Shugaba Tinubu ya amince da kafa sabuwar makarantar horar da kuratan sojoji a Abakaliki

Shugaban Sojin Ƙasa na Nijeriya Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya ce ana sa ran sabon depot ɗin da za a buɗe a Abakaliki zai fara aiki nan gaba kaɗan sannan kuma ya tallafa wa sauran wuraren horar da kuratan soji da ke Zaria da Osogbo.

By
Laftanar Janar Shaibu ya sanar da umarnin na Tinubu a yayin bikin yaye kuratan sojoji  3,439 a Depot Zaria / Nigerian army

Babban Hafsan Sojojin Ƙasa na Nijeriya Laftanar Janar Waidi Shaibu, a ranar Asabar ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da kafa sabuwar makarantar horar da kuratan sojoji ta a garin Abakaliki da ke Jihar Ebonyi, a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin Rundunar Sojin Ƙasa na faɗaɗa yawan jami’ai da kuma ƙarfafa shirye-shiryen aikin soja a faɗin ƙasar.

Laftanar Janar Shaibu ya bayyana hakan ne a yayin bikin yaye kuratan sojoji  3,439 a Depot Zaria, inda ya jaddada cewa buɗe sabuwar makarantar wata muhimmiyar dabara ce don tabbatar da ci gaba da samar da sojoji ƙwararru da aka horar sosai domin tura su aiki a sassa daban-daban na ƙasar.

Ya ce: “Amincewar kafa sabuwar makarantar da kuratan a Abakaliki na daga cikin shirinmu na ƙara yawan ma’aikatan da za a horar domin aikin ƙasa da kare ƙasa. Za ta taimaka wa sauran makarantun depots da ake da su tare da ƙara ƙarfin rundunar soji wajen tunkarar sabbin ƙalubalen tsaro,” in ji shi.

Shugaban sojin ya bayyana cewa sabuwar makarantar za ta samar da horaswa ta musamman da kuma wadda ta dace da ayyuka na musamman, tare da mayar da hankali kan iya harbi da makamai, dabarun aiki a fili, da shirye-shiryen fagen fama, da nufin samar da sojoji masu ladabi, ƙwarewa, da kuma cikakken shiri na aiki.

Laftanar Janar Shaibu ya ƙara da cewa sabon depot ɗin ya yi daidai da gyare-gyaren da Rundunar Sojin Ƙasa ke ci gaba da yi na sabunta manhajojin horaswa, inganta walwalar sabbin sojoji, da ƙarfafa ƙarfin tsarin rundunar wajen kare cikakken yankin ƙasar Nijeriya.

Shugaban sojin ya ce ana sa ran sabon depot ɗin da za a buɗe a Abakaliki zai fara aiki nan gaba kaɗan, kuma zai taka muhimmiyar rawa wajen cike giɓin da ake da shi kuma ya tallafa wa sauran wuraren horar da kuratan soji da ke Zaria da Osogbo, da sauran cibiyoyin horaswa a faɗin ƙasar.