An kama ɓarayin daji a filin jirgin sama a Nijeriya

Hukumar FAAN mai kula da filayen jiragen saman Nijeriya ta ce an yi kamen a wani aikin hadin gwiwa tsakanin jami'an tsaron filin jirgin saman da waɗanda ke yankin.

By
Hukumar ta ce lamarin ya faru ne a filin jiragen saman Akure, babban birnin jihar Ondo da ke kudu maso yammacin ƙasar

Hukumar FAAN mai kula da filayen jiragen saman Nijeriya ta ce an kama ‘yan fashin daji huɗu a filin jiragen saman Akure, babban birnin jihar Ondo da ke kudu maso yammacin ƙasar.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Lahadi da daddare wadda daraktan hulɗa da jama’a da kare masu amfani da filayen jiragen sama, Henry Agbebire, ya sanya wa hannu, FAAN ta ce an yi kamen ne a wani aikin haɗin gwiwa tsakanin jami'an tsaron filin jirgin saman da na yankin.

Ta ƙara da cewa lamarin ya auku ne bayan an samu rahoton cewa an ga wasu mutane da ba yarda da su ba a bayan katangar filin jirgin saman na Akure.

Daga nan sai jami’an tsaron filin jirgin saman da ‘yansanda da ma sauran jami’an tsaro da ke wurin suka ƙaddamar da aikin haɗin gwiwa, in ji sanarwar.

“A lokacin aikin, an ga wasu mutane da suke ƙoƙarin tserewa daga wurin. Daga baya dai tawagar jami’an tsaron ta kama huɗu daga cikin waɗanda ake zargin kuma ta miƙa su ga rundunar ‘yansandan Nijeriya da ke wurin domin ƙarin tambayoyi,” a cewar FAAN.

Hukumar ta yaba da haɗin gwiwa da wuri da aka samu tsakanin jami’an tsaron filin jirgin saman da ‘yansanda da sojoji da ma jami’an tsaron yankin, ciki har da Amotekun da ‘yan sa-kai a wajen kamen.

Ta ƙara da cewa lamarin ya sake nuna muhimmancin ƙarfafa katangun kare filayen jiragen sama na ƙasar, inda ta ce wannan ne ya sa gwamnatin tarayya ta gaggauta gina katangu na zamani a filayen jiragen sama a faɗin ƙasar.

Ta ce an fara aiki domin inganta tsaron filayen jiragen saman daga mataki zuwa mataki domin tabbatar da tsaron filayen jiragen saman da ke ƙarƙashin hukumar FAAN a faɗin ƙasar.

Sanarwar ta ba da tabbaci ga matafiya da ma al’ummomin da ke yankin filayen jiragen sama game da jajircewar hukumar wajen tabbatar da kariya da tsaron na dukkan kayayyakin filayen jiragen sama a faɗin ƙasar.