| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
An sace yara da manya 46 a hare-haren makarantu a kudancin Nijeriya
Elisha Olukayode Ogundiya, shugaban Ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya a Jihar Oyo, ya tabbatar da cewa mutum 46 aka sace a hare-haren.
An sace yara da manya 46 a hare-haren makarantu a kudancin Nijeriya
A ‘yan shekarun nan, an sha samun manyan hare-haren sace ɗalibai da dama a makarantu daban-daban a Nijeriya. / AP

An sace yara da manya 46 a hare-haren makarantu a kudancin Nijeriya

An sace mutane 46, yawancinsu yara, a yayin wasu hare-haren da aka kai makarantu uku a kudu maso yammacin Nijeriya, kamar yadda Ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya ta bayyana.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a ranar Jumma’ar da ta gabata, inda ‘yanbindiga suka kai hari a lokaci guda kan Makarantar Nursery da Primary ta Baptist da ke Yawota da kuma wasu makarantu biyu a Esiele, suka tafi da ɗalibai da malamai.

Yaran da abin ya shafa sun kasance masu shekaru tsakanin biyu zuwa 16.

Elisha Olukayode Ogundiya, shugaban Ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya a Jihar Oyo, ya tabbatar da cewa mutum 46 aka sace a hare-haren.

‘Yan sanda sun ce daga cikin waɗanda aka sace har da malamai bakwai, yayin da aka kashe mutum ɗaya a harin.

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi Allah-wadai da harin, inda ya bayyana shi a matsayin “mummunan aiki na ta’addanci,” tare da tabbatar da cewa gwamnati na aiki tare da gwamnatin jihar Oyo domin ganin an kuɓutar da dukkan waɗanda aka sace.

Ya ce ana fatan samun nasara nan ba da jimawa ba.

Ba a bayyana ko wace ƙungiya ta ɗauki alhakin harin ba. Sai dai gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya ce ana zargin maharan ‘yanbindiga ne da ke ƙaura zuwa kudanci sakamakon matsin lamba daga farmakin sojoji a arewacin ƙasar.

A Jihar Oyo, irin wannan sace-sacen makarantu ba su da yawa, duk da cewa yankin na daga cikin manyan cibiyoyin ilimi a ƙasar. Sai dai a baya an samu wasu hare-hare, ciki har da na masu gadin daji a watan Janairu.

Wannan sabon harin ya ƙara yawan mutanen da suka ɓace a hare-haren makarantu zuwa kusan 90 a faɗin ƙasar cikin makon da ya gabata.

Sace mutane domin neman kuɗin fansa ya zama ruwan dare a sassan ƙasar, musamman a yankunan karkara da ke da ƙarancin tsaro.

A ‘yan shekarun nan, an sha samun manyan hare-haren sace ɗalibai da dama a makarantu daban-daban a Nijeriya.