| Hausa
TURKIYYA
1 minti karatu
Ana buƙatar haɗin kai mai ƙarfi domin farfaɗo da kasuwancin duniya: Erdogan
A jawabin da ya gabatar a taron shugabannin G20 a Johannesburg da ke Afirka ta Kudu a ranar Asabar, shugaban ya bayyana goyon bayan Ankara wajen karɓar wata hanya da ta dogara ga adalci da daidaito domin sake tsarin bayar da bashi, musamman ga kasa
Ana buƙatar haɗin kai mai ƙarfi domin farfaɗo da kasuwancin duniya: Erdogan
Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa ya tarbi Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan don taron kolin shugabannin G20 a Johannesburg / Reuters
22 Nuwamba 2025

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce ana bukatar haɗin kai sosai na ƙasa da ƙasa, sabbin manufofi da kuma ɗorewar hanyoyin jigilar kayayyakin domin farfado da kasuwancin duniya.

A jawabin da ya gabatar a taron shugabannin G20 a Johannesburg da ke Afirka ta Kudu a ranar Asabar, shugaban ya bayyana goyon bayan Ankara wajen karɓar wata hanya da ta dogara ga adalci da daidaito domin sake tsarin bayar da bashi, musamman ga kasashen da ke da ƙarancin kuɗaɗen shiga.

"Ina gayyatar dukkan G20 su ɗauki ƙarin nauyi wajen gina tattalin arzikin duniya wanda ya haɗa kowa, ba a bar kowa a baya ba," in ji Erdogan.

Shugaban Turkiyya yana Johannesburg don wannan taro na kwanaki biyu wanda ya fara a ranar Asabar kuma yake mai mayar da hankali kan magance wasu daga cikin manyan matsalolin da duniya ke fuskanta.