Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka (CAF) ta sanar a ranar Asabar cewa za a gudanar da gasar Cin Kofin Afirka ta 2027 daga 19 ga Yuni zuwa 17 ga Yuli, ba tare da bayyana ƙasar da za ta karɓi baƙuncin wasan buɗe gasar ko kuma wasan ƙarshe ba tsakanin Uganda ko Kenya ko Tanzania.
Ranakun sun samu amincewar Kwamitin FIFA a Vancouver, Canada, bayan an rage damuwar cewa ƙasashen ba za su kammala shiri ba; yayin da shugaban CAF, Patrice Motsepe, ya yi nasarar daƙile yunƙurin ɗage gasar zuwa 2028.
"Mun yi aiki tukuru don tabbatar da cewa za a gudanar AFCON a Gabashin Afirka, kuma alƙawarimmu bai sauya ba. Ina da tabbacin cewa za mu shirya AFCON cikin nasara a waɗannan ƙasashe uku," in ji Motsepe.
Wannan gasar ta AFCON, wacce ita ce ta farko da za a gudanar a ƙasashe uku, za ta nuna komawar gasar zuwa Gabashin Afirka tun daga wacce aka buga a 1976 a Habasha (Ethiopia).









