Farashin mai ya yi tashin gwauron zabi, hannayen jari sun yi warwas saboda yaƙin Gabas ta Tsakiya
Ana fargabar idan aka ci gaba da yaƙi tsakanin Amurka-Isra'ila da Iran, ci gaba da tashi da ɗanyen mai yake yi zai iya jawo hauhawar farashin kayayyaki a ƙasashen duniya da kuma hana babban banki na ƙasashe damar rage kuɗin ruwa.
Farashin ɗanyen mai ya tashi sosai a ranar Juma'a saboda fargabar ƙaruwar tangarɗa ta jingiliar man da ake samu sakamakon yakin Gabas ta Tsakiya, yayin da hannayen jari suka faɗi.
Yakin Amurka da Isra'ila a kan Iran da martanin Tehran na ramuwar gayya a faɗin yankin Gulf na girgiza bangarorin makamashi da sufuri na duniya, lamarin da ya kai ga jawo rufe Mashigar Hormuz.
Farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya ya tashi zuwa dalar Amurka 92.69 a kowace ganga, inda farashin ya ƙaru da kashi 8.5 cikin 100 a rana ɗaya da kuma kusan 30 cikin 100 a mako guda, bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya ce sai Iran ta “miƙa wuya” ne zai kawo ƙarshen yakin.
Farashin ɗanyen man nan mai inganci na West Texas Intermediate (WTI), ya tashi sama da kashi 12 cikin 100 zuwa fiye da dalar Amurka 90 a kowace gangal, wanda ya zama mafi girman hauhawar mako-mako a tarihi.
Zirga-zirgar teku kusan ta tsaya cik a Mashigar Hormuz, ta hanyar da kashi daya cikin biyar na danyen mai da iskar gas da na duniya ke bi.
Da farko ‘yan kasuwa sun yi zaton wannan yaƙin zai kasance gajere ne, amma bukatar Trump na ganin Iran ta mika wuya ya ƙara sa ana hashen ƙarin tsawonsa.
"Maganganun Trump sun kawar da fatan cewa za a magance rikicin da sauri, kuma farashin mai ya ci gaba da tashi," in ji Kathleen Brooks, daraktar bincike a XTB.