'Yanwasan Super Eagles 21 sun isa birnin Antalya na Turkiyya don wasannin sada zumunta
Za a gudanar da wasannin sada zumuntar ne tsakanin ƙasashe uku, Nijeriya, Jordan, da Iran wadda ke cikin rikicin da ake yi.
Aƙalla 'yanwasa 21 na tawagar Super Eagles ta Nijeriya ne suka isa birnin Antalya na Turkiyya domin shirye-shiryen buga wasannin sada zumunta.
Tun ranar Litinin ne aka buɗe sansanin Super Eagles ɗin, inda masu horarwa da sauran jami'ai suka isa birnin, ciki har da mataimkan koci Daniel Ogunmodede da Fidelis Ilechukwu.
'Yanwasan da suka fara hallara don yin atisaye gabanin wasannin sun kai 21 zuwa safiyar Laraba.
Za a gudanar da wasannin sada zumuntar ne tsakanin ƙasashe uku, Nijeriya, Jordan, da Iran wadda ke cikin rikicin da ake yi.
A baya an shirya buga wasanni na ƙasashe uku a ƙasar Jordan, amma sakamakon yaƙin Iran da Amurka -İsra'ila, sai aka sauya wajen wasanin.
Yanzu a birnin yawon buɗe-ido na Antalya da ke kudu maso yammacin Turkiyya aka yi masauki da kuma filin wasan da za a yi duka wasannin.
Jordan da Iran suna shirya wa gasar Kofin Duniya na FIFA 2026 ne. Amma ita Nijeriya ta gaza samun cancantar buga gasar da za a yi a ƙasashen Amurka, Canada da Mexico ba.
Ga jerin 'yanwasan da suka hallara a sansanin Antalya:
1. Fisayo Bashiru
2. Iwobi Alex
3. Emmanuel Oluwasegun
4. Yira Sor
5. Onuachu Paul
6. Philip Otele
7. Semi Ajayi
8. Moses Simon
9. Uzoho Francis
10. Bruno Onyemaechi
11. Bright Osayi
12. Frank Onyeka
13. Adebayo Adeleye
14. Ademola Lookman
15. Akor Adams
16. Chidera Ejuke
17. Raphael Onyedika
18. Igoh Ogbu
19. Maduka Okoye
20. Samuel Chukwueze
21. Zaidu Sanusi (edited)