'Yan bindiga sun yi garkuwa da masu ibada aƙalla 160 a Nijeriya
Gungun 'yan bindiga sun yi garkuwa da masu ibada 163 bayan afka wa wasu coci biyu a Jihar Kaduna a ranar Talata, kamar yadda wani jagora na cocin ya shaida wa AFP.
Gunugun ‘yan bindiga ɗauke da makamai sun sace masu ibada 163 bayan sun kai hari wasu coci biyu a Jihar Kaduna ta arwa masu yammacin Nijeriya a ranar Lahadi, kamar yadda wani limamin cocin ya bayyana wa AFP.
"Maharan sun zo da yawa sannan suka rufe ƙofofin cocukan suka tilasta wa masu ibada su fita zuwa daji," in ji Reverend Joseph Hayab, shugaban Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya a arewa, a ranar Litinin.
"Adadin wandanda suka sace shi ne 172, amma tara sun tsere, don haka 163 suna tare da su," kamar yadda Hayab ya bayyana.
Wani rahoton tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da AFP ta gani a ranar Litinin ya nuna an sace fiye da mutane 100.
Harin 'yan bindiga
'Yan bindiga sun farmaki cocin biyu yayin ibadar Lahadi a ƙauyen Kurmin Wali a karamar hukumar Kajuru.
A sau da dama gungun “'yan bindiga” suna yin garkuwa da mutane da dama don neman kuɗin fansa, kuma suna sace kayayyaki da dukiya a ƙauyuka, musamman a sassan arewaci da tsakiyar ƙasar.
A watan Nuwamba, 'yan bindiga sun sace fiye da dalibai 300 da malamai daga makarantar Katolika a Jihar Niger. An sako su makonni kaɗan cikin rukunoni biyu.