar Dagalo.
Gwamnatin Sudan ba ta ce komai ba kawo yanzu game da kalamansa waɗanda suka biyo bayan kakkausar suka daga ƙungiyoyi Larabawa da Musulmai da na ƙasa da ƙasa game da take haƙƙoƙin da RSF ta aikata a Al Fasher.
Raba mutane da yawa da muhallinsu
Ranar Laraba ɗakunan ba da agajin gaggawa da fararen-hula ke jagoranta a yankin Tawila da ke North Darfur sun yi kira ga tallafi na ceton rayukan waɗanda aka raba da muhallansu da ke isowa daga Al Fasher cikin tsananin mawuyacin yanayi.
"Muna kira na gaggawa ga ƙungiyoyi na ƙasa da ƙasa da na yanki da ƙasa da kuma ƙungiyoyin ba da agaji su bayar da agaji na gaggawa ga ɗakunan agajin gaggawa na Tawila domin ceto rayuka da kuma rage wahalarsu," in ji su a wata sanarwa.
"Tawila na samun ƙarin shigowa na mutanen da aka raba da muhallansu da suke ci-gaba da isowa daga Al Fasher. Sabbin isowan suna fuskantar yanayi mai tsananin wuya ciki har da ƙarancin ruwa da abinci mai tsanani da kuma rashin abinci mai gina jiki da kuma yanayin lafiya mai tsanani na mara lafiya da waɗanda suka ji rauni," kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Rundunar RSF ta ci gaba da musanta zarge-zargen, tana mai iƙirarin cewa tana "share duk wani sauran [dakarun adawa] a Al Fasher ."
Hukumar hijira ta MDD ta ba da rahoto ranar talata cewa mutum 7,455 sun tsere daga Al Fasher cikin yini ɗaya saboda hare-haren RSF, lamarin da ya kawo adadin mutane da aka raba da muhallinsu cikin sama da kwanaki uku zuwa 33,485.
Tun ranar 15 ga watan Afrilun shekarar 2023, ne sojin ƙasar da dakarun RSF suka fara gwabza yaƙi, wanda sa bakin masu shiga tsakani na ƙasa da ƙasa da na yanki ya gaza kawo ƙarshensa. Rikicin ya kashe dubban mutane tare da raba fiye da mutum miliyan 15 da gidajensu.