Aden Abdullahi: Wani matashi da ke kula da dabbobin da ke gararamba a kan titi

Wani matashi wanda ake yawan hange a kan titunan Mogadishu yana kula da dabbobin da ba su da matsuguni, a hankali yana jawo ra’ayin mutane kan muhimmancin kula da dabbobi a ƙasar da yaƙi ya ɗaiɗaita.

By
Aden Abdullahi, mai kula da dabbobi a Mogadishu / TRT Afrika

A yayin da Mogadishu ke ƙoƙarin farfaɗowa da Asubahi, Aden Abdullahi na yawo a kan titunan birnin wanda yake a cikin yanayin shiru tare da mage a hannunsa.

Wasu karnuka biyu a hankali suna jagoranci. Wani tsuntsu ya zauna a kafadarsa, kamar an umarce shi a lokacin wasan kwaikwayo. Mutanen da suka farka daga bacci sun rinƙa juyawa suna kallon Aden. Wasu suna murmushi wasu kuma suna fito da baki inda suke mamaki da sha’awa.

A ƙasar da ke warkewa daga shekaru na yaƙi, inda rayuwa take zama labarin kowace magana, ga wani matashi da ke sadaukar da safiyarsa ga dabbobin da mutane da yawa ke watsi da su.

Kullum Aden na sayen ragowar nama daga masu sayar da nama, yana kula da raunukan da dabbobin da ke kan tituna suka ji, da kuma samar musu da walwala. Yana yin haka da kudi kadan da yake da shi.

"Wani lokaci, ina jin kamar na daina wannan aikin. Amma ba zan iya dakatawa ba. Ina ganin dabbobi suna fama a ko'ina, dole ne in kula da su," in ji shi ga TRT Afrika.

Jinƙai na asali

Tafiyarsa ta fara ne da ceton maciji. Maciji, dabba mai haɗari, tsoro da rashin fahimta, ita ce dabba da mafi yawan Somalai za su kashe ba tare da wata-wata ba. Amma Aden ya ga rayuwa a cikinta, halitta da ta cancanci jinƙai.

Ya ceci macijin ya kula da shi shekaru da dama. Lokacin da macijin ya rasu, ya ji bakin ciki da har yanzu yake ciwo.

"Ya shafe ni sosai," in ji Aden. "Na koma kan kulawa da mage, sai kuma karnuka, da tsuntsaye. Kowace dabba da na kula da ita ta koya mini sabon abu. Duk lokacin da na gan su cikin koshin lafiya sai ya ba ni ƙwarin ƙarfafa gwiwa na ci gaba."

Ba kuɗi kadai ba ne ƙalubalen da Aden ya fuskanta. Sau da yawa, yadda al'umma ke kallon mutum da ke ɗaukar dabbobi a fili kuma yana yawo da su ya juya zuwa kyama.

Ra'ayoyi marasa daidai da addini da tsafi sun sa wasu su ɗebansa a matsayin baƙo. Abokai suka ɓace, maƙwabta suna ta ƙaraɗaɗa maganganu, kuma hanyoyin samun riba sun kasance cikin haɗari.

A wancan lokacin, Aden na gudanar da ƙaramin gidan shayi, yana samun kuɗi kaɗan da ya isa ya rike kansa da iyalinsa.

Amma yayin da ya ƙara sadaukar da lokaci ga dabbobi, kasuwanci ya takura kuma jita-jita suka yadu. Mutane sun guje wa gidan shayin saboda suna alakanta shi da karnukan kan titi, waɗanda da yawa ake ganin ba su da tsafta. A ƙarshe, ya rasa komai.

"An rufe gidan shayina," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika. "Abokaina sun ɓace. Wasu sun ce ina ɓata rayuwata. Na ji kadaici. Ban da dabbobina babu komai, wani lokaci ina jin hakan bai isa ba."

Amma Aden bai tsaya ba. Ya ga wahala ya zaɓi yin abin da ya dace, ko da duniya ta juya baya. Ya danganta jinƙai marasa son kai ga bangaskiyarsa.

