| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Ghana ta ƙwato fiye da cedi biliyan 18 ta hanyar binciken kuɗi – Babbar mai binciken kuɗi
Dr Graham ta ce hukumar ta kuma taimaka wajen ceto wa ƙasar cedi biliya 11.7 a cikin shekarar 2025 kaɗai ta hanyar ganowa da kuma hana biyan kuɗaɗe ba bisa ƙa’ida ba.
Ghana ta ƙwato fiye da cedi biliyan 18 ta hanyar binciken kuɗi – Babbar mai binciken kuɗi
Tsohon Hoto: Shugaban Ghana John Mahama

Babbar mai binciken kuɗi ta Ghana, Dr Pamela Graham, ta ce hukumar binciken kuɗi ta ƙasar ta yi nasarar ƙwato fiye da cedi biliyan 18 na kuɗaɗen ƙasa tsakanin shekarar 2022 zuwa 2026 ta hanyar ayyukan binciken kuɗinta.

Ta ce hukumar ta kuma taimaka wajen ceto wa ƙasar cedi biliyan 11.7 a cikin shekarar 2025 kaɗai ta hanyar ganowa da kuma hana biyan kuɗaɗe ba bisa ƙa’ida ba.

Yayin da take jawabi a wani taron Ƙungiyar Akawu ta Afirka, Dr Graham ta ce akwai buƙatar hukumomin gwamnati su aiwatar da matakai na gyara bisa sakamakon binciken kuɗi domin ƙarfafa fayyace gaskiya da inganta sarrafa kuɗaɗen gwamnati.

Ta bayyana cewa ya kamata rahotannin binciken kuɗi su wuce gano yin ba daidai da kuɗi ba kuma maimakon hakan a yi amfani da su a matsayin hanyar ƙarfafa matakan gudanarwa na cikin gida da kuma tsara manufofi.

“Daga shekarar 2022 zuwa yanzu, mun ƙwato fiye da cedi biliyan 18 na Ghana daga aikin Babbar Mai Binciken Kuɗi. Mun ceto wa ƙasar kimanin cedi biliyan 11.7 daga biyan kuɗi ba daidai ba a cikin shekarar 2025 kawai,” in ji ta.

“Ya kamata a kalli bayanai na kuɗi ko kuma binciken kuɗi a kayayyakin binciken laifi mai tarihi ba kawai, amma ya kamata a kalle su a matsayin masu bayar da bayanai na dabaru masu muhimmanci da za su taimaka wajen kafa matakai na gaba da kuma tsare-tsaren manufofi.”

Dr Graham ta ce bai kamata a kalli tasirin binciken kuɗi kan gano maguɗin kudi ba kawai, amma kan yadda ma’aikatu za su yi amfani da sakamakon binciken kuɗin wajen hana sake aukuwar irin maguɗin.

Ta bayyana cewa sauya sakamakon binciken zuwa gyare-gyaren manufofi zai taimaka wajen ƙarfafa gudanarwa da inganta fayyace gaskiya da kuma tabbatar da tsama wajen amfani da kuɗin gwamnati.

Saboda haka, Babbar Mai Binciken Kuɗin ta yi kira da ƙara mayar da hankali wajen aiwatar da shawarwarin binciken kuɗi, tana mai jaddada cewa bayanan da aka samo ta hanyar binciken kuɗi za su iya taka muhimmin rawa wajen inganta gudanar da ayyukan gwamnati da kuma hana asara na gaba.