| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
3 minti karatu
Masar ta yi kira ga kwamitin tsaro na MƊD ta dakatar da faɗaɗa [harin] da Isra'ila ke yi a Lebanon
Masar ta yi kira ga kwamitin tsaro na Majslaisar Ɗinkin Duniya (MƊD) ta daukin matakin gaggawa domin dakatar da hare-haren sojin da Isra'ila ke yi da kuma hare-haren ƙasa da take yi a Lebanon.
Masar ta yi kira ga kwamitin tsaro na MƊD ta dakatar da faɗaɗa [harin] da Isra'ila ke yi a Lebanon
Masar ta ce matakan faɗaɗawa na Isra'ila a kudanci Lebanon na barzanar janyo rashin zamna lafiya a yanlin Gabas Ta Tsakiya / AA

Masar ta yi kira ga kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD) ta ɗauki matakin gaggawa na dakatar da faɗaɗa harkar sojin da da kuste ta ƙasa da sojin Isra’ila ke yi a Lebanon, tana mai gargaɗin cewa ci-gaba da hare-haren na barazanar tsunduma yankin cikin ƙarin rashin zaman lafiya.

A wata sanarwar da ta fitar ranar Lahadi, ma’aikatar harkokin wajen Masar ta yi Allah wadai da “ci -gaba da tsangwama ” da Isra’ila ke yi kan Lebanon da kuma faɗaɗa hare-haren ƙasanta a kudancin ƙasar.

Kiran na zuwa ne sa’o’i bayan Firayim Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ba da sanarwa a wani jawabin da aka naɗa cewa dakarun Isra’ila sun karɓe iko da katafaren gini mai daɗaɗen tarihi da aka sani da Beaufort Castle, ko kuma Qalaat al-Shaqif a Larabci, a kudancin Lebanon, a wani kutse mafi nisa da ta yi cikin ƙasar cikin sama da shekaru ashirin.

Alƙahira ta ce faɗaɗa samamen ƙasa na Isra’ila ya kasance “tsagwaron ƙeta ‘yancin kan Lebanon ” da kuma “tsaban mataki na tsangwama da ya nuna niyyar Isra’ila na ƙaƙaba wani sabon yanayi na soji a ƙasa.”

'Ƙeta kan iyakan Lebanon '

Ta kuma jaddada “watsi[nta] da ko wane nau’i na ƙeta kan iyakokin Lebanon” da kuma sabunta goyon bayanta ga haɗin kan Lebanon’ da hukumomin ƙasar da kuma kan iyakokin ƙasar.

Ma’aikar ta yi kira ga wani “janyewa na nan take kuma cikakke na Isra’ila daga dukkan ƙasar Lebanon,” yana mai gargaɗin cewa ci-gaba da faɗaɗa ayyukan soji zai iya haddasa taɓarɓarewar lamuran tsaron.

Ta yi kira ga Kwamitin tsaro na MƊD da kuma masu faɗa a ji na duniya su sauƙe nauyin da ya rataya a kansu su ɗauki mataki na dakatar da hare-haren Isra’ila.

“Ci-gaba da faɗaɗa [hare-haren] zai janyo ƙarin hatsaniya da rashin zaman lafiya a yankin ,” kamar yadda ma’aikatar ta yi gargaɗi, tana mai cewa masu ruwa da tsaki na yanki da na ƙasa da ƙasa suna ƙoƙari mai zafi na rage tashin hankali.

Ganawa ta gaggawa

Ma’aikatar harkokin wajen Lebanon ta bayyana ranar Lahadi cewa ministan harkokin wajen Faransa Jean-Noel Barrot ya shaida wa takwaransa na Labanon Youssef Raggi cewa Paris za ta nemi zaman gaggawan na kwamitin tsaro na MƊD a matsayin martani ga faɗaɗa yaƙi na Isra’ila a Lebanon.

Beaufort Castle ɗaye ne daga cikin shahararrun wurare a kudancin Lebanon. Dakarun Isra’ila sun janye daga wurin a shekarar 2000 a wani ɓangare na janyewa daga abin da suke kira “yankin tsaro” wanda suka kafa a kudancin Lebanon tsakanin shekarar 1982 da shekarar 2000.