| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
EFCC ta janye ƙarar da ta shigar da Maryam Shehu da Abubakar Shuraim kan zargin ɓata suna
Sakin nasu ya zo ne a daidai lokacin da lauyoyin Maryam suka shigar da buƙatar bayar da belinta don samun damar rubuta jarrabawar shekarar karshe a jami’a, kamar yadda ɗaya daga cikin lauyoyin Abba Hikima ya bayyana a shafinsa na Facebook.
EFCC ta janye ƙarar da ta shigar da Maryam Shehu da Abubakar Shuraim kan zargin ɓata suna
Maryam ɗaliba ce ta shekarar ƙarshe a jami'ar Bayero ta Kano / FB: Abba Hikima

Shugaban Hukumar Yaƙi da Yi wa Tattalin Arzikin Nijeriya Zagon Ƙasa (EFCC), Olanipekun Olukoyede ya ba da umarnin janye ƙarar da hukumar ta shigar da wasu matasa biyu, Maryam Shehu da Abubakar Shuraim Abdulhamad, kan ɓata wa EFCC suna, kamar yadda sanarwar hukumar ta bayyana.

Shugaban na EFCC ya ce ya yi hakan ne don tausayawa matasan, waɗanda aka gurfanar a gaban Babbar Kotun Tarayya a Abuja, ranar 20 ga Agustan 2026.

An zarge su ne da aikata laifuka a intanet, da yaɗa bayanan ɓata-suna ga hukumar ta EFCC, lamarin da ya janyo suka daga wasu ‘yan Nijeriya, da kuma neman afuwa daga mahaifin Maryam Shehu.

Sakin nasu ya zo ne a daidai lokacin da lauyoyin Maryam suka shigar da buƙatar bayar da belinta don samun damar rubuta jarrabawar shekarar karshe a jami’a, kamar yadda ɗaya daga cikin lauyoyin Abba Hikima ya bayyana a shafinsa na Facebook.

Maryam dai tana shekarar ƙarshe ne a Jami’ar Bayero da ke Kano.

A ranar Talata ne lauyan ya wallafa wata buɗaɗɗiyar wasiƙa ga ministan shari’a na Nijeriya yana kira a gare shi ya sa baki don ganin EFCC ta saki Maryam ko kuma ta gurfanar da ita a kotu.

Abba Hikima ya yi zargin cewa EFCC ta tsare Maryam fiye da kwanaki 30 ba tare da gabatar da ita a kotu ba, abin da ya ce ya saɓa wa dokokin ƙasar.

A ranar Laraba ne kuma EFCC ta gurfanar da Maryam da Shuraim a kotu kan zargin ɓata suna.

Batun dai ya janyo ce-ce-ku-ce a kafofin sada zumunta, inda lauyoyi da masu fafutuka irin su Omowele Sowere suka shiga fafutuka da kiraye-kirayen a sake su.  

Sowere, wanda ya halarci zaman kotun a ranar Alhamis lokacin da aka gurfanar da su Maryam, ya ce suna fatan kotun za ta zauna a yau Juma’a ko da ɗan taƙaitaccen zama ne, don a samu damar sakin Maryam, ta yadda za ta samu damar rubuta jarrabawar da za a fara ranar Asabar.

 

Rumbun Labarai
Tinubu ya ceci Nijeriya daga wargajewa, in ji Kashim Shettima
Yawan iskar gas ɗin da Nijeriya ke samarwa a cikin gida ya ɗara ƙafa biliyan 2
Mutfwang ya gana da Tinubu, ya ce an fara gurfanar da masu kai hare-hare a Filato
'Yansandan Nijeriya sun ceto mutane 10 daga cikin 'yan NYSC da aka yi garkuwa da su a jihar Imo
Nijeriya: Mutane uku sun mutu a turmutsitsin rabon tallafin kuɗi a Jihar Neja
Ranar 'Yancin Kai a Nijeriya: Sauye-sauyen da muke yi za su haifar da sakamako mai kyau - Tinubu
Dubban fasinjojin Kano da suka bi Saudi Airline sun koka cewa kayansu sun maƙale a Saudiyya
Rundunar Sojin Nijeriya ta ƙaddamar da motocin yaƙi masu sulke da bataliyar soji uku a jihar Kebbi
'Yansandan Nijeriya sun gano ƙoƙon kawuna 28 a wani daji a Jihar Abia
Kotun Nijeriya ta umarci NMDPRA ta bai wa A.A Rano, AYM Shafa da Matrix lasisin shigo da fetur
An sace fiye da mutum 80 a cikin mako biyu a arewacin Nijeriya
‘Yan Nijeriya fiye da 67,000 sun amfana da shirin ba da lamuni ga ƙananan masana'antu – Tinubu
Tinubu yana nan lafiya, zai koma Nijeriya a makon nan: Fadar Shugaban ƙasa
Kwalara ta kashe wasu fursunoni a gidan gyaran hali na Kurmawa da ke Kano
Sojojin Nijeriya sun kama mutum uku da ake zargi da yi wa ‘yanta’adda aikin masinja a Katsina
An sake harbe wani ɗan Nijeriya har lahira a Afirka ta Kudu
Nijeriya ta buƙaci a bai wa Afirka kujeru biyu na dindindin a Kwamitin Tsaro na MƊD
Nijeriya da Amurka sun ƙulla yarjejeniyar biliyan $700 a ɓangaren haƙar ma'adinai
Ƙungiyar Amnesty International ta soki gwamnatin jihar Kano a Nijeriya kan musguna wa ‘yan adawa
Ba na da-na-sanin taimaka wa waɗanda suka yi watsi da ni a yanzu— El-Rufai