| Hausa
AFIRKA
3 minti karatu
Aljeriya da Benin sun nuna goyon baya ga Nijar bayan hari kan filin jiragen sama
Aljeriya da Benin sun shiga sahun kasashen duniya wajen la’antar harin ‘yan ta’adda a filin jiragen sama mafi girma a Nijar.
Aljeriya da Benin sun nuna goyon baya ga Nijar bayan hari kan filin jiragen sama
Lamarin ya tunatar da hari makamancin haka da ya afku a a watan Janairu. / AP

Aljeriya da Benin sun yi Allah wadai da harin ta'addancin da aka kai kan filin jirgin saman Diori Hamani da sansanin sojin sama na kusa da su a babban birnin Nijar, Yamai ranar Alhamis, yayin da suke nuna goyon baya ga gwamnati da al'ummar Nijar.

Ma'aikatar Harkokin Wajen Aljeriya, a cikin wata sanarwa, ta yi Allah wadai da harin tare da bayyana "babar suka da kin amincewa" kan harin, tare da sake jaddada cikakken hadin kan Aljeriya da Nijar.

"A cikin wannan yanayi mai wahala, Aljeriya ta sake jaddada cikakken hadin kan ta ga al'ummar Nijar da gwamnati a kan wannan mummunan harin, wanda ke da nufin kawo cikas ga tsaro da kwanciyar hankali na 'yar uwa Nijar," in ji sanarwar da aka buga a shafin X.

Kasar Arewacin Afirka ta kuma sake nanata goyon bayanta ga hukumomin Nijar a yakin da suke yi da ta'addanci kuma ta yi alkawarin karfafa hadin gwiwar kasashen biyu da na shiyyar don tunkarar barazanar rashin zaman lafiya da tsaro a fadin yankin.

Benin ta sake jaddada goyon baya

Benin ma ta mayar da martani ga harin, tana mai bayyana shi a matsayin wani abu da ba za a yarda da shi ba na cin zarafi ga wani waje mallakin fararen hula da ke da muhimmanci.

A cikin wata sanarwa, gwamnatin Benin ta yi Allah wadai da harin da aka kai a filin jirgin saman Diori Hamani da kakkausar murya, tana mai cewa harin ya jefa rayukan fararen hula cikin hatsari da gangan kuma ya yi barazana ga tsaron kasar.

"Benin ta sake jaddada goyon bayanta ga al'ummar Nijar da suke 'yan uwan juna, Shugaba Abdourahamane Tiani, da hukumomin Jamhuriyar Nijar. Tunaninmu yana tare da wadanda abin ya shafa da iyalansu yayin da muke tunawa da kyakkyawar dangantakar 'yan uwantaka da abota da ke tsakanin kasashenmu biyu," in ji sanarwar.

Kwatano ta ce sakon goyon bayanta ya nuna dawwamammiyar dangantaka tsakanin kasashen biyu makwabtan juna.

Yunkurin ruguza filin jirgin sama

Harin, wanda ya faru da asubahi, ya haifar da mummunan rikici da ya shafi manyan makamai bayan da aka rawaito cewa 'yan ta'adda sun ketare iyakar filin jirgin saman. Lamarin ya sake farfaɗo da tunanin wani yunƙurin kai hari makamancin haka a watan Janairu.

An kashe maharan 22 a Nijar kuma an kama kimanin wasu 20 da ake zargi bayan wani hari da aka kai wa filin jirgin saman Niamey a ranar Alhamis, a cewar wani rahoto na wucin gadi da ma'aikatar tsaro ta fitar.

Hukumomin sun bayar da rahoton cewa an kashe jami'an tsaro 11, tare da fararen hula biyu.

Mutane hudu sun jikkata a lokacin harin.

Kungiyar 'yan ta'adda ta JNIM mai alaka da Al Qaeda ta ce ta kai "wani harin kunar bakin wake" a filin jirgin saman Diori Hamani da kuma sansanin sojoji da ke makwabtaka da su.