Me ya sa Trump da masu sharhi da ke da ra’ayin rikau ke sa ido kan al’ummar Somalia da ke Minnesota?

Shugaban Amurka da masu sharhi da ke da ra’ayin rikau na yin nune ga jama’ar Somalia a Minnesota, suna alakanta su da ayyukan zamba, ta’addanci da barazanar ‘yan gudun hijira, wanda ke nuni ga alamar Kyamar baki, Kyamar Musulunci da daukar mataki.

By
Shugaban Amurka Donald Trump yake murmushi a Fadar White House a ranar 2 ga Dismaban 2025 yayin bayar da wata sanarwa. / Reuters / Reuters

A 'yan kwanakin nan, Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya ƙara yawan kalamansa na kakkausar suka ga baƙi 'yan Somalia da ke Minnesota, yana kiran 'yan ciranin Somalia da "shara" kuma yana cewa "ba sa yin komai sai korafi." Ya dage da cewa ya kamata su "koma inda suka fito."

Shugaban ya ƙara yawan sukar da yake yi wa 'yan Somalia a Amurka tun bayan harbin da aka yi wa wasu sojojin Tsaron Kasa biyu a makon da ya gabata a Washington, harbin da ya kashe ɗaya daga cikin sojojin kuma aka tuhumi wani ɗan Afghanistan da aikata laifin.

A lokaci guda, jami'an shige da fice na tarayya suna shirin ɗaukar matakin murkushewa.

Hukumar Shige da Fice da Kwastam ta Amurka (ICE) tana ƙaddamar da wani "aikin shige da fice mai tsauri" wanda ke kai samame ga ɗaruruwan 'yan Somalia da dama a yankin Twin Cities.

Kimanin 'yan Somalia 80,000 ne ke zaune a Minnesota, galibi a yankin Twin Cities metro.

Hukumar ICE za ta tura jami'ai kusan 100 daga ko'ina cikin ƙasar don tallafa wa aikin, wanda zai fi mayar da hankali kan baƙi 'yan Somalia waɗanda ke da umarnin korar su.

Yawancin 'yan Somalia a yankin Minneapolis-St Paul ko dai 'yan ƙasa ne, masu izinin zama na dindindin ko kuma suna da wani matsayi da doka ta amince da shi.

Trump ya kuma ɗauki matakin soke kariyar da aka bai wa mutane da yawa a cikin al'umma. Ya kawo ƙarshen matsayin shari'a na musamman (Matsayin Kariya na Wucin Gadi, TPS) ga 'yan Somalia, yana ambaton ikirari da aka fayyace dalla-dalla na "ayyukan halatta kuɗin zamba."

Waɗannan matakan sun tayar da hankali sosai tsakanin 'yan Somalia, jami'an yankuna, da masu fafutukar kare haƙƙin jama'a, ba wai saboda tasirin shari'a kai tsaye ba, har ma saboda yanayin ɓata sunan al'umma gaba ɗaya.

Batun ‘zamba da ta’addanci’

Wannan sa ido da nune na baya-bayan nan ya dora ne akan zarge-zargen da aka daɗe ana yi cewa wani ɓangare na al'ummar Somalia a Minnesota na da hannu a zambar kudaden walwala da kuma tallafin gaggawa, tare da iƙirarin cewa wasu daga cikin kuɗin da aka samu sun ƙare ne don tallafa wa Al-Shabab - wata ƙungiyar ta'addanci mai tayar da kayar baya da ƙasar Somalia da mutanenta suka sha wahala a kanta tsawon shekaru.

Manyan zarge-zargen da ake yi sun haɗa da cewa da yawa daga cikin waɗanda ake tuhuma da zamba a cikin manyan shari'o'in kudaden walwala da tallafin annobar Corona 'yan Somalia ne kuma wasu daga cikin kuɗin da aka samu ta hanyar zamba an yi zargin an tura su ƙasashen waje ta hanyar hanyoyin da na hukuma ba (yawanci waɗanda 'yan Somalia mazauna ƙasashen waje ke amfani da su), sannan aka tura su zuwa ga Al-Shabab.

