Jagoran Addinin Iran ya ce an buɗe ‘sabon babi’ kan kula da Mashigar Hormuz, ya nemi diyyar yaƙi

Jagoran Addinin Ƙasar Iran, Mojtaba Khamenei, ya bayyana a cikin wani saƙo cewa gudanar da Mashigar Hormuz “tabbas za ta shiga wani sabon babi,” yayin da ya ƙara da cewa Iran za ta buƙaci diyyar dukkan asarar da ta yi sanadiyyar yaƙin.

By
Jagoran Addinin Iran ya ce an bude ‘sabon babi’ kan kula da mashigar Hormuz, yana mai neman diyyar yaki / Reuters

Jagoran Addinin Ƙasar Iran ya bayyana cewa Mashigar Hormuz tana shiga wani sabon mataki, a daidai lokacin da yake neman diyyar ɓarnar da aka yi lokacin yaƙin da ƙasarsa ta yi da Isra’ila da Amurka.

Jagoran Addinin Ƙasar Iran, Mojtaba Khamenei, ya bayyana a cikin wani saƙo cewa tafiyar da Mashigar Hormuz “tabbas za ta shiga wani sabon babi,” yayin da ya ƙara da cewa Iran za ta buƙaci diyyar dukkan asarar da ta yi sanadiyyar yaƙin.

Saƙon na ranar Alhamis, wanda ofishinsa ya fitar a rana ta 40 tun bayan kisan mahaifinsa, tsohon Jagoran Addinin Ƙasar Ali Khamenei, ya bayyana mutuwarsa a matsayin “babban rashi da tarihi ba zai manta da shi ba” kuma rashi ne ga al’ummar Iran, sannan ɗaya daga cikin lokuta mafi baƙin ciki a tarihin ƙasar na baya bayan nan.

Ya bayyana wannan mataki na yanzu a matsayin ci gaba da tafarkin mahaifinsa.

Khamenei ya ce Iran za ta buɗe wani sabon babi cikin hikima dangane da Mashigar Hormuz.

“Kula da Mashigar Hormuz tabbas zai shiga wani sabon mataki,” in ji shi, ba tare da yin ƙarin bayani ba.

Khamenei ya jaddada cewa Iran za ta bi kadin doka da kuma neman diyyar dukiyar da aka lalata.

“Tabbas ba za mu bar masu laifin da suka kai wa ƙasarmu hari su tafi ba tare da hukunci ba,” in ji shi. Ya ƙara da cewa Iran za ta “nemi diyyar dukkan ɓarna, da kuma jinin shahidai da waɗanda suka ji rauni.”

Waɗannan kalamai na zuwa ne yayin da Iran ke shirye-shiryen tattaunawa da Amurka a ƙasar Pakistan, wanda ake sa ran za a fara ranar Asabar ƙarƙashin shirin shiga tsakani da Pakistan ke jagoranta, kuma za a ci gaba da yin hakan har tsawon mako biyu.

Iran ta ce tattaunawar na da nufin kammala muhimman bayanai na yarjejeniyar da za a iya cimma, tana mai jaddada cewa hakan ba yana nufin karshen rikici ba ne.

Haka kuma, Khamenei ya yi gargaɗin cewa Iran tana nan cikin shirye don mayar da martani ga duk wani sabon hari.

“Muna jiran a ce mana kule…” in ji shi, yana mai kara da cewa duk wani kuskure da makiya suka yi zai gamu da martani mai tsanani.

Yankin ya kasance cikin dar-dar tun bayan da Isra’ila da Amurka suka kaddamar da hari kan Iran a ranar 28 ga watan Fabrairu, inda aka kashe akalla mutane 3,000, ciki har da tsohon jagoran addinin kasar.

Iran ta mayar da martani da hare-haren jirage marasa matuka da makamai masu linzami kan Isra’ila, Jordan, Iraki da kasashen Tekun Fasha da ke da sansanonin dakarun Amurka, wanda ya janyo asarar rayuka da barna ga ababen more rayuwa, sannan ya jawo cikas ga kasuwannin duniya da zirga-zirgar jiragen sama.

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da tsagaita bude wuta na mako biyu a ranar Alhamis, yana mai cewa Iran ta gabatar da sharudda guda 10 “wadanda za a iya karba,” yayin da ake sa ran tattaunawar za ta nuna ko za a iya cimma yarjejeniya ta dogon zango.