Shugaban Barcelona, Joan Laporta ya miƙa ƙoƙon bara wajen masu zuba jari don ceto gagarumin shirin ƙungiyar na gyaran filin wasanta na Camp Nou.
Barca ta koma kasuwar sayar da hannun jari tana neman kuɗin da ya kai euro miliyan 210, a wani mataki da ya ƙara nuna matsanancin ƙarancin kuɗi da ke damun ƙungiyar.
Wata sanarwa daga ƙungiyar ta ce matakin ya zama wajibi saboda matsalar lokacin shigowar kuɗaɗenta, kasancewar filin wasanta na Spotify Camp Nou bai koma aiki cikakke ba wajen samar da kuɗin-shiga.
A halin yanzu ana jiran kwamitin amintattu na ƙungiyar ya amince da matakin a babban taronsu.
Bayanai sun nuna cewa kafin wannan yunƙuri na neman kuɗi daga kasuwar hannun jari, Barca ta nemi kuɗi a kasuwar lamuni a 2021 da 2024.
Rahotanni sun ce tun da fari, Barca ta samu miliyan €210 garanti daga kuɗaɗen kamfanonin talabijin.
Euro miliyan 105 cikin kuɗin lamunin tuni aka nemo shi a Yulin 2026, kan kuɗin ruwa da ya kai kashi 5.14% sakamakon yawaitan masu son zuba jari.
Amma sai a Oktoba zuwa Nuwamba ne za a kammala wannan zagayen cinikin. Kamfanin hada-hadar kuɗi na Goldman Sachs shi ne shirya cinikin.



