Wannan zargi da ake maimaita shi sosai a kafofin watsa labarai na yau da kullum, ana amfani da shi don nuna ‘yan gudun hijirar Somalia a matsayin barazanar tsaro.

Wani iƙirarin kuma shi ne cewa Minnesota ta zama "cibiyar ayyukan zamba na satar kudade," a cewar wasu labaran da masu sharhi masu ra'ayin mazan jiya suka kukuza, don haka ya cancanci tsauraran matakai, gami da kawo ƙarshen TPS da ƙara korar mutane.

A kan wannan dalili, masu fafutuka kamar Christopher F Rufo da wasu kafofin watsa labarai da suka amince da hujjojinsa sun yi kira a bainar jama'a da a yi taka-tsantsan wajen aiwatar da hukunci mai tsauri kuma sun taimaka wajen tsara labarin cewar 'yan Somalia a Minnesota suna yin barazanar kudi da tsaro ga Amurka.

Me ya sa wannan labarin yake da hatsari

Duk da cewa an tuhumi mutane da dama a shari'o'in zamba, yawancinsu 'yan ƙasar Amurka ne, ba 'yan cirani na baya-bayan nan ba.

Masu gabatar da ƙara na tarayya, duk da sanin laifukan da suka shafi ta'addanci a baya, ba su gabatar da wata ƙarar da ke da alaƙa da ta'addanci a cikin sabbin shari'o'in zamba ba, wanda ke nuna rashin shaidar cewa an aika ko amfani da kuɗin da aka sata zuwa ga Al-Shabab.

A cewar masu suka na cikin gida, ikirarin da ke alakanta kuɗaɗen Somalia da ta'addanci ya yi watsi da gaskiyar cewa yawancin 'yan Somalia a ƙasashen waje na aika kuɗi zuwa gida bisa doka da kuma don tallafin zamantakewa, sau da yawa ta hanyar hanyoyin aika kudi na yau da kullun (kamar hawala) waɗanda ake amfani da su tun kafin a yi waɗannan zarge-zarge.

Tasirin mafi girma shi ne yunƙurin ƙiyayya ga Musulunci da ƙiyayya ga baƙi. Ta hanyar sanya duk baƙin da suka zo daga Somalia a matsayin masu zamba ko masu yiwuwar aikata ta'addanci, labarin yana sanya zargi kan daukacin al'ummar wata ƙabila da addini gaba ɗaya maimakon mayar da hankali kan mutanen da ake zargi da aikata laifukan.

Masu suka na cewa duk da ya kamata a bi diddigin zamba, kamar a kowace al'umma, amma haɗa hakan da kuɗaɗen ta'addanci da amfani da shi don bakantar da al'umma gaba ɗaya abin da bai dace ba ne, nuna wariya ne da kuma cutarwa.

Me ya wannan batu ya zama mai wasu manyan manufofin siyasa

Dalilai da dama sun sa al'ummar Somalia da me Minnesota zama karkatacciyar kuka mai dadin hawa.

Al'ummar Somalia kuma ‘yan kasar Amurka sun taru a wasu unguwanni; da yawa daga cikinsu baƙi ne, 'yan gudun hijira, ko kuma suna da alaƙa ta kud da kud da Somalia, wanda hakan ya sa suka fi bayyana ga duniya a matsayin wata al’umma.

Al’amuran zamba na janyo manyan kanun labarai, wanda wasu masu fafutuka da masu sharhi ke amfani da shi don bayyana dora laifin kan al’umma gaba ɗaya.

Wannan yana ƙara haifar da tsoro, wariya kuma yana goyon bayan manufofin siyasa na tsaurara matakan shige da fice.