"Allah ne ya dasa wannan jinƙai a zuciyata," in ji Aden. "Kula da dabbobin da suke cikin wahala ya zama burina na rayuwa."

Mayar da hankali kan dabbobin gida

Ba kamar Kenya, Tanzania, Uganda da Rwanda da ake saninsu da yawon shakatawa na namun daji ba, a ƙasar Somaliya inda Aden ya fito dabbobi na nufin dabbobin gona. Akuya da raƙumi sune suka mamaye al'adu da tattalin arziki.

A cewar Hukumar Abinci da Noma ta Duniya (FAO), Somaliya na fitar da fiye da dabbobi miliyan huɗu a kowace shekara, mafi yawansu zuwa Gabas ta Tsakiya. Dabbobin gona suna kai kusan kashi 70% na ma’aunin GDP na ƙasar da kuma kashi 85% na jimillar fitar da kaya, ana sayar da su a farashi mai araha kuma ana bin ka'idojin halal wajen kashe su.

Wannan mayar da hankali ga dabbobin gona ya rufe bukatun sauran dabbobi. Maguna, karnuka da tsuntsaye da ke rayuwa a unguwanni tare da mutane ana barinsu ba tare da kulawa ba.

Aden ba wai kawai yana kare dabbobin da mutane ba su kula da su kawai ba, har ma yana kalubalantar dabi'u da al'adu da suka gurɓata tunani.

Ya ci gaba da yawo a fili tare da dabbobi a tituna kuma yana magana da yara da masu shaguna game da muhimmancin nuna ƙauna gare su. Idan suka yi hulɗa da shi, yana a hankali jayayya da ra'ayoyin da aka jima da su game da waɗannan dabbobin.

A hankali, ƙoƙarorin Aden yana fara ba da sakamako. Yara da suka saba jefa duwatsu kan karnukan yanzu suna barin kwanukan ruwa a wajen gidajensu. Tituna inda ake korar dabbobi yanzu sun zama wuraren tambaya da, wasu lokuta, nuna ƙauna.

"Iyayanmu sun tashi a lokacin yaƙe-yaƙe da tsananin wahala," kamar yadda Aden ya bayyana.

"Ba a taɓa koya musu tarbiyya game da dabbobi da bukatunsu da hakkokinsu ba. Ina taimaka wa mutane su fahimci cewa dabbobi na jin ciwo. Nuna ƙauna gare su ba rauni ba ne."

Dabbobin kan titi sun samu gida

Shekaru da dama, Aden ya yi aiki ne kawai a tituna. Dabbobi suna rayuwa kuma wasu lokuta suna mutuwa a ƙarƙashin kulawarsa, suna fuskantar rana, ruwan sama da rashin lafiya. Sai ya gina ‘yar ƙaramar mafaka a Mogadishu inda maguna da karnuka suke kwanciya a ciki," kamar yadda Aden ya shaida wa TRT Afrika.

Amma gwagwarmaya ta ci gaba. Magunguna kadan ne. Kulawar likitocin dabbobi ba ta isa ba. Wasu dabbobi har yanzu suna mutuwa duk da ƙoƙarinsa maras gajiyawa. Kowace asara tana jawo ɓacin rai, kuma tana tunatar da gaggawar bukatar tallafi.

"Ina buƙatar likitoci, abinci, magunguna da kayan aiki masu kyau domin kula da dabbobina," in ji shi.

"Wani lokaci dabbobi suna mutuwa a hannuna saboda rashin lafiya, kuma hakan yana karya zuciyata. Ina son mutanena su ƙaunaci dabbobi. Ina so su rayu cikin salama kuma su nuna jinƙai."

Yayin da Somaliya ke tashi daga tarkacen yaƙi, ayyukan jinƙai na Aden sun zama kiran nuna tausayawa da kuma tunatarwa kan cewa dabbobi suna da muhimmanci ga rayuwar ɗan adam kuma dole a kula da su.