An tabbatar da cewa akalla yara 21,000 aka kashe a Gaza a cikin kwanaki 1,000 na yaƙi, yayin da daruruwan dubbai suka rasa matsugunansu kuma aka hana su ilimi, in ji kungiyar bayar da gaji ta Save the Children a ranar Alhamis.
A ranar da aka cika kwanaki 1,000 na yaƙin, kungiyar bayar da agajin ta ce yara suna ci gaba da mafarkin zaman lafiya duk da rasa gidajensu, makarantu da kuma jin daɗin tsaro.
"Kowace rana tsawon kwanaki 1,000 da suka gabata, duniya ta gaza kare yara miliyan ɗaya a Gaza, ta hanyar rashin shiga tsakani don dakatar da kisa da nakasta yara," in ji Daraktan Save the Children na Yankin Gabas ta Tsakiya, Arewacin Afirka da Gabashin Turai Ahmad Ahendawi.
Kungiyar ta ce an tabbatar da cewa an kashe akalla yara 21,000 a lokacin yaƙin, kodayake adadin da aka kashe na iya fin haka yawa saboda da yawa daga cikin su suna nan a ƙarƙashin nuraguzan gine-gine.
Ta ce sama da yara 800,000, kimanin kashi 80 cikin 100 na yaran Gaza, sun rasa matsuguni, yayin da yara 625,000 na Gaza da suke zuwa makaranta suka rasa karatunsu na tsawon shekaru uku.
Yara 245,000 na fuskantar hatsari
Yaran da suka yi magana da Save the Children sun bayyana rayuwa cikin tsoro a kowane lokaci tare da yin fatan samun makoma mai kyau.
"Za mu iya mutuwa a kowane lokaci. Ina fatan yaƙin ya tsaya saboda mu," in ji Amani, mai shekaru 14.
"Ina fatan yaƙin ya tsaya domin in ci gaba da karatuna a Gaza da kuma rayuwa da 'yancina a matsayin ɗan adam kamar kowace yarinya a wasu ƙasashe. Akwai yara da yawa a Gaza waɗanda ba a jin muryoyinsu."
Wata yarinya 'yar shekara 14, Bisan, ta ce: "Burina shi ne yaƙin ya tsaya, kowannenmu ya koma gidansa, kuma rayuwarmu ta koma yadda take."
Haka kuma yanayin jin kai yana ci gaba da taɓarɓarewa, inda aka kiyasta yara 245,000 suna cikin hatsarin rashin isasshen abinci mai gina jiki ko kuma waɗanda suka kamu da yunwa saboda tallafin jinkai, in ji ƙungiyar.
Kungiyar ta Save the Children ta ambaci wani rahoton Kwamitin Bincike na Majalisar Dinkin Duniya da ya yi zargin cewa hukumomin Isra'ila da jami'an tsaro sun kai hari kan yaran Falasɗinawa da gangan, wanda ya haifar da zargin kisan kare dangi, laifukan cin zarafin bil'adama da laifukan yaƙi a Gaza.
Kungiyar ta yi kira da a tsagaita wuta nan take kuma na dindindin, a dauki alhakin laifukan da aka aikata wa yara, sannan a dakatar da jigilar makamai zuwa Isra'ila.
Ko da yake an cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta a watan Oktoban 2025, Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare Gaza. Gabaɗaya, yakin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 73,000 tare da lalata yankin da zai ɗauki shekaru kafin a sake gina shi.










