Matatar Dangote ta ƙara man da take turawa ƙasashen Afirka yayin da yaƙin Iran ya katse jigilar mai

Matatar man Dangote ta Nijeriya ta ƙara yawan man da take fitarwa zuwa ƙasashen Afirka da ke fama da ƙarancin makamashi sakamakon yaƙin Iran, in ji Aliko Dangote ranar Litinin.

By
Attajirin Nijeriya Aliko Dangote ya ce matatarsa ta ƙara yawan man da take turawa ƙasashen Afirka yayin rikicin Gabas Ta Tsakiya / Reuters

Matatar man Dangote ta ƙara yawan mai da take fitarwa zuwa ƙasashen Afirka da ke fama da ƙarancin makamashi sakamakon yaƙin Iran, in ji Aliko Dangote ranar Litinin.

Dangote ya ce matatar, wadda ke tace gangar ɗanyen mai 650,000 a ko wace rana, ta taimaka wajen rage raɗaɗin tasirin da yaƙin Iran ke yi a Nijeriya da ma faɗin nahiyar.

"Abin da zan iya yi shi ne na tabbatar wa ‘yan Nijeriya... da ma yawancin ‘yan yammacin Afirka, da tsakiyar Afirka da kuma gabashin Afirka cewa, muna iya biyan buƙatarsu ta fannin mai," a cewar Dangote yayin da yake rangadi a matatar da ke Legas.

Ya ce matatar ta fitar da tankokin jiragen ruwa cike da man fetur har 17 zuwa wasu ƙasashen Afirka kuma yawan man da take fitarwa ya ƙaru a baya bayan nan.

Matatar da ƙara yawan ababen da take turawa ƙasashen Afirka

"A cikin ‘yan kwanakin nan, mun mayar da hankali kan ƙasashen Afirka, abin da ba ma yi a baya," in ji shi , inda yake magana game da fitar da taki, ba tare da ba da adadi ba.

Matatar na iya samar da tan miliyan 3 na urea a shekara, wanda yawancinsa ana fitarwa ne zuwa Amurka da kudancin nahiyar Amurka, in ji jami’ai.

Dangote ya ce matatar na fatan samun ƙarin jiragen ruwa cike da ɗanyen mai da za a sayar mata da kuɗin naira na Nijeriya domin rage farashin tataccen mai.

Majiyoyin cinikayya biyu da kuma wani jami’in matatar sun shaida wa kamfanin dillancin labaran Reuters a makon jiya cewa kamfanin man ƙasar NNPC zai ƙara yawan ɗanyen man da yake bai wa matatar man Dangote zuwa jiragen ruwa bakwai a watan Mayu, maimakon jiragen ruwa biyar da ta samu a watannin baya.