| Hausa
WASANNI
2 minti karatu
An saka wa wata sabuwar halitta da aka gano sunan golan Cape Verde, Vozinha
Ɗanwasan mai shekaru 40, ya tare ƙwallo har sau bakwai, inda ya samu yabo da jinjina da masoya ƙwallo a duniya.
An saka wa wata sabuwar halitta da aka gano sunan golan Cape Verde, Vozinha
Mai shekaru 40, Vozinha ya nuna bajintar da ta ja hankalin duniya a gasar Kofin Duniya ta FIFA 2026.

Vozinha, tauraron golan ƙasar Cape Verde ya samu wata karramawa da bai yi tsammani ba, inda aka laƙaba wa wata nau’in halittar ruwa mai kwanso da aka gano, sunan ɗanwasan.

Wani mai bincike ɗan Sifaniya, Jesus Ortea ne ya karrama Vozinha don yabawa da bajintar da ya nuna a gasar Kofin Duniya, inda ya taimaka wa ƙasarsa kafa tarihi a karonta na farko na shiga gasar.

An ba wa sabuwar halittar da aka gano sunan “Aldisa vozinhai”. Halittar nau’in ɗan ƙaramin dodon koɗi ne ja, wanda tsayinsa bai wuce milimita huɗu ba, wanda a baya kimiyya ba ta san da shi ba kafin Ortea ya wallafa bayani kansa.

An gano halittar ne a yankin Caribbean kusa da Havana, a Cuba, da Guadeloupe. Kuma Ortea ya daidaita lokacin wallafa bincikensa ya yi daidai da Kofin Duniya, bayan Vozinha ya zama gwarzon wasa a wasan da Cape Verde ta yi canjaras da Sifaniya, 0-0.

Ɗanwasan mai shekaru 40, ya tare ƙwallo har sau bakwai, inda ya samu yabo da jinjina da masoya ƙwallo a duniya.

Jesus Ortea ya ce ya laƙaba wa halittar sunan Vozinha don godiya ga al’ummar Cape Verde. Kuma da ma yana da alaƙa da ƙasar bayan ya samu Lambar Yabo Kan Muhalli a 2023, saboda aikinsa a nazarin halittun ruwa a tsibirin.

Ba wannan ne karon farko da Ortea ya karrama wani ɗanwasa ta wannan hanya ba. Mai binciken wanda farfesa ne a jami’ar University of Oviedo, a 2019 ya saka sunan tsohon ɗanwasan Real Madrid kuma golan Costa Rica, Keylor Navas.

Kafin wannan, Vozinha ya samu shuhura sakamakon ƙoƙarinsa a gasar. Ya samu ƙaruwar mabiya a Instagram daga 50,000 kafin Cape Verde ta fara wasa, zuwa miliyan 28.5 a lokacin buga wannan labari.

Rumbun Labarai
Masu adawa da Infantino sun yi barazanar gudanar da gasar kofin duniya ba a karkashin FIFA ba
WAFCON: Tawagar Super Falcons ta Nijeriya mai 'yanwasa 10 ta doke Zambia
Infantino ya ce FIFA ta fasa shirin sayar da hannayen-jari na Kofin Duniya ga ‘yan kasuwa
FIFA ta ce 'babu wanda zai sayar da ƙwallon ƙafa'
UEFA ta sha alwashin ƙaurace wa FIFA idan aka ci gaba da shirin sayar da Gasar Kofin Duniya
Infantino ya goyi bayan ƙudurin saka hannun jari na FIFA, ya ce 'dama ce ta musamman'
UEFA ta soki shirin Infantino na $4.2bn don zuba jari a Gasar Kofin Duniya ta FIFA
An nada Zinedine Zidane a matsayin sabon kocin tawagar kwallon kafa ta Faransa
Yan Diomande ne zai kasance dan Ivory Coast na farko da zai buga wa Real Madrid wasa
Real Madrid ta sanya fam miliyan 137 kan Vinicius Junior
Lamine Yamal: Gwarzon Kofin Duniya na Spain ɗan asalin Moroko da Equatorial Guinea
Norway za ta shigar da ƙara ga hukumar FIFA game da ce-ce-ku-ce kan jan katin Balogun
Real Madrid na farautar zakaran kofin duniya Ferran Torres daga wajen Barcelona
Yadda goyon bayan Falasɗinu ya haɗa kan Musulmai suka goyin bayan Spain a Gasar Kofin Duniya na 2026
Sifaniya ta zama ƙasa ta farko da ta riƙe Kofin Duniya na maza da na mata, da kofin nahiya a tare
An sayar da jesin da Pele ya saka a wasan ƙarshe na Kofin Duniya a 1958 kan $4.9m
Likitan tawagar Senegal 'likitan mata' ne, in ji shugaban hukumar kwallon kasar
Za a yi karon-battar taurari a wasan Faransa da Sifaniya na zagayen semi-fainal
Tsohon ɗanwasan Man United, Diego Forlan zai zama kocin Uruguay
Argentina ta doke Switzerland 3-1, ta shiga matakin dab da na ƙarshe a Gasar Kofin Duniya