Toni Kroos ya soki gasar ƙwallo ta Saudiyya game da raina tasirin Ronaldo

Tuni aka fara raɗe-raɗin ƙungiyoyin da Ronaldo zai iya komawa, saboda rashin jin daɗinsa da irin goyon bayan da hukumomin Saudiyya ke bai wa ƙungiyarsa.

By
Tun a 2023 ne Cristiano Ronaldo ya koma taka leda a Saudiyya. / Reuters

Tsohon ɗanwasan Real Madrid wanda ya yi wasa da Cristiano Ronaldo tsawon shekaru, ya nemi a girmamam matsayin gwarzon ɗanwasan saboda gudunmawar da ya bai wa tamola.

Da yake magana kan taƙaddamar da ke tsakanin Ronaldo da hukumar da ke kula da babbar gasar ƙwallo ta Saudiyya, Kroos ya soki gasar yana mai nuna muhimmancin Ronaldo.

Kroos, wanda ɗan asalin Jamus ne, yana cewa zuwan Ronaldo ƙungiyar Al-Nassr ta Saudiyya shi ne abin da ya kawo babban sauyi a tagomashin gasar a fagen ƙwallo na duniya.

“Gasar Saudi Pro League ta zama wata iri. Ba wanda ya san da ita kafin Cristiano Ronaldo ya je can, amma yanzu suna raina tasirin mutumin da ya fito da su duniya. Ba domin Ronaldo ba, gasar Saudiyya da ta rasa farinjinta”, in ji Kroos.

Dalilin da ya sa Kroos ke kare tsohon abokin wasan nasa shi ne cewa, kada a raina tallafin da Ronaldo ya bai wa gasar ta Saudiyya.

Taƙaddama da Ronaldo

A farkon watan nan ne rahotanni suka nuna cewa an fara yin tababa kan ci gaba da kasancewar Cristiano Ronaldo a ƙungiyar Al-Nassr, da ma gasar ta Saudiyya ɗungurungun.

Duk da cewa Cristiano Ronaldo yana da kwantiragi da za ta kai har 2027, rahotanni na nuna cewa zai iya barin Saudiyya a bazara mai zuwa saboda Karim Benzema ya koma Al-Hilal daga Al-Ittihad.

Tuni aka fara raɗe-raɗin ƙungiyoyin da Ronaldo zai iya komawa, saboda rashin jin daɗinsa da irin goyon bayan da hukumomin Saudiyya ke bai wa ƙungiyarsa.

Sakamakon taƙaddamar Ronaldo ya ƙauracewa wasanni biyu da ƙungiyarsa ta buga a baya-bayan nan, tare da Al-Riyadh da kuma Al-Ittihad.