Ga masu ruwa da tsaki a siyasa waɗanda ke son yin amfani da ra'ayin ƙiyamar baƙi, bayyana al'umma marasa rinjaye a matsayin mai wahalar sha’anin kuɗi da barazanar tsaro na shafar dukka bangarorin biyu.

Ta hanyar zargin al'umma da take baƙuwa galibi Musulmai, na ingiza labaran ƙiyayya ga Musulunci, waɗanda za su iya tasiri kan jefa kuri’a.

Ta hanyar neman daukar matakai masu karfi kamar kawo ƙarshen TPS, korar jama'a, da kuma tilasta wa ICE yin amfani da ƙarfi, kalaman sun tashi daga "hukunta mutanen da suka aikata zamba" zuwa "hukunta al'umma gaba ɗaya."

Martanin jama’a

Jami'an da aka zaɓa a yankin da shugabannin birni a Minnesota sun yi Allah wadai da suka da nufar da ake yi wa 'yan Somalia.

Jami'ai a Minneapolis sun ce a ranar Talata ba su san da wani samame na gaggawa da ake kai wa 'yan Somalia a yankin ba.

Magajin garin Minneapolis Jacob Frey, yayin da yake mayar da martani ga rahoton da aka fitar a jaridar The New York Times cewa sama da jami'an shige da fice na tarayya 100 suna shirin kai samame kan birninsa da maƙwabciyarsa St Paul don kai farmaki kan mazauna ‘yan Somalia da ba su da takardun zama, ya ce, ko da kuwa za a kai samamen, to al'ummar Somalia dai za su sami goyon baya ta kowace hanya daga hukumomin yankin.

Frey, ɗan Democrat, ya ce 'yan sandan yankin ba za su yi aiki tare da wakilan tarayya kan duk wani batu na shige da fice ba, kuma ya yi suka sosai kan iri suka da bakantarwar da Trump ya yi wa al'ummar Somalia kwanan nan.

"Yin barna ga wata ƙungiya abu ne mai ban dariya a kowane hali," in ji Frey.

Frey ya ce al'ummar ta kasance mai fa'ida a fannin tattalin arziki da al'adu ga yankin kuma ta shafe shekaru da dama tana zaune a Amurka.

Trump ya daɗe yana amfani da kalaman batanci, da kuma kalaman nuna wariyar launin fata da na nuna wariya ga mata, yana fadi a lokuta da dama cewa baƙi a Amurka da ba sa zaune bisa ƙa'ida ba su zama "guba a jinin ƙasarmu."

Magajin garin St Paul Melvin Carter, baƙar fata na farko magajin garin Twin City, wanda kuma gida ne ga 'yan Somalia da yawa, ya ce Trump na bata wannan al'umma ta hanyar "nuna wariyar launin fata" da "ƙiyayya ga baƙi."

Ƙungiyoyin kare haƙƙin jama'a sun yi gargaɗin cewa irin waɗannan kalaman na batanci da matakan da ake dauka na iya ƙara kawo rarrabuwar kawuna a zamantakewa, haifar da rashin yarda, da kuma haifar da take haƙƙin jama'a, musamman idan aka ba wa jami'an tsaro ikon ƙara yawan kayan aikinsu na aiwatar da shige da fice bisa ga zargin jama’a baki daya.

Da yake ambaton kalmomin farko na Kundin Tsarin Mulkin Amurka - "Mu ne Mutane" - a matsayin kalmar da ta fara kaddamar da ƙwarewar Amurka, Carter ya ce "lokutan alfarma a tarihin Amurka su ne lokutan da muka yanke shawara kan su wanene 'mu', wane ne aka haɗe da shi.'

"Wadanda Trump ke suka da bakantawa ba wai 'yan Somalia kawai ba ne - 'yan Somalia kuma Amurkawa ne," in ji Carter. "Wadanda ya kai wa hari Amurkawa ne."