Gwamnatin ƙasar Mali ta haramta amfani da wasu irin babura a wajen manyan birane a ƙasar, matakin ya zo ne yayin da kasar ke fafatawa da kungiyoyin 'yan ta'adda, kamar yadda kafar yada labarai na gwamnatin ƙasar ta bayyana a ranar Laraba.
Kungiyoyin ‘yanta’adda sun fi yawan amfani da babura wajen kai hare-hare a Mali.
Umarnin dokar wadda aka karanto ta gidan talabjin din gwamnatin ƙasar a yammacin Laraba ta ce ‘‘ an dakatar da zirga-zirga da babura masu karfin injin 125cc ko fiye da haka, a wajen manyan biranen ƙasar nan.’’
Ko ya dake dokar ba ta shafi babban birnin Bamako, manyan biranen yankin da wasu yankunan birane.
Dakatar da shigo da kayayyaki
Kazalika hukumomin ƙasar sun sanar da dakatar da "shigo da kayayyaki, da zirga-zirga jama’a, tallace-tallace,da kuma rabon kyautar babura" a dukkan faɗin kasar.
Mali na fustantar tarin matsaloli na tsaro bayan hare-haren da 'yanta'adda da 'yan awaren Tuareg ke jagoranta suka kai ƙasar a ranakun 25 da 26 ga watan Afrilu inda suka kashe ministan tsaron ƙasar Sadio Camara a gidansa.
'Yanta'addan sun toshe hanyoyi da dama da ake shiga Bamako tun daga ranar 30 ga Afrilu, inda suka kona motoci da dama da kuma manyan motocin daukar kaya.
Kungiyoyi masu dauke da makamai sun kwace yankuna da dama a arewacin ƙasar, ciki har da garin Kidal mai matukar muhimmanci.









![Masar ta yi kira ga kwamitin tsaro na MƊD ta dakatar da faɗaɗa [harin] da Isra'ila ke yi a Lebanon](https://d2udx5iz3h7s4h.cloudfront.net/2026/4/25/67480fcc1bc16e3971fbb70d/image/35fa6aac64e41c9240c09651b2ba0fb1be4eb5b1e1ca009d1c3d191c8f65622b.webp?width=512&format=webp&quality=80)





