Shugabannin ƙasashen Afirka a ranar Alhamis sun buƙaci ƙasashen da suka ci gaba su cika alƙawuran da suka ɗauka na bayar da tallafin kuɗi domin yaƙi da sauyin yanayi, tare da tabbatar da adalci wajen raba tallafin da mayar da alƙawuran duniya zuwa ga ayyuka na zahiri.
Sun yi gargaɗin cewa ƙasashe masu ƙaramin ƙarfi ba za su iya ɗaukar nauyin ƙarin kuɗaɗen da matsalar ke haifarwa su kaɗai ba.
Mataimakin shugaban ƙasar Cote d’Ivoire, Tiemoko Meyliet Kone, ya yi kira da a ƙarfafa haɗin kai tsakanin ƙasashen duniya da kuma sauƙaƙa hanyoyin samun tallafin kuɗi domin yaƙi da sauyin yanayi a taron COP31 da ke gudana a Antalya na Turkiyya.
Ya ce ya kamata ƙasashen Afirka su iya magance matsalar sauyin yanayi ba tare da yin watsi da burinsu na samun ci-gaba ba.

"Idan babu tabbas a yanayin damuna, amfanin gona ne ke fuskantar barazana. Hanyoyin samun kuɗin shiga suna ɓacewa, sannan makomar iyalai gaba ɗaya takan shiga cikin haɗari," in ji shi.
Seychelles
Mataimakin shugaban ƙasar Seychelles, Alix Sebastien Pillay, a ranar Alhamis ya yi kira da a ɗauki matakan gaggawa domin cika alƙawuran yaƙi da sauyin yanayi ta hanyar samar da ayyukan yi da kuɗaɗen tallafi.
Ya yi gargaɗin cewa bala’o’in sauyin yanayi na jefa ƙasashen yankin tsibirai cikin mawuyacin hali.
"Ya kamata alƙawura su koma kuɗaɗen tallafi," in ji shi, yana mai kira da a hanzarta samar da ingantaccen taimako ga ƙasashen da sauyin yanayi ya fi shafa.
Gabon
Mataimakin shugaban ƙasar Gabon, Hugues Alexandre Barro Chambrier, ya yi kira da a samar da tallafin kuɗi mai ɗorewa da adalci domin yaƙi da sauyin yanayi, yana mai cewa bai kamata ƙasashen da ke kare muhallin duniya su kaɗai su ɗauki nauyin kuɗaɗen wannan aiki ba.
A jawabinsa a taron COP31, Chambrier ya buƙaci a amince da irin gudummawar da yankin dajin Congo Basin ke bayarwa wajen daidaita yanayin zafi a duniya.
Ya kuma yi kira ga ƙasashen da suka ci gaba da su cika alkawuran tallafin da suka ɗauka ga ƙasashe masu tasowa.
Zimbabwe
Mataimakin shugaban ƙasar Zimbabwe, Constantino Guveya Dominic Nyikadzino Chiwenga, ya buƙaci ƙasashen da suka ci gaba su samar da tallafin kuɗi na yaƙi da sauyin yanayi wanda za a iya wadatarwa.
Ya kuma yi kira da a tallafa wa sauye-sauyen makamashi ta yanda za su faɗaɗa samun wutar lantarki, da ayyukan yi da kuma hanzarta bunƙasa masana'antu.
A jawabinsa a taron COP31, ya ce ya kamata alƙawarin tara aƙalla dala biliyan 300 a kowace shekara ya zama wani sahihin tsari na samar da kuɗaɗe cikin gaskiya da riƙon amana, tare da jagorancin ƙasashen da suka ci gaba.
Guinea-Bissau
Firaministan Guinea-Bissau, Ilidio Vieira Te, ya yi gargaɗin cewa sauyin yanayi na daga cikin manyan barazanar da ke fuskantar bil'adama.
Ya yi kira da a samar da isasshen tallafin kuɗi domin taimaka wa ƙasashen da suka fi rauni a wannan ɓangaren don tunkarar illolin matsalar da ke ƙara ƙamari.
Ya jaddada cewa Guinea-Bissau na cikin ƙasashen da sauyin yanayi ya fi shafa, duk da cewa gudunmawarta wajen fitar da iska mai haddasa ɗumamar duniya ba ta taka kara ta karya ba.
Rwanda
Firaministan Rwanda Justin Nsengiyumva ya buƙaci masu zuba jari da su riƙa tantance ayyukan da ake gabatarwa a ƙasashe masu tasowa bisa ingancinsu, maimakon la'akari da inda ƙasashen suke.
A jawabinsa a COP31, ya ce shirin Rwanda na uku na ƙasa kan yaƙi da sauyin yanayi na da burin rage hayakin da ke haddasa ɗumamar duniya da kashi 53 cikin 100 nan da shekarar 2035, idan aka kwatanta da hasashen da ake yi idan ba a ɗauki wasu matakai ba.
Ya ce aiwatar da shirin na buƙatar zuba jari na dala biliyan 12 da kuma gagarumin tallafi daga ƙasashen duniya.
Mali
Firaministan Mali, Abdoulaye Maiga, a ranar Alhamis ya buƙaci ƙasashen duniya da su himmatu wajen rage fitar da hayaƙi mai gurbata muhalli kana su ɗauki alhakin matsalar sauyin yanayi.
Ya yi gargaɗin cewa kwararar hamada da fari da kuma lalacewar muhalli na barazana ga ci-gaban ƙasar da hanyoyin samun abin dogaro da rayuwa na al'ummarta.
Maiga ya ce shirin bunƙasa Mali, wanda ya yi daidai da Ajandar Tarayyar Afirka ta shekarar 2063 (Agenda 2063), ya ƙunshi dawo da martabar muhalli da tabbatar da ɗorewar albarkatu, tare da mayar da hankali kan ainihin buƙatun al'ummar ƙasar.






















