Jakadan Saudiyya a Nijeriya, Yousef bin Mohammed Al-Balawi, ya gana da attajirin Afirka kuma shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, domin tattauna damarmaki na zuba jari a fannonin makamashi da ababen more rayuwa.
Ganawar da suka yi domin ƙarfafa dangantakar tattalin arziki da ke tsakanin Nijeriya da Saudiyya an yi ta ne ranar Jumma’a a gidan jakadan da ke Abuja, a cewar wani saƙo da jakadancin Saudiyya a Nijeriya ya wallafa a shafin X.
Da yake magana a lokacin ganawar, jakadan ya ce tattaunawar ta nuna yadda dangantaka tsakanin Saudiyya da Nijeriya ke haɓaka da kuma yadda ƙasashen biyu suka jajirce wajen inganta dangantaka a muhimman fannoni ciki har da na makamashi da masana’antu da ababen more rayuwa.
Al-Balawi ya ce tattaunawar ta mayar da hankali kan yadda dangantaka tsakanin ƙasashen ke sauyawa, tare da bayyana damarmaki na zuba jari da ke da ke tsakaninsu.
Ya ƙara da cewa ƙasashen biyu suna da haɗin kai na tattalin arziki mai ƙarfi da ke sauyawa.

“Masaurautar Saudiyya da Nijeriya suna da dangantaka ta tattalina arziki mai ƙarfi da ke sauyawa, kuma wannan ganawar ta nuna jajircewarmu ta ƙara gini a kan wannan tushen ta hanyar zuba jari mai tsari da kuma haɗin gwiwa,” in ji Al-Balawi.
Jakadan ya ce tattaunawar ta mayar da hankali ne kan damarmaki na zuba jari da ɓangarorin biyu suke so, musamman game da sakamakon ziyarar da Dangote ya kai Saudiyya kwanan baya.
“An mayar da hankali kan ziyarar Dangote ta kwanan baya zuwa masarautar tare da damarmaki masu alamar nasara da rukunin kamfanonin Dangote ke da su a Saudiyya,” in ji shi.
Al-Balawi ya kuma nuna cewa akwai damarmaki ga masu zuba jari ‘yan Saudiyya a cikin ayyukan rukunin kamfanonin Dangote.
“Mun kuma yi nazari game da muhimman damarmaki da rukunin kamfanonin Dangote ke iya bai wa masu zuba jari ‘yan Saudiyya da ke son faɗaɗa jarinsu a Nijeriya da ma faɗin Afirka,” in ji shi.
An ƙarƙare ganawar ne da liyafar cin abinci da aka yi domin karrama Dangote, inda jakadan ya miƙa masa wata kyauta ta tunawa da ziyarar, wadda ya bayyana ta a matsayin “wata alama ta dangatanta mai ƙarfi da ke ƙara girma tsakanin ƙasashenmu biyu”.
Dangote ya bayyana ganawar a matsayin mai amfani kuma ya nuna kyakkyawan fata game da harkokin haɗin gwiwa na gaba.
“Muna ganin yiwuwar haɗin gwiwa mai ƙarfi da abokan kasuwanci na Saudiyya, musamman a fannoni da suke haɓaka ci-gaban masana’antu da ci-gaban tattalin arziki,” in ji shi.
Cin gashin kai
A makon jiya shugaban rukunun kamfanonin Dangote ya sha alwashin gina matatar mai a Gabashin Afirka idan shugabannin yankin suka mara masa baya.
Aliko Dangote ya bayyana hakan a wani taro na zuba jari na yankin da aka yi a ƙasar Kenya inda ya ce kamfaninsa ya shirya domin gina matatar a Gabashin Afirka irin wadda ya gina a Legas.
Aliko Dangote ya ce nahiyar Afirka na buƙatar gina masana’antu ta yadda za ta iya cin gashin kanta ba tare da dogara kan wasu sassan duniya ba.

















