Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi gargaɗin cewa rikicin Iran da ke ƙamari ya kai tashin hankalin yankin zuwa wani “mataki mai ban tsoro,” lamarin da ke ƙara fargaba cewa rikicin zai bazu a faɗin Gabas ta Tsakiya.
“Da hare-haren sama kan maƙwabciyarmu Iran, tashin hankali na yanki ya kai wani mataki na ban tsoro,” kamar yadda Erdogan ya bayyana ranar Alhamis a wani taro a babban birnin ƙasar Ankara.
Ya kuma yi ishara ga hare-haren makamai masu linzami da jirage mara matuƙa na Iran kan sauran ƙasashe a yankin, yana mai cewa sun ƙara damuwar cewa rikicin zai iya ƙara faɗaɗa.
“Makamai masu linzami da jirage mara matuƙa masu halaka kansu da Iran ta ke turawa sauran ƙasashe a yankin na ƙara tsoron cewa rikicin zai iya yaɗuwa zuwa yankin da ya fi hakan faɗi,” in ji shi.
Turkiyya ta ƙarafafa tsaro, tana neman a bi diflomasiyya
Erdogan ya ce Turkiyya na ɗaukar matakai domin kare kan iyakokinta da sararin samaniyarta yayin da take ci gaba da ɗaukar matakan diflomasiyya domin hana ƙarin taɓarɓarewar lamura.
Turkiyya ba ta nuna “rashin kula ko shakka wajen tabbatar da tsaron kan iyakokinmu da sararin samaniya,” a cewarsa, yana mai jaddada cewa matsayar ƙasar tun da aka fara rikicin shi ne mayar da hankali kan zaman lafiyar yanki.

“Za mu ci gaba da diflomasiyarmu mai hanyoyi daban daban da zummar hana ƙarin zub da jini a yankinmu da kuma tabbatar da cewa babu ƙarin mutane da ba su ji ba basu gani ba da aka ɗauke rayukansu,” kamar yadda Erdogan ya bayyana.
Shugaban ya kuma yi ishara ga lamarin da ya faru a makon nan inda shirin tsaron NATO ya kakkaɓo wani makamin da aka harba daga Iran zuwa ta sararin samaniyar Turkiyya.
Erdogan ya ce Ankara ta fitar da “gargaɗin da ya kamata” biyo bayan lamarin domin hana aukuwar irin wannan lamarin nan gaba.
“Idan barazana ga tsaron ƙasarmu ta taso, za mu ɗauki dukkan matakan da suka kamata da cikakkiyar kula tare da ƙawayenmu,” in ji shi.
Rikicin yanki na daɗa zafafa
Tashe-tashen hankula a Gabas Ta Tsakiya sun ƙaru tun lokacin da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar da hare-haren sama kan Iran daga ranar 28 na Fabrariru, waɗanɗa suka kai kan wuraren soji da muhimman wurare a ƙasar.
Rahotanni sun ce hare-haren sun kashe fiye da mutum 900, ciki har da jagoran addinin Iran Ali Khamenei.
Tehran ta mayar da martani da hare-haren makamai masu linzami da na jirage marasa matuƙa kan ƙasashen Larabawa masu karɓar baƙuncin sansanonin sojin Amurka, lamarin da ke ƙara damuwa game da katse zaman lafiyar yankin da kuma hanyoyin jigilar makamashi na duniya.

















