Shugaban Zambia Hichilema ya yi farin ciki da masoyan da suka ba shi kyautar kazar gida
Shugaban Zambia Hichilema ya yi farin ciki da masoyan da suka ba shi kyautar kazar gida
Shugaban Zambia Hichilema ya yi farin ciki da masoyan da suka ba shi kyautar kazar gida
Maggie Sapatu ta yi tafiya fiye da kilomita 800 don ba Shugaban Zambia Hichilema kyauta na "kaza na gida", a lokacin da wani mai goyon bayan sa Jeremiah Tembo ya yi bisa motar sa kilomita 400 don halartar jirgin shugaban.

Shugaban Zambiya Hakainde Hichilema ya jinjina wa masu goyon bayansa guda biyu da suka yi takakkiya ta musamman don nuna ƙaunarsu a gare shi bayan an sake zaɓarsa kwanan nan.

Maggie Sapatu ta yi tafiyar fiye da kilomita 800 don ba Shugaba Hichilema kyautar kazar gida ta ƙauye.

Tafiyarta daga Mwinilunga a Jihar North-Western zuwa babban birnin Lusaka ta jawo hankalin al’ummar ƙasar.

Jaridar Lusaka Times ta ruwaito cewa kyautar tana nuna ma'anar al'adu domin a cikin mutanen Lunda na Zambiya, inda matar ta fito, ana ɗaukar kyautar kaza a matsayin 'al'adar nuna girmamawa mai zurfi, ƙauna, godiya da karamci'.

Sannan wani masoyin Shugaba Hichilema ya nuna goyon baya ta wata hanyar daban mai ban sha'awa.

Jeremiah Tembo ya hau keke daga Karamar Hukumar Lusangazi a Jihar Eastern zuwa Lusaka don halartar rantsuwar Shugaba Hichilema. Wannan nisan ya haura kilomita 400.

'Ƙauna da goyon baya'

Su biyun sun ce sun fara waɗannan bulaguro ne a matsayin alamar ƙauna da goyon bayansu ga shugaban.

Shugaba Hakainde Hichilema ya gode musu saboda waɗannan ayyuka.

A ranar Lahadi, 6 ga Satumba bayan karɓar su a Fadar Shugaban Kasa, ya ce duk da kasancewarsa shugaba ga fiye da mutane miliyan 21 na Zambiya, 'kowane ɗan ƙasa yana kawo wani muhimmin abu a ci gaban kasa da nuna goyon baya'.

A cikin wani sako a shafin sada zumunta, ya tabbatar wa 'yan Zambiya cewa 'mafi alheri zai zo nan gaba'.

Duk da haka, bayan shagulgulan cin kaza da bukukuwa, yanayin siyasa na ci gaba da kasancewa mai cike da tayar da jijiyar wuya.

Shugaban Zambiya, wanda ya hau kujerar mulki a 2021, an sake rantsar da shi don wa'adi na biyu a ranar 1 ga Satumba bayan nasarar da ya samu a zaɓen wata da ya gabata, bisa ga sakamakon hukuma.

An tsare babban abokin hamayyarsa, Brian Mundubile da abokin takararsa Makebi Zulu, waɗanda suka ƙi yarda da sakamakon, bisa zargin cin amanar ƙasa.

Su da magoya bayansu sun ƙaryata zargin cin amanar, suna cewa an yi zargin ne da manufar siyasa.